Sashe 66
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba da kulata ta tabbatar da ba lallai zamanta da Fu'ad yayi nisan zango ba. Ta gaji sosai kanta har ciwo yake mata tsabar stress, Ruwan zafi tashiga ta gasa jikinta, ta fito tayi Shirin kwanciya, tea kawai ta hada tasha tayi feeding little, ta tofa musu addu'a suka kwanta. Koda yashigo ya samu har tayi bacci yayi pecking goshinta, yayi pecking kumatun little yaja musu kofa. Kwana biyu da suna suka fara exams, yau satin unaisah 2 a duniya, Kuma yau sukayi final paper, kamar Koda yaushe yauma su hudu suka jero suna tafiya, unaisah na kafadar Umaina. Sauban ne ya karaso ya musu sallama, Muhibbah ta amsa. da mamaki yake kallonta yau karo na farko daya tabajin muryarta, duk haukan binta da yayi a baya be taba jin Koda tarinta ba. Daker ya iya bude baki suka gaisa, ya dan Kalleta yaga babu ciki a jikinta dan yana ganin wucewar su kwanaki da katon cikinta a gaba, kallonshi ya kai gurin Umaina, ganin baby a hannunta yasa yayi dan murmushi yace, "Ashe ansamu karuwa, Allah ya raya" batayi magana ba se Aesha ce ta amsa da "Ameen". Yarinyan ya karba ya saki murmushi, yana tina shakar da yasha gurin babanta kila a lokacin daya ke bin mamanta ma da cikinta, mikata yayi tare da ciro kudi ya mikama Muhibbah yace a ba baby, taki karba, Ganin yanata rokonsu yasa Aesha ta karba tayi mai godiya. Ya Kalli Umaina yace, "Gashi anyi hutu, dan Allah ki bani dama nazo inda kike please" Dan yatsina fuska tayi tace, "zan duba na gani, zamuyi waya" tana Kai nan ta wuce suma suka mara mata baya suka barshi tsaye. Muhibbah tace, "Haba Umaina! Wulakanci babu kyau, miye aibin bawan Allahn nan ne? Tun tuni kike ja mai class, ni nayi tinanin zuwa yanzu kun dade da wuce gurin, dan Allah ki bashi dama please" "har yanzu bangama tinani akan lamarin bane, kema fa a baya babu wulakancin da bakiyi mai ba....." saurin daga mata hannu tayi tace, "Dan Allah karki dawo da hannun agogo baya abinda ya wuce ya riga ya wuce, kinsan ni matar aure ce babu yadda za'ayi na biye mai, hatta jin muryata ta haramta a gareshi indai ba bisa larura bane, so inada wakiliya sister na tafada mishi inada aure, ta wakilceni babu bukatar se yaji daga gareni, duk wata matar auren data san mutumcin kanta natabbatar abinda nayi itama shi zatayi" jikinta ne yayi sanyi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace, "Okay in Sha Allah idan naje gida zan kirashi yazo mu fahimce juna, thank you" murmushi tayi suka karasa inda suke jiran driver. Itama Ramlat soyayyar su ita da malam mukhtasir yayi karfi, lokacin da yafara nuna yana sonta da farko ki tayi, da taimakon Allah dana Muhibbah da shawarwarin data dinga bata ta janyo ra'ayin ta har ta sake suka daidaita. Ta kabbarta sallahn isha'i ya shigo dakin, ya zauna bakin gado, tana idarwa tashafa addu'a ta mike ta nade pray mat din tareda zare hijjab din jikinta, ta dawo gefenshi ta zauna, ganin ya hade rai yasa ta kai hannu ta shafa sajenshi tana murmushi tace, "Waye ya tabamun sadauki na? Daya tamkar da dubu" hannu ya Kai ya rike kwankwasonta har lokacin fuskarshi a hade yace, "Meyasa kike boyemun?" Cikin rashin fahimtar abinda yake magana a kai ta waro idanu tana kallonshi, har bakinta na rawa tace, "Hearty! Nikam me kake tinani zan iya boye maka a rayuwa?" "Kema kinsani" yayi maganan har lokacin yana rike da kugunta. Marairace fuska tayi ta rike dayan hannunshi tace, "Kaifa mijina ne kuma sirrina, kayarda dani babu wani abu da nake boyemaka". "Dama kinyi tsarki, amma kullum idan nazo zan kusanceki se kice har yanzu bakiyi wanka ba, Ashe boyemun kikeyi, ni bansan dalilinki nayin hakan ba" rausayar da Kai tayi, ta haye kan cinyarshi suna fuskantar juna ta sakalo hannayenta a wuyanshi a shagwabe tace, "Wllhi babu abinda na boyemaka my heart, dazu ne fa nayi tsarkin" ya bude baki zeyi magana ta hade bakinsu ta shiga aikamai da hurt kisses, romancing dinshi tashigayi tana aikamai da sakonni masu wuyan mantawa, turata yayi ta kwanta kan bed din yamata runfa da kirjinshi, yafara yawo da hannunshi a jikinta, sosai suka ruda juna ganin yana neman daukar wata hanya yasa ta saurin dawowa hayyacinta tayi saurin tureshi amma yaki dagata Kuma be fasa kokarin yin abinda yayi niyya ba. Tino da maganan su Aunty Maiminatu yasa gabanta faduwa, taso ta hakura ta kyaleshi dan tasan ya wahala na tsawon satikai amma tino batun ciki yasa taji wani karfi yazo mata ta tureshi amma ina takasa, data rasa mafita seta sa mai kuka sanin ba'a gida suke ba yasashi mirginawa gefe ya janyota yana bubbuga bayanta, "Bloody! Meyasa kikemun rowan na lasa ni'imar ki?" Kaita girgiza cikin muryar kuka tace, "Abban fateema! bafa a gida muke ba, dan Allah kayi hakuri har mu koma gida, kaga a can duk abinda zamuyi se muyi, kai ko a parlour kace muyi kasan bazan ce aa ba, amma nan fa gidan iyayen mu ne kuma sirikaina kaga ai akwai kunya" "yanzu da daren nan wa ze san abinda mukeyi, ko da rana ne ma babu me shigowa tunda ansan ma'aurata ne a dakin kuma akwai sirri tsakaninmu, hakurina ya kusa karewa idan bazaki dinga bani hakkina ba gaskiya zaki tattara ki koma gida jegon nan ya isa haka, ai kin iya wanka, ke nida kainama sena dinga miki" iya gaskiyarshi yake fada. Dariya sosai tayi tace, "Kai Abban Fateema" "Allah karki ga wasa nasoma gajiya". Ajiyar zuciya tasauke ta lumshe idanu bata Kuma cewa komai ba. Bayan Muhibbah ya maida babyn ya kwantar shikuma ya rungumi matarshi batayi yunkurin koranshi ba gudun fitinan shi badan taso ba ta lafe ajikinshi har bacci ya kwashesu. Drama suka dingayi ita dashi, tana mai duk abinda zesashi farinciki, tana biye mai suyi bidirinsu amma da taga yana kokarin zarcewa seta samishi kuka, idan taga yayi fushi se tayi kamar ta yarda, amma da ta tina Kalmar ciki seta rabu dashi har yagama fushinshi ya sauko, ko yace tazo suje shopping ki take gudun yamata wayau ya nufa gida da ita ya ritsata, sedai tace yasiyo mata duk abinda yaga ze dace da ita. Daga karshe ma fushi yayi yadena kwana gidan Ummi sedai yazo da safe ya duba babynshi da yamma ma idan ya dawo daga asibiti ya biyo yaga lafiyan babynshi, be wani kulata gaisuwanta kawai yake amsawa se kuma ya tambayeta ko akwai abinda suke bukata itada unaisah, abin duk ya dameta amma haka nan ta daure dan bataji zata iya mai abinda yake bukata batare da tayi 40 days ba. Suna zaune a parlour itada Aesha da Ummi se Fu'ad dake rike da unaisah yana mata wasa. Ummi tace, "Muhibbah! Kinsan jibi zakiyi arba'in ko, ki fara shirya kayanki idan Allah ya kaimu jibin da rai da lafiya su Maiminatu da Suhailat zasu zo su maidake dakinki" "Ummi!dan Allah ki bari nagama yawan arba'in tukunna sena koma gaba daya" tayi maganan tana marairaicewa "Zaman me zakiyi anan din? Ki hada kayanki ki tafi tunda kinyi arba'in, idan yaso a gidanki kya yi ziyaran, Aesha ki tayata ku hada kayan, gobe me gyaran jiki zata zo ta miki" fuska ta bata kamar zata saki kuka, tana dagowa karaf idanunsu suka shiga cikin na juna, gabanta ne ya yanke ya fadi, shikuma yasakarmata wani cute smile me wahalan fassarawa................... *Alhamdulillah idanu da sauki, zafin ma kadan yakeyi shima se idan na jima ina kallon hasken screen, ina godiya sosai da addu'o'in ku Allah yabar kauna* AMINIYAR ANGO [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD* *AMINIYAR ANGO* *Page 60* *Wannan page din naki ne my Aunty (MUM MUNEEFA) kiyi yadda kike so dashi, Allah yabar so da kaunar juna, ya kara muku dankwan kauna keda doctor* Tana zaune bakin gado se Aesha ke faman hada kayan, ita ko se aikin masifa take ma Aesha, saboda haushin Ummi taki bari tagama yawon arba'in kafin ta koma gida. Aesha ta Kalleta tace, "Malama kin wani samu guri kin zauna, nufinki ni kadai zaki bari da aiki?" Harara ta watsamata kana tace, "Wllhi ko tsinke bazan dauke ba, ni na aikeki kika jibgo kaya kamar masu barin gari? Tunda har ke kika jibgo su, dan haka ke zaki hada kawunan su" dariya sosai Aesha tayi tace, "Allah ya huci zuciyar uwar unaisah, bani na kar zomon ba rataya aka bani, ni karki wuce a kaina" ta kai karshen maganan tana cigaba da abinda takeyi. Tsaki taja tace, "Kanki ake ji" Bata kulata ba, har ta gama hada duk wani kaya da tasan na unaisah da Muhibbah bane. Washe gari Ummi ta kira me gyaran jiki tazo ta yimata dilka, aka mata lalle da kitso, ta dawo fess kamar sabuwar amarya. Yau baby Unaesah tayi @40 days, tasha gayu tana shirye cikin riga da skirt, kallo daya zakama kayan kasan sunja kudi, tayi kyau abinta Aesha sai kashe mata hotuna takeyi tana daurawa a status, Abbanta na gani ya cire wanda yafi mai kyau ya maidashi a wallpaper dinshi. Ganin 3pm tayi yasa Ummi ta dube su tace, "Maiminatu wai me kuke jira ne? kutashi ku tafi mana har la'asar ta kusa fa" kafin suyi magana Muhi bbah ta marairaice fuska tace, "Dan Allah ummi ki bari na kara ko 1 week ne, lokacin nagama yawona" saurin taran numfashinta tayi tace, "kinsan Allah Muhibbah ko Kwana daya bazaki kara gidan nan ba, Mijin ki se wani hada rai yakeyi har yaji yayima gidan nan, kuma nasan saboda an rike mai mata duk yake wa innan abubuwan, magana ce kawai beyi ba, dan haka tun be fito yace nabashi matarshi ba ki shiga ki dauko mayafin ki ku tafi, Allah ya raya" kwalkwal tayi da idanu tace, "Ummi dan Allah ki rokamun Yaya ya barni naje KD, idan yaso idan nadawo se na koma gaba daya". "Ni Khadija! Babu ruwana dashiga lamarinku, mijinki ne kun fi kusa kitambayeshi idan yace kije toh Allah ya tsare hanya" Baki ta tura, hawayen idanunta suka silalo tace, "Toh Ummi ai nasan koda na tambayeshi baze barni ba" "Toh Muhibbah nidai banida abin cewa kiyi hakuri, ki tashi ku