Sashe 12
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan ka Allah ne yayi yanada sauran kwana a gaba, akwai abinda akayi mai da ya jijjigashi Allah ne yatsare dan yawanci idan hakan ta faru da mutum toh take yake kamuwa da matsanan cin ciwon zuciya Kuma mafi yawa daga nan basa tashi amma shi alhamdulillah bashida wata matsala se dai kuyi kokarin kiyaye duk abinda ze tada mishi hankali, domin sakaci da hakan komai ze iya faruwa". Mikewa yayi yama likitan godiya tare da yimai alkawarin in Sha Allah za'a kiyaye duk da shi a iya saninshi babu abinda sukama mukhtar hasalima basu san meya sakashi cikin halin nan ba. *Muhibbah* Tana zaune kan pray mat tayi ta gumi se sake sake take, Aisha ta shigo kiranta suyi dinner yafi sau 3 tace bazata ci ba gaba daya hankalinta baya jikinta jikinta yayi sanyi tanaji a jikinta duk yadda akayi mukhtar dinta babu lafiya tayita gwada Kiran wayan amma har yanxu switch off. Tana nan zaune har 10pm mummy ta turo a tambayeta meke damuta tace babu komai kawai kanta ke mata ciwo, Aisha ma tayi tambayar duniya tace mata babu komai da ta gaji da tambayar ma cemata tayi karta dameta dole ta hakura ta kwanta ta barta nan zaune. Se wajen 11pm ta kwanta tana tinane tinane a haka har bacci barawo ya saceta. Misalin karfe 4:30 na asuba tayi firgi gif ta tashi tana salati hannu ta zira ta kunna dum light ta dafa goshinta tana addu'o'i da neman tsari daga mummunar mafarkin da tayi. Ganin zaman bazeyi ba ta tashi tashiga toilet ta dauro alwala ta fara nafilo li da rokon ubangiji Allah yasa kome ke faruwa yazo musu da sauki daga ita har shalelen ta. Har tayi sallahn asuba bata kwantaba tanata lazimi se wajen 6am bacci ya dauketa a gurin, karfe 10am Aisha ta tasheta tayi wanka ko zataji kwarin jikinta ta shirya ta fito parlourn. A parlourn tasamu a halin gidan tashiga gaeshesu suka amsa suna mata ya jiki ta amsa musu da alhamdulillah. Dining ta karasa ta danyi breakfast tea kawai ta iya Sha Shima daker yake wucewa, ita dai mummy binta kawai take da ido dan tasan 'yarta gaba da baya tasan babu wani ciwon Kai Dan Koda akwai ciwon Kan to na damuwa ne. Parlourn daddy ta nufa bakinta dauke da sallama, risinawa tayi ta gaeshesu suka amsa cikin kulawa kafin Abba yace "Muhibbah lafiya kike kuwa?" Wani yawu zafi ta hadiya kana tace "Lafiya kalau Abba kawai kaina ne ke danyimun ciwo" "shine baki fada ba akira doctor" "Aa ai nasha magani Kuma nafara Jin sauki". "Allah yakara sauki" "Ameen". *Mukhtar* Har washe gari be farka ba hankalin umma a tashe Abba yazo yasa meta yacigaba da bata baki "Dan Allah hajiya ki daure ko tea ne ki sha kar kema wani ciwon yasa meki, addu'a zaki cigaba dayi amma kukan beda amfani, nakira su Zahra nasanar musu, suna nan zuwa se kije gida kiyi wanka. Daker ya lallasheta ta hada tea tasha seda ya matsa kafin tadan tsakura dankalin turawan da me aikinsu ta soyo driver ya kawo tun sassafe. Kamar almara ta hango yana motsa hannunshi, tayi saurin karasawa gareshi ta rike hannun. A hankali yake bude idanuwan har ya budesu a kan fuskan umma, bakinshi yana rawa yana so yayi magana amma bakinshi yayi Mai nauyi yakasa magana hawaye suka zubo mata bakinta na rawa tace "kayi magana me kake bukata?" Hannunshi ya Kai ya sharemata hawayen ya girgiza mata Kai alaman babu komai. Abba yace "sannu mukhtar" ya jinjina Kai alaman da sauki. Wani abu Abba ya danna yayi kara sega doctor nurses sun shigo, Abba yace su kira doctor. Doctor ya tabbatar musu in Sha Allah zeyi magana ya basu magungunan daza'a bashi idan yaci abinci. "Hajiya bari naje office tunda jikin da sauki, sena dawo". "Allah yatsare yadawo da Kai lafiya" "Ameen" yafada yana fita. Zahra na shigowa tasa kuka umma tace "kiyi shiru ai jiki Alhamdulillah da jiya ko dazu kika zo ai ko motsi bayayi kamar matacce, ta matsa kusa dashi tana kuka tace Yaya kayi magana please kafadamana meke damunka, meyasamu muhibbahn ka kota mutu ne?" Ta jero Mai tambayoyi Motsi da bakinshi yakeyi alamun yana magana ta kara kunnenta amma bataji komai ba, alama yayi mata da hannu tabashi wayarshi. Umma ta Mika mai wayan ya kunna ta, ai ko beyi 5 minutes da kunnawa ba Kira yashigo wayan, Zahra ta dauki wayan ganin sunan my life na yawo akan screen din wayan. Picking call din tayi tasa a speaker "Hello Hayateee, meyafaru tun jiya nake kiran wayanka a kashe, fatan kana lafiya? Kasani a tashin hankali dabaka ban samu wayanka ba zuwa axuhur zanzo gidan umma Koda kwatance ne ta karashe maganan tana sakin kuka" Kuka Zahra tasa batare da tace komai ba Cikin tashin hankali ta mike tace "Hello! Wake magana?, ina Hayateee" "Zahra ce" Cikin rawar murya tace "A... Unty Zahra, meyasamu ya mukhtar din kar ki fadamun komai kar kicemun wani abu yasamu ya mukhy". "Ya mukhtar yana asibiti bashida lafiya ko magana baya y..tun Bata karasa ba tasaki kuka me sauti tana fadin innalillahi wa inna ilaehi raji'un, kuna wane asibiti?". "Al_muneef" tafada a takaice, kit ta kashe wayan ta zube akan gwiwowinta tana kuka be cin rai, Aisha dake gefenta tana sauraron duk abinda ke faruwa ta karasa ta rungumeta tana kukan tausayin 'yar uwarta tace "sisto! Kiyi hakuri ki dena kuka addu'a zaki mishi". Daker ta tsaida kukan ta tashi ta dauki hijjab tasaka tana kokarin fita Aisha ta rikota "ina zaki haka?" "Asibiti" tabata amsa a takaice. Aisha tace "Aa karki fita kinsan halin ya fu'ad Kuma daddy da kanshi zesa ya dakeki tunda ya hanamu fita ko da driver ne indai bamu tambaya ba" wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata tace "Aisha bakya tausayina ne? Bakya ganin fitar ta gama dole ne, kina tinanin zan iya bacci ne idan banje ga farin cikina ba" hannu tasa ta dauke mata kwallar dake tsiyaya daga idanunta tace "bazan barki kifita ke kadai ba tare zamu je". hijjab ta zura suka riko hannun juna suka bi ta kofar baya suka fita ba tare da kowa ya gansu ba, seda suka Kai bakin titi kana suka samu napep. *Mukhtar* Tun da yaji muryan muhibbah zuciyar ta tsinke kukan da takeyi yana tabamai zuciya idonshi ya kada yayi jajir, yana tausayin kanshi amma yafi tausayinta saboda alama sun nuna batasan abinda ke faruwa ba tabbas ko idan ta sani zata shiga cikin wani hali Kuma dole zata sani sedai baze zama mutumin da ze fara sanar da ita munmunan labarin ba. Umma na tsaye ita da zahrah sun shiga rudani, mukhtar yace Muhibbah ce ga muhibbah na nuna batasan ma abinda yasameshi ba su Kuma a gurinta suke sa ran Jin abinda yasamu dansu. Suna nan a haka abokinshi ya shigo da ledoji niki niki Zahra ta amsa ta ajiye gefe. "Ina wuni umma" "lafiya kalau Mubarak" "ya Mai jiki" "dasauki Alhamdulillah". Gaf dashi ya matsa yana mishi sannu, jinjina Mai Kai yayi alamun dasauki Kujera ya janyo kusa da gadon ya zauna yace a hado Mai tea, Zahra ce ta hada tea din ta mikama Mubarak yashiga bashi da spoon yana karba kadan kadan. A guje ta shigo dakin ta haye gadon ta rungumoshi tana fashewa da kuka, "ya mukhy meke damunka? Dan Allah karka tafi kabarni bazan jure rashin ka kusa daniba" wasu zafaffan hawaye masu dumi suka gangaro daga idanunshi, tasa hannu ta daukesu tace "Kayi magana,dan Allah kayimun magana ko zanji sanyi, muhibbahnka ce fa kafadamun damuwarka kar ka boyemun komai" takarasa maganan tana sakin kuka me tsuma zuciyar me karatu. Umma guri tasamu ta zauna tana goge kwallan tausayin muhibbah Nikam nace umma tun ma mukhtar dinki be sanar miki da abinda ke faruwa ba? Uhmmm toh nayi shiru lokacin sanin na zuwa. Bakinshi ne yashiga motsawa alamun yana son yin magana, ta tsura ma bakinshi ido ko zata gane abinda yake son fada daker ya fisgo maganan yace "Muhibbah"............ *Share & repost fisabilillah* *A daure a danna mun like ayi comments* *Mura tasani gaba ga xaxxabi amma nace in Sha Allah sena farantama masoyana Rai nayi typing toh nima dan Allah ku farantamun Rai da comments* [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 21* "Na'am ya mukhtar". Shiru yayi yana kallon yadda ta rungumoshi ga su umma a dakin, ganin ya kafe ta da ido yasa ta sakeshi ta dan matsa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Shiru ne ya ratsa tsakani se chan tace "kayi magana mana ya mukhy". Still yaki cewa komai se kallonta yake kamar me son gano gaskiyar wani abu. Mubarak ne yayi waje yana mamakin wannan kauna ta mukhtar da muhibbah, umma da Zahra ma suka mara mai baya. Seda yaga fitan su umma kafin yace "Muhibbah muyi hakuri da duk wani abu da yasamemu komai mukaddari ne daga Allah idan har Allah ya rubuta ke matata ce to tabbas babu makawa sena mallakeki wannan rubutaccen al'amari ne daga lauhil mahfuz babu me goge shi, idan Kuma Allah ya rubuta ke ba matata bace toh duk sonmu da faruwar hakan baze taba kasancewa ba dan haka kome zakiji kiyi hakuri ki tayamu da addu'a Allah yasa haka shine Mafi alkhaeri" yakarasa maganar wasu zafaffan hawaye na silalowa daga idanunshi yayi saurin daukesu da babban yatsarshi, ya dafe saitin zuciyarshi da yakejin kamar zata tarwatse. Jan numfashi tafarayi tana damke setin zuciyarta a tsorace yashiga girgizata Jin kamar numfashinta ze dauke "muhibbah! Muhibbah!! Karkiyimun haka". Dasauri Aisha da tun dazu tasamu guri ta zauna tana sauraron iKon Allah ta karaso tana kwalama muhibbah kira. Daker ta janyo numfashinta tasaki kuka me sauti tana furta "innalillahi wa inna ilaehi raji'un, ya mukhtar kayimun bayani yadda zan fahimta, kar kacemun Abba cewa yayi baze baka niba" ta fada tana sakin sabon kuka. Harde hannunshi yayi a kirji yana kallonta, seda ya numfasa kafin yace "ba haka nake nufi ba, ina nufin komai mukaddari ne daga Allah bamu san me gobe zata zo mana dashi ba". Nannauyar ajiyar zuciya tasauke tace "babu abinda ze faru ya