← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 69

Sashe 39

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da tace "Aunty dama dagaske yanada wata budurwan?". "Idan ma beda ita minti nawa ne ya samota shida Koda yaushe 'yan mata ke zaryan yi mai tallan kansu a kullum basuda wani burin daya wuce su mallakeshi matsayin miji kin ga ko seya zama ya darje, Kuma wllhi tsaf zanje na hado mai lefe tunda ke kika zaba hakan". Fada take mata sosai inda take shiga bata nan take fita ba "ki bude kunnenki ki saurare ni miji yafi gaban wasa, aljannarki na karkashin kafarshi seya daga zaki shiga ubangiji da kanshi yace da ze umurce wani bawa yama wani dan Adam sujjada toh da mata ze umurta tayima mijinta sujjada, tsabar girman da Allah yama miji, kisani duk wani abu na gidan aure lada ne. Kina girki ki manta wuka ki koma ki dauko kinada lada kamar kinyi Umarah duk abinda kikayi da kyakkyawan niyya Kuma kikayi shi domin Allah lada ne me dunbin yawa, zaman aure zaman hakuri ne ki shiga hankalinki minti goma nabaki ki shirya ki sameni parlour na maida ki gidanki maza maza" tana kai nan ta fice tana huci. Tana kuka ta shiga toilet ta wanke fuska tadawo ta zira hijjab dinta dama babu abinda tazo dashi kayan Aesha take sawa. Aesha ce ta riko hannunta har parlourn Ummi takara yimata nasiha da bata hakuri, Aunty maimunatu ta tasa keyar ta gaba sukama Ummi sallama suka fice. Har cikin parlour ta kaita ganin parlourn na bukatar gyara ne ta zage ta gyara parlourn saboda tunda tabar gidan mairo bata kara zuwa ba suna tare gidan ummi tsaf ta gyara parlourn tasa turare ita Kuma Muhibbah ta gyara dakinta da na mijinta. Har yamma Aunty Maiminatu na gidan tare sukayi girki suna aikin tana kara yimata nasiha da koya mata dabarun zaman gidan aure, seda suka shirya dining din tamata sallama tayi tayi ta tsaya taci abincin taki haka ta wuce. Ummi ce ta kira Aunty Maiminatu ta sanar mata da abinda ya faru da Kuma kin komawar Muhibbah gidanta shine ta tabbatar ma ummin in Sha Allah zata zo a ranan ai ko tana kai yaranta islamiyya tayo gidan. Wanka tashiga tayi tareda dauro alwala tana fitowa taji ana kiraye kirayen sallahn magrib. Pray mat ta shinfida tasa dogon hijjab dinta har kasa ta tada sallah bayan ta idar ta cigaba da azkar din maraice bata tashi daga kan pray mata din ba seda tayi isha'i kana ta nade pray mat din ta zare hijjab din jikinta ta. Gaban mirror ta karasa ta shafa body lotion ta dauki humra ta shafe jikinta dashi powder kawai tashafa seta sa kwalli a ido se lipstick. Wardrobe ta nufa ta dauko kaya ta zira ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi. Yana budo kofan parlourn yaji kamshin turare na tashi sosai alamun ba'a dade da sashi ba. Bakinshi dauke da sallama iya kan lips dinshi yakarasa shigowa parlourn har ya fara taka staircase ya tsaya ya dan juya yana kara kallon dining din idan idanunshi ba karya suka fada mishi ba kuloli ya hango jere a kan dining din Kuma yasan ya kwashe wa incan ya zubar da abincin ciki daya lalace a dust bin. Da baya baya ya nufi dining din juice din daya hango cikin jug, jug din na na son sanyi yasa ya gasgata ba'a jima da shirya dining din ba. Karan takalmi yaji alamun ana saukowa daga up stairs dasauri ya kai idanunshi gurin ya hangota tana taku dai daya idan tayi taku daya setayi seconds kan ta kara takowa. Sanye take cikin atampha anyi mata straight gown ta kamata ta kasa, shape dinta ya fita sosai ta buga dauri ya zauna yamata kyau sosai. Harta karaso kusa dashi be Saniba seda tace "Sannu da dawowa". Kauda Kai yayi yaja tsaki kawai seya tsinci kanshi da zama kan daya daga kujeran dining din. Serving dinshi tayi ta tura mai plate din gabanshi kamshin turarenta ya daki hancinshi ya dago ya kalleta kawai idonsu ya sarke dana juna sun kai 1 minute suna kallon juna kan ya dauke kanshi yana Jan uban tsaki. Abincinshi yashiga ci yako ci sosai dan dama yunwa yakeji yagaji da cin abincin restaurant shiyasa be biya ba Kuma baya son yake yawan xuwa gidan Ummi ayi tinanin ko saboda Muhibbah ne alhalin bata gabanshi. Kadan ta danci abincin ganin yana kokarin tashi tayi saurin mikewa ta karasa gan ganshi ta zube kan guiwowinta............. [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *Page 43* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 "Yaya kayi hakuri nayi nadama na tuba ka yafemun bazan sake ba". Takai karshen maganan tana hada hannayenta biyu alamar roko. Ido ya tsuramata ya kama lip dinshi na kasa ya tauna da karfi yanajin kanshi na sarawa lokaci daya yana tino ranan daya sameta tana waya da mukhtar, abubuwan dasuka faru a ranan ya na dawo mai take idanunshi suka kada sukayi jajir ji yake zuciyarshi namishi mugun zafi. Mikewa yayi ze bar gurin tasaki kuka tareda mikewa da sauri a dan tsorace ta riko hannayenshi "Yaya a idanunka ina iya hango tsantsar bacin rai da tarin damuwa nasan kuma duk nice silar faruwan hakan, nasani banyi ma adalci ba amma nayima alkawarin gyarawa kar ka kwanta kana fushi dani kar kabarni na kwana cikin fushin ubangiji karkashin ka nake kanada iko da ni da duk wani abu da ya shafeni, kanada ikon yanke mun ko wane irin hukunci wllhi a shirye nake na karba hannu bibbiyu ni din mallakin kace se yadda kaso kayi dani nasani na cutar da kai nayima laifi sannan daga karshe kai Abba ya daurama laifi kuma bakayi yunkurin fadar laifin da nayima ba, yaya dan Allah ka mareni idan har marina zesa kaji sanyi a zuciyarka amma kar ka cigaba da fushi dani" kuka take sosai kamar zata shide, bata tsanmaci zeyi magana ba se tsinkayan muryarshi tayi "Muje ki kwanta". Be kuma maganaba yaja hannunta suka haura sama, a kofar dakinta ya saki hannunta "Seda safe" seda taja majinar kuka kafin tace "Allah yatashemu lafiya". Bece komai ba ya shige dakinshi ya kullo ta jima tana kallon kofar dakin kan ta shiga nata taje toilet tayi alwala tazo ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya ajere ajere. Da safe kusan tare suka fito "ina kwana" "kintashi lafiya?" "Alhamdulillah & you" "normal" ya fada yana dagemata gira daya. Dukar da kai kasa tayi ta karasa dining tayi serving dinshi. Shiru babu wanda yayi magana har suka kammala breakfast din ficewa yayi daga parlourn tabi bayanshi karo sukayi da mairo suka gaisa kan ta karasa ta shiga motan yaja suka fice daga gidan Har suka isa bakin gate babu Wanda yace uffan se sautin karatu kawai dake tashi. Kudi ya ciro ya ajiyemata kan cinya ta dan kalleshi taga ita yake kallo ta kai hannu ta dauka "thank you". Ta fada tana ficewa. Jan motan yayi yabar arean. Hakanan take Jin mood din yamata dadi har tashiga school din tana murmushi a lokaci daya kuma tana mamakin hali irin na Fu'ad idan ya hade rai zaka rantse be San wani abu dariya ba daka kalleshi se ka tsorata bata son suke hada ido dan duk lokacin daxa su hada idanu se gabanta ya fadi. Amma yau kamar bashiba duk da ba dariya yake ba amma fuskarshi ba'a hade kamar ko yaushe ba har tantama take akan gaske shi din ne yau ya sake mata kodai mafarki take. Sun jima sosai a class dan se 4 suka fito cafeteria suka nufa su hudu Aesha, Muhibbah, Umaina da Kuma Ramlat seda suka siyo snacks da drink kana suka dawo suka zauna sunaci suna fira can Ramlat ta dan kalli Aesha "Wai ni in tambayeki gidanku ba daya bane da Fateema?" Dan kallanta tayi kamar bazatayi magana ba "gida daya muke mana me kika gani?" "Aa babu komai kawai dai naga ba tare kuke zuwa bane" "kawai duk Wanda ya riga shiryawa ne Abba ke saukeshi a school wanda Kuma be shirya da wuri ba driver ke kawoshi shiyasa kikaga bama zuwa a tare". Umaina tace "Kiji Ramlat da wata magana gidansu daya mana last week naje gidansu ai karki so kiga kirkin Ummi". "Toh daga tambaya shine nayi laifi, ai matambayi be bata ba gashi yanzu an fahimtar dani sosai ba, Allah sarki Aesha ki gaisharmun da Ummin" "zataji, mungode" Ita dai Muhibbah tana gefe bata ce musu kala ba. "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" saurin daga kai sukayi suka kalla inda sukaji sallaman ganin malam mukhtasir tsaye yasa su danyin murmushi suka shiga gaishe shi ya amsa hankalinshi na kan Muhibbah Ita ko tayi kasa da kanta tana operating phone dinta ko dagowa ta kalleshi batayi ba bare yasa ran zata tankashi. Ta gefen da take zaune ya dan matsa "Barka da rana hajiya" dan dagowa tayi ta kalleshi "Barka dai Ina wuni" "lafiya kalau, Fateema kwana biyu?" "Se alkhaeri". "Kin buya kwata kwata bamu hadu ba fatan dai kina lafiya" "Kasan lafiya ita ke buya" ta fada a takaice. Kai ya Jinjina "Ina alkawari na?" Dan Jim tayi kamar me tinani kan can tace "oh Allah sarki se yanzu na tina, gashi wayan Ummin ma ya dan samu matsala ya baci". ta Kai karshe tana mika ma Umaina wayan hannunta "Umaina rike wayanki na kirata yaki shiga shine kawai na turama message ta watsapp" "Kuma kinyi dubara dan maybe ba network ne inda take tunda bata kashe wayanta amma tunda message din ya tafi zata yi reply" "Toh Allah yasa tayi reply dawuri, kinga idan kika tafi bazan San amsar data dawomun dashi ba ga wayan ummi ya lalace bare ki kira ki fadamun duk abinda tace" "In Sha Allah ma kafin mu tafi zakiga tayi miki reply kinsanta 24 hours tana online" "Haka ne Kam". Ganin tsayuwar baze yi mai ba "Se idan Allah ya kaimu gobe" abinda ya fada kenan yabar gurin jiki a sabule. Yana tafiya suka tafa da Umaina suna shekewa da dariya "Kai Umaina ya akayi kika gane abinda nake nufi dawuri haka?" Dariya tayi "Ai tunda naga kin mikomun wayanki Kuma naji kina cewa wayan Ummi ya lalace na dau haske" "kyale dan anaci zemayi ya bari ne ayi mutum ba zuciya bani wayata mu tafi". Ramlat ta dubesu "Wasu mazan
Chapter 39 · 0% Book details