← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 69

Sashe 51

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

din zaka san maraici ba karamin abu bane maraici ba dadi duniya ta baci mutane basu dauki zuminci a bakin komai ba ko kai ka karanta se ka zubda kwalla" "Wannan wane book ne haka bani labari inji" yafada yana cusa kanshi wuyanta yana shin Shinar sihirtaccen kamshin ta. "Wata yarinya ce fa babanta ya rasu tun tana ciki wajen haihuwar ta kuma Allah ya karbi ran mahaifiyar ta se kakanta mahaifiyar babanta ta dauketa bata wuce 8 years ba Allah ya ma kakar tata rasuwa ta koma wajen innanta kanwar mahaifinta ita ma wajen haihuwa ta rasu shikenan ake kiranta da mayya wai tun tana ciki take maita wasu kuma su ce mata annoba rasuwar kanwar mahaifinta yasa ta koma gun kawunta kanin mahaifinta kawu shima bashida mutum ci yaita zaginta matanshi suke dora mata tallah wannan da safe wannan da yamma Kuma ko kadan bazasu bata ba se dai ta kankare kanzon tukunya taci akwai ranan da ta fita tallah wani daga siyan abincin ta yaci a take a gurin ya mutu nan matasa sukace se sun kashe ta daker aka kwaceta daga karshe kanwar mahaifiyar ta tazo ta tafi da ita taji dadin zama gidan sosai Auntyn ta ta haifa 'yan biyu babu jimawa ta rasu nan kishiyar Auntyn nata ta kwaso jama'ar gari wai ita ta kashe Auntyn nata nan fa ta dauki piya piya ta sha tsabar yadda rayuwa tamata kunci shine wasu sojoji su biyu sun zo wucewa suka ga dan dazon mutane suka karasa gurin dayan sojan ne ya haura Katanga yasameta tana kokawa da numfashinta ya fasa madara yabata kana aka tafi da ita asibiti, anan na tsaya se naji shigowarka" tana labarin tana kuka. Shima kanshi daya ji labarin seda jikinshi yayi sanyi yakara tsorata da duniya Hancinta ya ja "yanzu Kuma lokacina ne kibari gobe da rana seki karashe karatun nima zanso inji karshen labarin nan" ya fada yana dauke mata hawayen fuskanta "Kuma kasan abinda ze kara daga ma hankali?" Ta kare maganan cikin sigar tambaya hade da jimami Kai ya girgiza kan yace "Aa sekin fada" "Is a true life story" Dan zaro ido yayi "Really?" Kai ta jinjina "Shiyasa labarin ya tabamun zuciyata sosai imagine nake tayi idan nice ya zanyi". Ajiyar zuciya ya sauke "Ko wane bawa da kaddararshi Heebbah wayanmu ko dubarar mu bazata taba sa mu guje ma kaddararmu ba seta riske mu a duk inda muke, fatan mu dai Allah yabamu iKon cinye jarabawarmu ita kuma Allah yakawo mata mafita irinsu gaba zakiyi mamakin matsayin daza ta taka ita haka rayuwa take baka taba yin nasara ba tare da kalubale ba yayinda kalubale suka tasoka toh akwai nasara na jiranka gaba, Allah yasa mudace" "Ameen! Ai wannan ko wacce irin nasara ta samu ta can can ceshi wannan uku ban rayuwa haka da kana nun shekarunta" tafada tana sauka daga jikinshi tare da riko hannunshi "Hearty muje kayi dinner" dan waro idanu yayi se yanzu hankalinshi ya kai kan kayan dake jikinta, riga ce transpered iya guiwa babu abinda be bayyana na jikinta ba Mikewa yayi yana kare mata kallo yana jin wani abu na fisganshi yana kokarin yin magana tayi gaba tana dariya dole tasa yabi bayanta yaja kujera ya zauna, serving dinsu tayi tana murmushi tana Jin ninkin kaunarshi, ta zuba musu juice din a cup daya ta dare cinyarshi ta shiga bashi abincin a baki ita ma tana ci duk yadda yaso tabari ya ciyar da ita da kanshi ki tayi wai yana mata wayau itama tana so ta hidimta ma mijinta tana Kai mai laumar farko ya lumshe ido "Wow delicious! bloody kinji dadin abincin nan kuwa?" "Kai hearty kose ansa ma waigi ne" tafada tana dariya "Gaskiya gara kisamun waigi kar in fadi wannan dadi har tsakar ka" yafada yana murmushi Sosai ya karbi abincin juice din ma yasha babu laifi dan bakaramin dadi ya mai ba. Mikewa yayi da ita suka nufa bedroom dinshi kan bed ya direta da sauri ta sauko tafara balle mai botir din rigarshi tare da mika mai towel ya daura ta juya baya ya karasa cire wandonshi murmushi me sauti yayi "Soon zan cire miki wannan kunyan" ya fada yana nufan toilet. Dariya tayi ta nufa wardrobe ta dauko mai kaya be san dauriyar da tayi ba wajen balle mai botiran Gefen bed ta zauna, be jima ba ya fito ta mika mai riga da wando na bacci karba yayi yasa iya wandon ya bata rigan ta maida wardrobe Gaban mirror ya karasa ya feshe jikinshi da turare kan yadawo ya zauna gefenta kwanto da kanta tayi kan cinyarshi shi Kuma ya riko hannun ta yana shafa bayan hannun da babban yatsanshi dayan hannun Kuma yana shafa gashin ta da be taba gajiya da shafawa indai suna tare. Wayanshi ya janyo yayi dialing numbern Suhail ringing daya ya daga "Dan uwa ya akayi ne yanzu nake shirin kiranka" "Ya ake ciki ne?" "Uhmmm toh ya zanyi tunda ka gaji da ganina a gwauro zan karbeta kan dole ya na iya ai ba'a maida hannun kyauta baya" ya fada yana dariya Murmushi yayi "Kaji dashi dai saura wata rana naga kana rawar kafa a kanta, zan ajiye ma numbern ta dan Allah kayi kokari ka kirata cikin daren nan please" "Haba rawar kafar me zanyi" "Kaga ni kam seda safe yanzu lokacin madam ne" yayi maganan yana dage mata gira Tayi murmushi mara sauti "Eyyeeee muda bamu da mata mun bani da gori dole nasamu Jafar mu tattauna" "Idan kunji haushi kar ku bari ku kai Friday baku shiga daga ciki ba" yana kai nan ya sauke wayan yana murmushi Ita dai tana jinshi amma bata ce mai uffan ba dan bata gane da wanda yake wayan ba ************ Jikin Ammi ta fada ta fashe da sabon kuka hankali tashe Rumaisa ta karaso "Aunty zeeee lafiya? Me aka miki" Ta fada tana zama gefen su "Zainab meyafaru? Kiyi magana mana duk kin daga mana hankali" Dagowa tayi tana kallon Ammi cikin muryar kuka tace "Ammi dr ya gama yanke hukunci baze iya auren mata biyu ba, se dan uwanshi ya hadani dashi" Bubbuga bayanta ta shigayi kan tace "Zainab ki sani duk abinda kika ga baki samu ba toh ba rabonki bane idan duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su hanaki mallakan abinda Allah ya riga ya mallaka miki ba, haka zalika Koda duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su miki abinda Allah be miki ba ina nufin basu isa su baki abinda Allah be baki ba dan haka kisani kowane bawa yana da tashi kaddaran, ba komai muke so muke samu ba. Doctor ya cika mutum me halacci ki Karbi kyautar daya miki hannu bibbiyu muyi fatan Allah yasa hakan ya zama na shine mafi alkhaeri kinji ko?" Gyada Kai tayi tana share hawayen ta kan ta mike ta nufi daki Rumaisa ta mara mata baya sosai takara rarrashinta ta kawomata ruwa tasha kan ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Wayarta ce ta dau kara Rumaisa ta dauko ta mika mata ganin bakuwar number yasa har ta katse bata daga ba Jin an kara Kira yasa tayi picking ta kara a kunne batare da tayi magana ba "Amincin Allah yatabbata ga gimbiyar mata" Dan wara idanunta tayi ta kara kallon numbern kan ta sake karata a kunne cikin shakakiyar murya tace "Ameen tare da Kai" "Lafiya kike kuwa naji muryarki haka ko bacci kike na tashe ki" "No! Kaina kemun ciwo" "Eyyyaaa sorry Allah yabaki lafiya" "Ameeen" shiru ne ya ratsa tsakani na seconds kan yace "Nasan baki gane me magana ba ko" Daga kai tayi kamar yana gabanta kan tace "Uhmmm" "Ina fata Dr ya miki bayanin komai" Dama tun sallamarshi tayi tinanin shi din ne "Uhmmmm yayimun" abinda ta iya fada kenan "I'm by name Suhail Abdullahi Muhammad BICHI" "Zainab Sa'ad" ta fada a takai ce "Nice name! zainabu abu me ta gwayen suna, Fatan zaki sama mun special place a zuciyarki" Murmushi me sauti ta danyi ba tare da tace komai ba "Kinyi shiru gimbiya ta" "Uhmmm" abinda tafada kenan "Me uhmmm yake nufi ban gane yaren ba ko fulatancin 'yan yolah ne" Dariya tayi tace "Aa wllhi ba haka 'yan yolah ke fulatancin su ba" "Yaren ki ne kenan toh a fassaramun" Dariya sosai tayi kan tace "Eh" be kuma cewa komai ba yayi murmushi dan yasan kunyarshi take ji, sosai suka sha fira yana zolayanta tana dariya har ta sake dashi "Bari na barki, kisha magani kafin ki kwanta please, Allah yakara sauki" "Ameen tnx" "Sleep tight" Daga haka sukayi sallama Wayan tabi da kallo tana murmushi Rumaisa da take gefenta tana danna wayanta amma tanajin wasu abubuwan da suke cewa ta matso ta rike hannun zeeee tana murmushi "Aunty kinga kyautar ubangiji ko?, kina ta addu'a Allah ya mallaka miki Dr daya tashi seya musanya miki da wani, kuma shima da gani beda matsala Kuma shi yanada magana ba kamar dr Fu'ad ba" "Haka ne 'yar kanwata a alamu yanada kirki Kuma yanada barkwanci" kwanciya tayi tana murmushi tare da yima Allah godiya se murmushi take daren ya mata dadi sosai ******** Daukarta yayi ya kwantar da ita tsakiyar gado ya kwanto kan jikinta yana binne kanshi a wuyanta "Hearty" "bloody ya akayi" "Dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru a school, wllhi ban taba yi mai magana ba amma nasan nayi kuskure Ina tsoron kayimun fada ne shiyasa ban sanar maka ba" seda ta numfasa kan ta cigaba da magana "Malam Mukhtasir Kuma kai kace mishi kanwarka ce ni shiyasa nima ban fada mishi matarka bace saboda naga baka son jingina kanka dani Kuma ban kai matsayin da zaka nuna ma mutane ni matar ka ba ce" Be bari ta Kuma magana ba yasa hannu ya toshe mata baki yashiga yawo da hannunshi a jikinta har ya rabata da rigar jikinta, babban yatsan kafarshi ya shiga yimata susa dashi a tafin kafarta ya kai bakinshi yana huramata iska yanayi yana yawo da harshenshi cikin kunnenta zauta ta yake neman yi, a dan tsorace take dan be san yayi kadan ya hakura ba gashi ita kuma tarasa abinda yasa har yanzu ta kasa sabawa bata so ta cika raki
Chapter 51 · 0% Book details