← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 69

Sashe 28

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Se 9 ta tashi kayanta ta cire ta daura towel tashige toilet wanka tayi ta fito, a gaban mirror ta tsaya tana karema kanta kallo a hankali ta Kai hannunta ta shafo chest dinta ta danyi rama har kashin wuyanta ya fara fitowa, ta Kai hannu ta shafa fuskarta taga idanunta duk sun zurma kamar tayi a mai da zawo, wani abu ne yazo ya tokare mata kawon zuciya hawaye masu dumi suka silalomata tayi saurin dauke su tana kokarin danne kukan dake taso mata "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, Ya Allah ka kawomun nutsuwa da salama a cikin zuciyata Allah ka yayemun damuwata Allah ka sanyayamun zuciyata, Allah kabani iKon cinye wannan jarabawar Allah kafini sanin abinda ke fili da boye Kai kasan dalilin wannan aure Allah kasa auren nan yazama alkhaeri a rayuwarmu". kukan da take rikewa ne ya kufcemata tasa hannu ta toshe bakinta, seda ta samu ta daidaita natsuwarta ta shiga toilet ta wanke fuskanta ta dawo gaban mirror ta shafa body lotion ta dauki humra ta shafe jikinta dashi, powder kawai ta shafa tasa kwalli a ido se lipstick ta shafa ma lips dinta. Wardrobe ta nufa ta dauko doguwar rigan atampha anyimata dinkin straight gown ta cakare dauri gaban mirror ta tsaya ta Kalli kanta ta shafa sarkar dake wuyanta se kawai ta saki murmushin da rabonta da yinshi tun da satin bikinta ya kama. Juyawa tayi tana zagaye dakin tana kare mai kallo yanayin dakin da irin decoration dinshi ya birgeta bedroom din babba ne ba laifi furnitures din ash colour ga wani hadadden rough center carpet ash colour da ratsin black, Cutton din dakinma ash colour. Jin cikinta yasoma juyine yasata fitowa ta nufi kasa har tayi hanyan kitchen taji ana danna door bell dawowa tayi ta bude ganin Aesha tsaye yasata sakin murmushi, "Barka da safiya matar Yaya" Bata jira cewarta ba ta raba ta shigo parlourn itama Muhibbah ta bi bayanta A dining ta ajiye basket din hannunta taja kujera ta zauna, kitchen taje ta dauko plate da cup tadawo ta zauna kujeran dake facing din Aesha, Ruwan zafin da Aesha ta kawo ta zuba a cup ta hada tea ta zuba abincin soyayyen doya ne da miyan source tana ci suna fira seda tayi kat ta tattare kayan ta maida kitchen sannan suka koma parlour. "Wai ina su Summy ne naganki ke kadai?" "Ummi ce tace natafi ni kadai saboda tasan ya Fu'ad na nan kar muzo muyi shirme kinsan halinshi, amma zasu zo anjima "Uhmmmm" abinda ta iya cewa kenan. "Kai matar Yaya yau kinyi kyau, ko kefa amma da kin maida kuka abinci". Harara ta watsamata "kincika sa ido, Kuma bana son sunan nan indai ba kina so ajimu bane". "Ai dama ba tun yau aka fara jinmu ba, Kuma fa sunan yayi dadi Matar Yaya, wai ina ya Fu'ad dinma ba dai har ya fita ba?". "Oho ajiyar shi kika bani ne, ki duba dakinshi maybe yana ciki" zaro ido tayi "wa rufamun asiri". Suna nan zaune ya sauko tana hangoshi ta daure fuska Aesha tace "Ina kwana Yaya" "Lafiya kalau" kamar bazata gaisheshi ba tace "Ina kwana" "Lafiya" ya amsa da kalma daya batare da ya ko kalla gefen dasuke ba ya wuce. Dining ya je ya zauna tunda yaga Aesha yasan breakfast ta kawo musu, ya jima zaune be ga alamar tanada niyyan tasowa ba ya kula sosai can ya juya cikin dan daga murya yace "Keeee" sarai tajishi amma seta basar, Aesha dai tasan bada ita yake ba amma duk a tsorace take kar laifin Muhibbah ya shafeta suci na jaki, seda ta dauki lokaci batare da ta ko motsa ba kafin ta mike ta nufeshi a kusa dashi ta tsaya bata yi magana ba Shima bece komai ba kanshi a duke yana operating phone dinshi ta Kai 5 minutes tsaye kana yace "serve me" batareda ya dago ya kalleta ba. Girgiza Kai tayi ta nufa kitchen ta dauko cup da plate tazo tayi serving dinshi ta turamai gabanshi, kallonshi tayi na seconds se taga yamata kyau kananun kayan dayasa sun karbeshi, ya dago kai da niyyan cin abinci idanunshi ya sauka cikin nata ji tayi gabanta ya fadi rass yayi mata wani irin kwarjini amma takasa dauke idanunta daga kallonshi dauke Kai yayi yana sakin siririn tsaki ya shiga yin breakfast, yana gamawa ya dauki phone dinshi ya fice daga gidan. Parlourn suka kutso da sauri summy ta rungumeta "Wow matar Yaya, naji dadin ganinki haka yau" murmushi tayi "Uhmmm nima naji dadin ganinku, yanzu nake cewa kodai bazaku zo bane, Ashe kuna hanya" zahrah tace "Mun tsaya shiryawa ne kinsan daga nan zamu wuce" "Haba dai Aunty zahrah yau Kuma kamar ana goranku" Rufaeda tace "Toh me zamu jira kawata tunda mun kawoki dakinki ai yakamata mu tafi, se Kuma munzo suna" tafada tana 'yar dariya, Dukan wasa ta kaimata akasa dariya. Kayayyakin da Ummi ta basu suka shiga nunama Muhibbah sunata yaba karamcin da Abba da Ummi suka nuna musu. Wajen karfe 3 su summy dasu gwaggo haleematu da inna hassana suka tashi tafiya harda kukanta dan ba karamin missing din kawayenta zatayi ba Suma harda guntun hawayensu harda su baaba Salamatu duk ranan suka tafi har iyye ma cewa tayi bazata zauna ba tun kan su tawo gidan Muhibbah Abba yayi yayi da ita ta zauna tace gida zata tafi, Muhibbah tace "Tsohuwa a sauka lafiya, Yau dai zamuji shiru babu surutu, amma jiya hatta gidan nan yasan masifarki" "Kunjimun ja'ira kamar ba ta bace jiya take kuka kamar an aikomata da mutuwa dama nace kukan gulma ne, ina nan zan dawo nan da wata tara har da bakin tsiwa zan hada na gasa". Ta gane abinda take nufi ta basar tayi sallama da kawayenta. Har yamma Suhailt da Aesha na gidan Muhibbah na manne da little zahrah Suhailat tace "Zahrah Aunty tadawo kusa dake wata rana zaki zo kimata kwana biyu" "Aikam Aunty Suhailat da naji dadi". "Wasa nake, so kike na hadu da ya Fu'ad ba dani ba". Se 6 suka mata sallama. Tana zaune a parlour tana kallon TV ya shigo ta Mai sannu da dawowa ya amsa ciki ciki ya wuceta yayi sama bata damu ba dan idan da sabo tasaba da halinshi tun suna kd, har tagama kallonta bata ga ya sauko ba, kitchen ta nufa ta dama custard ta dawo dining ta Sha ta gama ta nufa bedroom dinta seda tayi wanka ta sauya kaya zuwa na bacci kafin ta kwanta. Yau ma Koda ta tashi wanka tayi ta fito parlour Sega driver ya kawo break fast tayi murmushi "Allah sarki Ummi". Yana fitowa be tsaya breakfast ba ya wuce a alamunshi ta gane sauri yake maybe ko yanada patient ne. Yana fitowa wanka aka kirashi akwae patient emergency sauri sauri ya shirya ya fito. Tana kwance kan bed ta tafi duniyar tinani taji anyi knocking door din, ta tashi zaune kafin tabada izinin shiga aka turo kofan daga Kai tayi ta kalleshi "Sannu da dawowa" "ki sameni mota yanzu" yana Kai nan ya juya ya fice. Seda ta danyi Jim kafin ta zari gyale ta fito, murfin gaban motan ta bude ta shiga taja ta rufe, seda yagama danna wayanshi kafin yaja motar yabar gidan. Sanyin AC da kamshin dadi ne suka ratsata ta lumshe ido, hanyan yola ya dauka yayi tafiya me dan tsayi ya danna hancin motarshi cikin wata tsararriyar unguwa Sulaiman ribadu extensions arean masu dashi ne unguwan tsit washe baki tayi ganin su cikin unguwan su Abba dan kallonta yayi ta kauda Kai. A bakin gate din wani tsararren gida yayi horn me gadi ya leko ganin shi ne yakoma da gudu ya wangale Mai gate, ya danna hancin motar cikin gidan Allah Allah take yayi parking dan jin ta take kamar tsuntsuwar da ta kubuto daga keji dan tun shekaran jiya da aka kawota ko compound din gidanta bata leko ba Kuma tun jiya dasu Aesha suka tafi babu Wanda takara gani se drivern da Ummi ta Aiko ya kawo break fast Shima me gadi ne ya karbo basket din, se Kuma Fu'ad Wanda da dawowanshi gidan da rashin shi duk daya tunda yana bedroom dinshi itama tana na ta Koda rana ita kadai a gidan kamar mayya idan tasoma Jin tsoro ta koma bedroom dinta ta kudundune a kan bed ta kunna kira'ar sheik Ahmad sulaiman a wayanta ta ajiye kan bed side drower. Yana yin parking ta balle murfin motan tayi cikin gidan da sauri tana murna................ *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 34* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku
Chapter 28 · 0% Book details