Sashe 6
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
komae ta wanke kwanukan dasukayi breakfast din kafin ta nufi bedroom dinta wanka tayi ta fito ta tsaya gaban mirror tasoma shafa lotion simple make up tayi kafin ta nufi wardrobe ta dauko Kaya tashirya cikin riga da skirt na atamfa ta yafa mayafinta black jaka da takalminta ma black ta nufi dakin mummy Mummy na tafi, toh ki gaeshar da su kice Ina Mata Sannu Kar ki Kae yamma, Tom Sena dawo, Adawo lafiya da Ameen ta amsa tana fita "A compound din gidan sukayi kicibis tana kwala Kiran bala driver kamar baxatayi magana ba tace Sannu da dawowa be amsa ba se cewa yayi Ina xakije? Gidan kawata ta bashi amsa a takaece, wuce ki shiga ciki baxaki ba baki sake take kallonshi tace ya Fu'ad maman kawata ce fa batada Lafiya Kuma na tambaye mummy tace naje na gaesheta" Baxa kiba wuce ki koma ciki ya dube driver yace yi tafiyanka yau babu inda xata se Monday shima baseka xo dawuri ba akwae Wanda xe kaeta, toh me gida abinda drivern ya fada kenan yana barin wajen, rau rau da Ido tayi xatayi kuka tace toh ae na tambaye mummy Kuma Sena je ko a napep ne tafada tana turo baki ganin Yana kokarin xare belt din jikinshi ne yasa ta kwasawa a guje tayi cikin parlourn tana kwala Kiran mummy .......... *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Dedicated to my lovely brother* *Nasadaukar da ragowar pages din Nan xuwa ga my yaya, Angon Fateema Kuma Abban Fateema, har gaban gobe ana kyawun tare* "Zaune suke a parlour suna taba fira rabin hankalinshi Yana kan TV yana kallon news paper" "Abba Ina gama waec xamu je kaduna nida ummi ko? Tayi maganan cikin sigar tambaya, murmushi yayi yace Kae Khadija kullum maganan ki kenan, shagwabe fuska tayi kafin tace Abba yaushe rabon da mu hadu da muhibbah mun Kae 1 year fa ita bata son xuwa garin nan sbd ya fu'ad ya cika takura tayi maganan tana saurin rufe baki" Murmushi ummi tayi tace ae xe dawo xaki maemaeta abinda Kika fada, dariya tasa tana girgixa Kae tace nasan yanxu tana can tana kwasar bakin cikin xaman ya fu'ad a gidan daddy har na hango yadda xata koma xaman bedroom dinta Koda yaushe ta karashe maganan tana cigaba da sakin dariyar mugunta, itama ummi dariyar take sbd tasan abinda xe faru kenan dan tasan halin fu'ad sarae musamman tsakaninshi da muhibbah da basa wani jituwa, murmusawa shima daddy yayi yana tina darun muhibbah, shiru yayi yana tinani Dan Allah daddy kayimun alkawari xamu je da ummi idan na gama exams ta katse Shirun, Allah ya kaemu gaba dayanmu xamu tafi ihun murna tasa tana nufan bedroom dinta da gudu. "Seda ya nunfasa kafin yace umminsu juyo da hankalinta gareshi tayi tace na'am alhaji, xuwana kaduna mun yanke hukuncin hada fu'ad da muhibbah aure! Gabanta ne ya yanke ya fadi tayi shiru takasa magana duk da ta dade tana tinanin hkn xata iya faruwa tasan halin Abba xeyi wuya ya bar fu'ad ya auro wata a waje, Lafiya kikayi shiru baki ce komae ba kakalo murmushi tayi tace naji abun ne yaxomun baxata toh umminsu banda abinki gida be koshi ba a Kae ma dawa ae gara muyi tuwo na maena xumincinmu yakara danko Kuma kinsan tsakanin fu'ad da muhibbah babu wata jituwa auren ne xesa su fahimce juna, toh Allah yasanya alkhaeri abinda ta iya fada kenan har ga Allah ba wae Bata son auren nasu bane kawae tasan akwae matsala ne kafin su jitu xa'aji jiki sedae babu yadda xatayi tasan tunda Abba yace toh baxe canxa wata magana ba, amsawa yayi da Amin! Kafin ya sanar da ita akan tafadama 'yan uwa da abokan arxiki Kuma tafara shirye shiryen ta sedae karta yarda Khadija taji labarin nan amsawa tayi da toh dg Nan babu Wanda ya Kuma magana. **** "Dakin mummy ta nufa tana kwala Mata Kira, a tsorace ta mike ta riketa tana fadin muhibbah Lafiya, meyafaru taje romata tambaya? saboda yadda gabanta ya fadi "Ba ya Fu'ad bane ya koroni wae babu inda xanje tayi maganan tana sakin kuka, ajiyar xuciya tayi ta koma ta xauna har ga Allah ta tsinkamata xuciya tayi tinanin wani Abu ne yafaru yadda taji ihun ta, wae ke muhibbah yaushe xaki girma ne saboda kawae ance baxaki fita ba shine kike wannan ihun? Haba mummy bake Kika ce inje ba shine xe ce baxaniba se kace uban... Kafin takarasa taji mummy ta bige Mata baki dasauri ta dafe bakin tana sakin sabon kuka, da gudu ta fito daga bed room din a parlour suka ci Karo ya kashe Mata Ido yana murmushin mugunta "Bedroom dinta ta shige ta fada gado ta rushe da kuka wannan wane irin musiba ne ita da gidansu a takuramata Kuma su daddy laefinta suke gani, tashi tayi ta Murda ma dakin key ta dawo ta kwanta tana tinane tinane a haka har bacci ya kwasheta. " Har a halin gidan suka gama dinner Bata fito ba, Anas ne ya keta faman buga dakin amma taki budewa dole ya hakura ya kyaleta, wayanshi ya dauka yaturamata text "Dan Allah auta ki fito kiyi dinner ya hado da emojis na alamar damuwa Karar shigowar sako wayarta yasata janyo wayar ta duba, tashi tayi jiki a sanyaye ta nufi parlourn suna xaune suna taba fira rabin hankalinsu duk yana kan wayoyinsu batace musu kala ba ta nufi dining ta Dan ci abincin kadan kafin ta dagama Anas hannu tace bye murmushi yayi shima yace bye "Runtse idonta tayi tana jin xuciyarta na Mata xafi, wayarta ce ta dauki Kara a hankali ta Kae hannunta ta dauka idonta a rufe jin muryan mukhtar ne yasata saurin tashi xaune tana sakin murmushi "Barka da dare ya mukhy, barka dae gimbiyata fadada murmushinta tayi har hakoranta na bayyana fatan kana Lafiya, uhmmm Amma nayi missing dinki, yaushe xaki bani dama naxo gida naga daddy ne? Nagaji daxaman kadaecin nan rufe Ido tayi wae kunya tace very soon in Sha Allah Kar kadamu saura kiris "Murmushi me sauti yayi yace toh kafin lokacin Ina so naga kyakkyawan fuskarki, juya Ido tayi kafin tace tom Monday mu hadu a school mana, mungama mbais waec ne kawae mukeyi yanxu murmushin jin dadi yayi yace Tom shikenan Allah ya kaemu Monday Lafiya, da Ameen ta amsa kafin tafada mishi time din daxata fito paper......... *Aminiyar ango*[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 11* Toilet ta nufa ta dauro alwala tafito tayi nafila tana rokon ubangiji ya sassautamata abinda takeji a xuciyarta kafin ta kashe bulb din dakin ta kunna dum light ta kwanta Tunda ta tashi take neman time table dinta na waec amma bata Gani ba ta hargitsa ko ina babu alamarshi, Rai a jagule ta shirya cikin sauri ganin takusa makara ta fito parlour babu kowa hakan yamata dadi, bedroom din mummy ta nufa ta gaesheta harta juya mummy ta kirata na'am ta amsa a taikace kinyi breakfast? Aa mummy idan muka fito paper zan siya wani abu naci seda ta numfasa kafin tace toh Allah yabada sa'a amsawa tayi da Ameen kafin ta juya ta wuce. Da maamaki take kallon compound din ganin bataga bala driver ba Kuma tasan baya makara wajen aikinshi Kuma ga motan kaeta school a ajiye, kodai bashida lafiya ne ko Kuma mummy ta aikeshi tayi tinanin a zuciya take maganan ashe yafito fili "caraf taji yace nii nace yau yaje ya huta ni zan Kai kanwata da kaina yayi maganan yana dage mata gira hade da murmushin mugunta" "Kauda kai gefe tayi tarike kugu tama rasa me zatace mishi saboda yagama kaita bango idan tace zatayi magana a yadda takejin zuciyarta to tabbas zatayi abinda har su daddy se sun jibgeta" Wuceta yayi Yana cilla key din motan sama Yana cabewa kafin ya bude mazaunin driver yashiga, zuciyarta ce tabata shawarar tashiga ya kaita saboda karta makara, jiki babu kwari tawuce ta bude bayan motan zata shiga yace waye drivern ki, bataja zancen ba ta bude gaba ta zauna tanajin wani kuka na zuwan mata amma ta hadiye a guje ya ja motar seda suka hau kan titi kafin ya rage gudun ya kunna kira'an sheik sulaiman yana bi yana sakin murmushin dashi kadai yasan ma'anarshi yaga school din amma da gangan yayi gaba da motan "Juyowa tayi ta kalleshi ya dauke kai kafin tace Yaya mun wuce school dinfa se a lokacin ya kalleta au ai bansaniba ita dai bata karacewa uffan ba saboda yagama kaita bango juyo da motan yayi suna zuwa gate din school din tayi saurin cewa mun iso gudun yakara wucewa da ita tunda taga Jan magana yake, 2k ya ajiyemata akan jiki yace kisiya snacks kici kar ulcer ta kamaki ayi exams lafiya yafada Yana dagemata gira, bude motan tayi tafita ta buga kofar da karfi tajuya tashige ciki sauri sauri ta shige hall din tazauna seat dinta. Basu fito paper ba se 12 daker tagama exam din saboda wata yunwa da take rarakar cikinta, cafeteria suka karasa suka siya snacks da drink kafin suka koma main class dinsu suka zauna suka soma ci summaya nata Janta da fira ita dai babu abinda take cewa daga eh se aa ganin hakan yasa sumayya tsuke bakinta tayi shiru danta fahimta aminiyar tata bata cikin mood me dadi *Fu'ad* Tun bayan yasauketa school ya juya ya nufi company a office yasamu Suhail yataimaka mai suka rage aiki daganan suka shiga fira suna kwasar dariya, duba a gogon dake daure a damtsen hannunshi yayi kafin yayi saurin mikewa yana cewa bari zanje nadawo, aa katsaya mutafi tare ai lokacin tashina yayi "Kajimun mutum dama tare dani kazo kabari se 4 katawo da daddy, Aa gaskiya bazan jirashi ba anjima bala zezo yayi driving dinshi, toh nikuma bazaka bini ba akwai inda zan biya daga hk yafice yabarshi baki sake yana bin bayanshi da kallo *Muhibbah* Wayar tace tadauki kara a hankali ta Kai hannu tadauka ta mannata a kunnenta "Barka da rana Abbana, Barka dae maamana fatan kina lafiya kamar jira take yayi magana kukan da take ta dannewa