Sashe 2
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
takarasa cikin makarantan. Awa biyu sukayi a class malamai biyu suka shiga kowannensu ya dauke 40mins yana musu karatu karfe 10:00am aka buga karar rawa muhibbah dama jira take ta kosa time din break yayi ta fesama Sumayya labari. Hannunta tarike tana fadin kawata xo muje kiji bata jira amsan taba ta fice bayanta Sumayya tabi tana fadin kice yau akwai labari kenan, murmushi kawai tayi batareda tace komae ba. Cafeteria suka nufa suka siya meat pie da drinks kafin suka nufi inda aka tanada domin xaman dalibai lokacin break. Gurin ya hadu sosae kujerune masu kyau da tebura zagaye da wajen wata kujera suka samu suka zauna. Ajiyar xuciya muhibbah tasaki tareda sakin murmushi tace I'm in love kallon mamaki tabita dashi cikin rashin fahimta kina nufin kinfada soyayya cewar Sumayya,gyada kai tayi alamar Eh wannan wane me sa'ar ne yasace xuciyarki ya Fu'ad ne tafada a takaice. Kara matsawa kusa da muhibbah tayi tace bana fahimtar abinda kike fada wane ya Fu'ad din? Ya Fu'ad dai dakika sani, a iya sanina bakwa jituwa tsakaninku kamar annabi da kafiri tukunnama shikuma mukhtar din yaxakiyi dashi kinsan babu Wanda yasan kina soyayya a gida bare kuma aji kina soyayya da mutane biyu at the same time tafada haka cike da mamakin abinda muhibbah tafadamata Lumshe idanunta tayi kamar mejin bacci tace soyayyar kwana daya nake nufi dukan wasa ta kaemata ke ki fahimtar dani yadda xan gane bana fahimtar abinda kike fada. Gyara zamanta tayi tace ina nufin mun fada soyayya da ya Fu'ad amma na kwana daya fahimtar da ita tayi yadda lamarin yakasance tayi kafin tadora da cewa kema kinsan bazan juyama mukhtar bayaba har gobe muna tare bazan iya soyayya da ya Fu'ad ba kinsanshi da iyayi ga son girma ga ji da kai kamar dan sarki dariya sukayi gaba daya suka koma class. Se karfe 2:00pm suka tashi daga makaranta a gajiye takoma gida a parlour ta tadda mummy kan kujera ta xauna tana maida numfashi tareda fadin sannu da gida mummy yauwa Shalelen daddynta Gaskiya nagaji dayawa tafada haka tana nufar bedroom dinta kaya tacanza ta dawo dining taci abinci tana ci suna fira da mummy. Bayan ta gabatar da sallan Isha'i taci abinci karfe 9:00pm suka shiga fira a watsapp cikin group din da su na makaranta topic ta kawo musu tsakanin maza da mata su waye sukafi yaudara ai tini ta hargitsa group kowa da abinda ke fadi mata suna maza ne maza sunacewa mata ne se 10 suka gama firar su tashiga toilet ta dauro alwala ta kwanta tareda yin addu'ar kwanciya bacci...........*SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION* *It based on true life story* *Page 3* Dedicated to *my uncle* *Sadaukarwa xuwa ga kawuna Alhaji Aliyu sona Allah yajikanshi ya Mae rahma ya haskaka makwancinsa yasa Aljannah firdaus taxama makoma agareshi ya hayyu ya qayyum Dan Allah duk wanda page din nan ya iso gareshi yamishi addu'ar Allah ya mae rahma* https://chat.whatsapp.com/IVMTZRVmci41jq3pTyzdZs "Bata tashi da wuriba kasancewar yau asabar ce babu makaranta karfe 9:00am agogon dake ajiye a gefen bed dinta ya nuna, Toilet tashiga tayi wanka tareda yin brush tafito gaban mirror takarasa tashafa body lotion bawani make up tayiba powder kawae tashafa se lipstick datasa a labbanta kafin tanufa wardrobe ta dauko kayanta shiryawa tayi cikin doguwar riga na atampha tayi rolling din gyale kayan sun amsheta suyi matukar kyau ajikinta parlour ta nufa. Gidan shiru kamar babu kowa alamun har yanzu basu tashi daga bacci ba, kitchen tashiga domin sama musu abinda xasuci dan tuni cikinta yafara juyi doya tafara ferewa, Alamun tafiya taji haka yasata juyawa taga waye mummy ce tanufo kitchen din dan dora abin breakfast seta cikaro da muhibbah murmushi tasakarmata Ina kwana mummy? Lfy kalau, har kintashi baccin, Natashi banji motsin kowa ba shine nace bari nasama Mana abinda xamu ci kin kyauta Shalelen daddynta cewar mummy. Tare sukayi girkin basu wuce 1 hour ba suka kammala suka jere komae a dining soyayiyar doya da kwae ne se pepper chicken. Break fast din suka soma yi har suka kammala Anas be fitoba mamana jeki kitaso anas cewar daddy, Aa Alhaji ka kyaleshi yunwar cikinshi zata tasheshi kasan indae Muhibbah taje dakinshi yanzu fitina zata tashi kasansu basa zama inuwa daya ko rufe baki batayi ba yashigo bakin shi dauke da sallama, gaeshesu yayi cikin girmamawa kafin yazauna shima yasoma breakfast din ita ko muhibbah tana gama breakfast din takoma parlour ta kunna tv tafara kallon cartoon. Daddy ya suhael yafadamun gobe ze dawo Nigeria cewar Anas are you serious? Muhibbah tafada cike da mamaki harara ya watsamata ai kinsan nasaba miki karya kina kallo amma hankalinki na nan kwabe fuska tayi tace daga tambaya, kunfara ko ya Isa haka yaushe kukayi waya dashi jiya da dadare ne, dauko system kakiraminshi video call cewar daddy. Befi 2 minutes ba yadawo hannunshi dauke da system din ajiyeshi yayi akan table din dake tsakiyar parlourn tareda danna mishi video call Ringing daya ya dauka kamar yana jiran kiransu. Ina kwana big bro? Lfy kalau lovely sister Ya school din, School Alhamdulillah munyi final exams gobe xan dawo Nigeria in Sha Allah, tsalle tayi tana fadin gaskiya naji dadi har na kosa gobe tayi, dauke system din anas yayi yace ke kadai zakiyita magana kibari su daddy suma suyi mana hade fuska tayi kamar xatayi kuka tace please ya anas ka ajiye munkusa karasa maganar seda daddy ya mai magana kafin ya ajiye me kike so na tawomiki dashi Suhael yatambayeta waya da system nake so tafada a takaice, sun kai 30 minutes suna waya kafin tamikama daddy suka gaisa sun danyi fira kadan ita kam mummy tunda suka gaisa bata Kara cewa komai ba ita a dole tana kawaici saboda dan fari ne, sallama yamusu yayi hanging call din. Parlour muhibbah da mummy Suka koma suna fira rabin hankalinta na kan kallon cartoon, daddy da Anas Kuma sun tafi daurin auren dan abokin daddy. "Zaune suke a palour suna fira cike da so da kaunar juna, Abba ina so gobe zanje kaduna me ake a kadunan lafiya ko?" Lafiya kalau gobe suhael ze dawo Nigeria shine nake so naje mugaisa cewar Fu'ad, gaskiya tare ya kamata muyi tafiyan nan dan najima banje kadunaba Kuma akwai abinda naketa so naje nayi amma Allah be bani iko ba amma gobe in Sha Allah tare xamu tafi, shikenan Abba Allah ya kaemu goben lafiya, Amin Abba ya amsa dashi. Abba nima zanje cewar Aesha wani harara Fu'ad ya watsamata dasauri ta hadiye maganar tana sunkuyar da kai, Aa Aisha kibari idan anyi hutun makaranta se kije keda umminki haka ta hakura badan ta soba saboda tasan Koda babu makaranta ya Fu'ad baze bari tajeba tunda tafiyar dashi za'ayi, ita ko ummi dake gefe tace bari ayi hutu muma zamuje murmushi tasake tana fadin tom shikenan ummi Allah ya kaimu da Amin suka amsa suka cigaba da firarsu, shikam Fu'ad tunda sukagama maganar tafiya da Abba ya maida hankalinshi kan wayarshi be kara cewa komae ba sanin miskilancinshi yasa babu wanda yakara cemai cikan ka. Sun dauki kusan 1 hour suna zaune suna firar su kallan muhibbah tayi tace menene tsakaninki da Fu'ad? Tayi maganar cikin sigar tambaya, kamar a mafarki taji maganan saurin juyowa tayi tana kallonta cike da mamakin tambayar data mata tace babu komai a tsakanina dashi illa 'yan uwantaka mummy, bata wani ja maganar ba tace tom shikenan tunda kince babu komai ji tayi gabanta ya fadi cikin sanyi jiki ta nufi bedroom dinta, kwanciya tayi tafara tambayar kanta meyasa mummy tamata tambayan nan kodai ta fahimta wani abu ne haka dai ta dingama kanta tambayoyi ganin babu me bata amsa yasata kwanciya ta runtse idanunta tarasa me zatayi dan tanaji ajikinta mummy sunyi magana da daddy akan magananta da ya Fu'ad kuma sunyi ma alakar su mummunar fahimta dan ba abinda suke tinani bane dan tana kyautata zaton taji wayan da takeyi dashi kwanaki. Ajiyar zuciya ta sauke tana addu'a a cikin ranta Allah ya taimaketa iyayenta su fahimta cewa babu wani alaka a tsakaninta da ya Fu'ad illa alakar 'yan uwantaka. Tana kwance har aka kira axuhur kafin tashiga toilet ta dauro alwala, pray mat tashin fida tagabatar da Sallah addu'o'i tayi kafin ta tashi ta fito parlour, anan zaune tasami mummy sannu da hutawa yauwa, se Ina naga kin ratayo jaka? Ina so xanje gidan su Sumayya ne islamiyyan fa banajin dadi yau bazan iya zuwa ba, tom shikenan kije ki kwanta ba inda zakije tayi maganar tana kallonta. Babu yadda ta iya ta juya ta koma bedroom dinta, waya ta dauko tafara kiran Sumayya ringing biyu tadauka hello kawata ya weekend din ajiyar zuciya tasauke tace lafiya kalau dan Allah ina so kizo gidanmu idan babu matsala, lafiya? Lafiya kalau akwai maganar dana keso muyi ne gashi nafita amma gobe zan shigo in Sha Allah ajiyar zuciya tasauke tace tom shikenan Allah ya kaemu sallama sukayi tayi hanging call din.......*SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* Dedicated to my *lovely Aunty* *Sadaukarwa xuwa ga Aunty Hafeexa wannan page din nakine ummu jafara/Habeebtee uwar gida agurin Abban Jafar Allah yabar so da kauna* https://chat.whatsapp.com/IVMTZRVmci41jq3pTyzdZs *Page 4* "A hankali yake saukowa daga jirgin lumshe idonshi yayi yana sauke ajiyar zuciya a lokaci daya yayinda ya shaki iskar kasarshi daya dauki shekaru rabonshi da ita" A natse yake tafiya hannunshi rike da akwati be ankaraba yaji an fado jikinshi oyoyo big bro ajiyar zuciya ya sauke haba Muhibbah wannan irin runguma ai seki yadda ni yafada yana rabata da jikinshi, Murmushi tayi ta karba akwatin suka karasa wajen dasu daddy ke tsaye. " bude bayan motar yayi yasaka akwatin, shiga motar su kayi Anas yaja suka nufa gida" ****** "Tunda suka fita ta shiga kitchen tasoma girki muryan muhibbah ta tsinkayo tana kwala mata Kira ganin bata parlourn yasata kara sowa kitchen din da murna, Juyowa mummy tayi tana kallonta irin wannan kira kamar makauniya kwabe fuska tayi cikin shagwaba tace Sorry, dama zan fadamiki mundawo ne" batace komae ba tacigaba da aikinta, Tare suka kammala girkin suka shirya dining tsaf. "Kae tsaye bedroom dinshi yashiga yayi wanka, shiryawa yayi tsaf kafin yafito parlourn, A dining