← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 69

Sashe 27

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jiki "Maamana mun baki tarbiyya dai dai iyawarmu kiyima mijinki biyayya, kibi mijinki duk wata nasiha mahaifiyar ki tariga ta miki saboda duk wani abu datakeyi kina Kallo, kiyi koyi da ita baza'a taba Jin kanku keda mijinki ba, Allah yamiki albarka, Allah ya albarkaci aurenku". "Nasiha kullum cikin yimiki nake, babu abinda zance se ki bi mijinki sau da kafa zaki rabauta ranar gobe kiyamah, kibi mijinki! Kibi mijinki!! Kibi mijinki!!! Tashi kije Allah yamiki albarka Allah ya albarkaci aurenku yabaku zuri'a dayyiba" ta Kai karshen maganan tana shesshekan kuka. Kankame mummy tayi Kam tana kuka harda majina duk mutanen dake parlourn nan seda suka zubda hawaye banda iyye data tabe Baki "Duk kukan gulma ne yaran zamanin nan Kuma da an dauki hanya zakijita tsit" Aesha dai kallonta kawai tayi ta dauke Kai dan bata cikin mood din dazata maida mata martani. Daker aka banbareta daga Jikin mummy, ko wajen shiga mota ki tayi ana turata tana kokarin fita se daker aka samu aka sata a tsakiyar su Aunty Maiminatu. Aunty Asma'u, Aunty Maiminatu, Amarya, Aesha, Zahrah, summy da Rufaeda a mota daya. Iyye, Baaba Salamatu, baaba bilkisu, baaba Mariya Suma mota daya. yayar Ummi haleematu da inna Hassana Suma motarsu daba. Ajere motocin suka bar unguwar zuwa air port, Flight din karfe 12 suka bi................... *Toh Amarya Allah yasanya alkhaeri yabaki iKon Dana gana 'yan team dinki su mum muneefa da sauransu sunce nafada miki se sun zo cin Chin Chin da taliya kinsan taliyan gidan amarya dadinshi nada ban ne *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 32* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Koda suka sauka a air port sun samu har Fu'ad ya turo motoci a jere motocin suka dauki hanyar jimeta, wani tsararren unguwa AT unit suka nufa babban unguwa ce shinfide take da kwalta manya manyan gidajena tsararru a unguwan wani hadadden gida drivern yayi parking tare da yin horn me gadi ya wangale musu gate ya danna hancin motar cikin makeken compound din sauran motocin suka mara mai baya. Tunda taga basubi hanyar yola ba tasan ba gidan Abba suka nufa ba aikam tasaki sabon kuka babu Wanda yayi yunkurin bata hakuri har suka iso. Compound din gidan shin shinfide yake da interlocks dg wajen shiga parlour Kuma shinfide yake da grass carpet ta can gefe Kuma flowers ne kure se daukar ido suke. Zahra da Aesha suka rikota a hankali har kofar parlourn sun zo shigar da ita iyye tace su tsaya tayi bismillah tashiga da kafar dama "Kai tsohuwa wannan al'adan fa andenashi, se kauye da basu waye ba sukeyi" cewar Aesha "Kuji ja'ira toh kema asalinki kauye ne" "Aa wllhi nikam babu abinda ya hadani da kauye" "Kinci gidanku naga uban nakima daga kauye ya fito, ku saketa ta shiga da kafar dama". Cikin rawar murya tayi bismillah ta zura kafarta ta dama suka mara mata baya cikin tankameman parlourn wani sanyin dadi ya ratsasu parlourn se tashin kamshin dadi yake gaba daya furnitures din brown colour ne su summy se kuranta kyaun parlourn suke ita dai Muhibbah tun da suka tawo ta nade kanta cikin lafayan tanajin suna zuzuta kyawun gidan amma taki bude kanta Kuma har lokacin kuka take kasa kasa sama suka haura Aunty Maiminatu tamurda handle din kofar dake hannun dama ta shiga taga duk kayan Fu'ad ne a bedroom din ta bude wardrobe taga kayayyakin shi jere a ciki hakan ya nuna mata ba dakin Muhibbah bane fitowa tayi ta rufo kofan suka nufa bedroom din dake gefen hannun hagu ta murda suka shiga dakin tsaf se kamshin room freshener yakeyi a bakin gado ta zauna ta kife kanta a tsakankanin cinyoyinta tashiga rera kukanta iyye tashiga zazzaga masifa "Kedai wannan yarinya kwai ja ira duk kin bi kin addaba mutane da kuka, wacce irin zuciya gareki da batajin lallashi toh ki mutu, zama gidan nan daram babu inda zaki Allah yasa wata rana naga kina iyayi akan fu'adu kiga yadda zamuyi dake, Kai kutashi mu tafi gidan Haruna tunda kunga gida gobe idan Allah ya kaimu kwa dawo". Mikewa su baaba Salamatu sukayi suna karama Muhibbah nasiha sukayimata seda safe suka fita gwaggo haleematu yayar Ummi ma ta mike tana lallashin Muhibbah tace su Asma'u su zauna karsu bar su Aesha kadai a gidan idan yaso da yamma se su tawo gaba daya. Aunty Maiminatu ta rako su compound din tasa driver ya kaesu iyye gidan Abba, bayan yadawo daga kaisu yatawo musu da abinci sallah suka tashi suka gabatar banda Muhibbah data kara na dewa akan bed tana ta ajiyar zuciya a jere a jere. Aunty Asma'u tace "Oya tashi kije kiyi alwala kiyi sallah ko zaki ji saukin abinda kike ji a zuciyar ki" ko motsi batayi ba bare asa ran zata tashi "Aunty period take fa, dazu da safe tasa nasiyo mata pad" Aesha da idar da sallahnta kenan ta fada. Batace komai ba suka fita da maimunatu zuwa kasa, Summy na ganin fitan su tace "Kai wannan lamari beyi dadi ba, wannan period yama ya Fu'ad bakin ciki" Aesha tace "Amma ance idan mace akayi bikinta tana period to data gama tana saurin daukan ciki, Kai wayaga ya Fu'ad da baby kila sanadiyyar babyn mu dinga ganin hakoranshi". Nan suka shiga tsokanarta amma ko kala ba tace musu ba, Zahrah ta bude wardrobe ta samata wasu manyan ledoji guda 2 tace gashi inji umma Dayar ledan Kuma sakon ya mukhtar ne, tanajin ta amma bazata iya magana a yanzu ba bare tayi godiya, Suma kasa suka sauka sukaci abinci. Se dasukayi magrib a gidan kafin su Aunty Maiminatu suka tasasu gaba suka bar gidan. Wani sabon kuka ta dasa tanaji suka kulle mata kofa sukayi gaba amma batada damar binsu tana kwance tana kuka bacci ya lallabo yayi awon gaba da ita. Se karfe tara na dare su Suhail suka rakoshi suna zuwa kofar parlourn ya karba ledojin hannunsu sukayi sallama ya kutsa kanshi cikin parlourn yanaji suna mai shakiyanci amma be kulasu ba. A dining ya ajiye ledojin ya haura sama direct dakinshi ya nufa yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci riga da wando iya guiwa ya feshe jikinshi da turare, ya nufa kitchen ya dauko plate ya dawo dining ya zauna ya bude Daya daga cikin ledojin daya shigo dasu yayi saving kanshi yana tsaki Dan baze iya tina lokacin dayayi saving kanshi ba kadan yaci kazar ya tattara kayan ya Kai kitchen ya dauko sauran ledojin ya haura sama dakinta ya nufa ya murda handle din kofar ya shiga da sallama a Saman lips dinshi, hangota yayi a kan bed ta kudundune kamar wata baby akan bed side drower ya ajiye ledojin ya nufa hanyar fita har ya dora hannunshi akan handle din kofar kome ya tina Kuma ya dawo, hannunshi ya Kai wuyanta yaji zafi rau dan zaro idonshi yayi a hankali ya furta subhanallah yarinyar nan naso ta kashe kanta. Zama yayi genfenta a hankali yake yawo da hannunshi a jikinta har ya Kai wajen daurin yasa hannu ya sunce daurin lafayan ya war ware lafayan cikin dabara karta tashi hannu ya Kai ya zage zip din rigarta yayi kasa da ita ya fara kokarin ballemata hook din bra tayi saurin rike mai hannu daga ita har shi suka sauke ajiyar zuciya kamshin turarenshi yasa tayi saurin bude ido idanunsu suka sarkafe dana juna sun kai 1 minute a haka kafin ta lumshe idonta ajiyar zuciya ya sauke ya zame hannunshi daga nata ya Kai hannunshi ya balle hook din ta zabura ta mike zaune tasa hannu tana kare kirjinta kafada ya dage yana tabe baki ya mike ya bude wardrobe dinta ya dauko mata rigar bacci ya hauro gadon yana kokarin samata rigar tasa kuka dama me neman kuka ne aka je feshi da kashin awaki ajiyemata rigar yayi ya fice tana ganin fitarshi tayi sauri ta dauki rigar tasa ta shige cikin blanket ta kudundune. Allurai yaje ya dauko paracetamol da atimeter hada giran sama da kasa yayi ganin fuskanshi babu wasa yasa tashiga hankalinta amma duk da haka daker akayi alluran, gudun AC ya kara ya kashe hasken dakin ya nufa bedroom dinshi. Cikin dare yunwa ya tasheta taje kitchen ta dauko plate da cup ledan Kazan ta bude ta yanka rabi tasa a plate ta janyo dayar ledan ta bude hollandia yoghurt ta zuba a cup sosai taci Kazan ta kora da hollandia, toilet taje tayi brush ta dawo ta kwanta tana tinane tinane har bacci ya sureta......... *Kuyi hkr bacci nakeji yau bazan iya kai kmr jiya banyi bacci ba please* *Aminiyar ango * *Aminiyar ango * *Aminiyar ango * *Ayi hkr Dani please babu yawa, ga bacci inaji* [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 33* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t
Chapter 27 · 0% Book details