← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 69

Sashe 59

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tambayan ina Muhibbahn akace tana kwance batada lafiya. Anci ansha, yaro yaci sunan Fu'ad ana kiranshi da Aadil, murna gurin Muhibbah ba'a cewa komai akwati guda ta ciko da kaya, bini bini ta daukeshi ta manna mai kiss a kumata. "No wonder! Shiyasa yaron nan yazo a kyakkyawa, Kuma tunda naganshi naji ina mutuwar kaunar shi ashe sunan habeebeee ze ci". Shima Fu'ad yayi bajinta ya kashe naira. A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, Cikin Muhibbah yashiga wata hudu har ya soma fitowa, tadena amai, sedai ba ko wane irin abinci take iya ciba, ta soma jin karfin jikinta sedai Kunsan yanayin jikin masu ciki yau lafiya gobe babu, Fu'ad kullum cikin karfafa mata guiwa yake da nunamata laulayi ne kawai keda wahala amma wajen haihuwa bazataji wani wahala ba. Shirye shiryen komawa school ta shigayi, dan yau hutun su ya kare..................... AMINIYAR ANGO * Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD* *AMINIYAR ANGO* *Page 55* Tana tsaye gaban wardrobe tana faman neman kayan da zata sa, ko wanne ta dauko idan tasa setaji ya matseta. Hugging dinta yayi tabaya ya zira kanshi a wuyanta yana shin Shinar sihirtaccen kamshin ta. Dago Kai tayi tana kallonshi ta sakarmai murmushi "Maman baby ya akayi ne? Tun dazu inata jiran fitowarki najiki shiru" Kukan shagwaba tasa mai "Uhumm uhummm! Baka gani narasa kayan dazan saba, duk wanda na dauko se inga yayimun kadan". "Toh ai kece kinzama 'yar lukuta" yayi maganan yana dariya "Toh ba babynka ne ya maidani haka ba" tayi maganan a shagwabe. "Shiyasa nace idan babyn nan yazo se na rankwashe shi, saboda ya wahalarmun dake dayawa". "Ai yana fitowa ni zan fara mintsinanshi, kafin kai Kuma seka rankwasheshi tunda baya jin magana". Ta karashe maganan tana dariya. hannu ya kai ya shafa cikinta "Anya kina son babyn nan naki kuwa?" Baki ta tura "Ni bana wani sonshi, ai shima ba sona yake ba tunda yana wahalar dani". "Waya fadamiki baya sonki? Akwai dan da baya son mahaifiyar shi ne? Ko kuma akwai mahaifiyar da take kin danta? Duk da dai yau nafara ganin mahaifiyar data ce bata son babyn ta". Yafada yana dagemata gira "Kaima fa Yaya sheda ne, kasan ba karamin wahalar dani yake ba, dan haka ni babu ruwana dashi kawai dan nariga nama alkawarine shiyasa ma zan haifoshi, amma daga nan na gama nawa aikin na fita, ko kaba mummy shi ko kaba Ummi ko Kuma Aunty Suhailat ta hada da Aadil ta shayar dasu". Murmushin gefen baki yayi tareda girgiza kai, shirmen Muhibbah se ita. Wata doguwar riga me roba ya dubomata. "Gwada wannan maybe ya miki" Karba tayi ta zira, ta kalleshi, tayi dariya tana kai hannunta kan cikinta "Yaya kalla yadda rigar nan tasa cikina yayi Kato kamar wani kwallo". Shima dariya yayi, yana dora hannunshi kan nata "babu ruwan riga bloody, dama cikin ki a haka yake" "Amma harda rigan kaga tanada roba shiyasa ta kara fito dashi, salan naje school ai ta kallo na, su Umaina suyimun dariya". "Nikam nafi son haka, kinga yanzu duk wanda ya ganki yasan ke matar aure ce, base an fadamishi ba" Yayi maganan yana kwafa, tino sauban da yayi, dan bayajin haushin malam mukhtasir kamar sauban saboda ya daura laifin a kanshi, tun farko da yaje karba mata admission letter, be sanar mishi tanada aure ba da beyi yunkurin kulata ba. Zatayi magana ya rikota "Let's go! Ki bar maganan su Umaina, suma ai mata ne idan layi naja ze zo kansu" Yayi maganan yana mikamata hijjab. Yatsina fuska tayi "Eyyyaaa Yaya bazan iyasa hijjab ba zafi nakeji, kuma kace mutum baze sha fanka ba bare naje da hand fan". Beyi magana ba ya zaro wani gyale ya mikamata, ta yafa suka fito rike da hannun juna. Basu fi 20 minutes ba suka kammala breakfast suka fice Bakin gate din school yayi parking, ya ciro facemask ya Mika mata, ta bata fuska "Dan Allah Yaya kayi hakuri, bazan iya sa facemask ba, a haka ma numfashin baya isata yadda nake so". Kai ya Jinjina, yana kara jin tausayin ta na kamashi, kaunarta na ninkuwa a zuciyarshi. kudi ya mikamata tayi godiya, ta fito tana daga mai hannu ta shige cikin school. Koda tashiga class tajima su Umaina basu iso ba, balance tayi a seat, ta ciro tsamiyar birinta tana sha. Kamar hadin baki a jere su ukun suka shigo, da fara'arsu suka karaso ganganta. Itama da fara'arta ta mika musu hannu suka gaisa. "Kai wllhi bamuda kirki, ace ayi hutu har a dawo ba'a ziyarci juna ba" "Bari Fatima nima seda nayi maganan nan a zuciyata, gaskiya ya kamata mu gyara" "Allah yabamu iko" "Ameen" duk suka amsa dashi. Tare suka fito daga hall din, gaba daya duk ta tsargu ji take kamar idanun kowa a kanta yake. Waro idanu tayi, dasauri ta kai hannu ta tabo Umaina, a mamakance tace, "Umaina! Aesha!! Kunga abinda nake gani kuwa?" Duk tsayawa sukayi suna kallonta, "A ina?me kika gani?" "Dama Fateema nada aure?" Saurin kallon Muhibbah tayi, itama ta zaro ido tana murmushin farin ciki "Wllhi na dade ina zargin haka, tun lokacin da sauban ke binta tana mai wulakanci naji suna cewa kar Allah ya kamata tun a lokacin nasa ayar tambaya, kawai dai ban tabbatar ba ne shiyasa nabarshi cewar ko kuma ta kusa aure ne suke boye mana. Masha Allah, Allah ya fito mana da babyn mu lafiya, babu abinda yasani farin ciki a yau kamar wannan lamari. Mun kusa zama mothers". Takarashe maganan tana dage ma Muhibbah gira Tsaki taja "Ku kam wllhi kuncika sa eyes, yaushe ma cikin yayi girman da har kuka hangoshi, nidai ba wannan ba, mu biya cafeteria nasamu abinda zanci, yunwa nake ji" "Toh ya muka iya, ai yanzu kinzama a lallaba auren zamani" Aesha tafada tana dariya Rumaisa tace, "Amma wllhi kun rufemu, bancin cikin nan ya tona da zamu dade bamu gano ba, nidai naga surname dinku ba daya ba nabada cousin sisters ne, ashe kam na cinka". "Toh yanzu da lokacin sanin yayi ba gashi kun sani ba, Kudai ku fara shirye shiryen suna dan ranan akwai shagali" cewar Aesha dariya suka yi suka karasa, ta siya meat pie da drink suka jira tagama ci kan suka karasa bakin gate. Wanka tayi ta dauro alwala tazo tayi sallah, ta nufi dakin Fu'ad ta dauki jallabiyarshi ta zira ta shiga kitchen ta dafa indomie ta cika yaji, tadawo kan kujera ta zauna tana ci, yunwa takeji sosai kamar bataci snacks a school ba. Wayanta ne ya dauki kara tayi picking tareda mannata a kunne. "Aesha ya akayi ne?" "Albishirinki?" "Goro, tasamu kenan? Bani nasha" "Yanzu Abba ya kira Ummi yake fadamata, Sunje nema ma ya Suhail auren Aunty zeeee, a gurin aka biya sadaki aka gama komai. Har sunyi fixing time". "Dan Allah fa?" "Wllhi kuwa, nima yanzu ummi ke fadamun" "Masha Allah! Kice akwai cin uwar sabada, fatana dai Allah yasa lokacin na haihu". "Ameen, idan ba haka ba ayi bake" "kedai bari sister cikinan yana maidani baya a abubuwa, yanzu ko kwalliyar arziki baya bari nama hearty, sedai naita fama da jallabiya, ga jallabiyar hearty duk sun mun yawa har suna sharar kasa" dariyar mugunta tashigayi, seda tayi me isarta kan tace "Sorry maman baby! Gobe ki tambaya Yaya idan muka tashi school se mu biya ki kaima tellor ya dinkamiki dogayen riguna, yadda zakiyi balance. Daga nan se mu biya gidan su Aunty zeeee tunda duk hanya ne". "Ni wllhi banji haushi ba, kiyi dariyarki kwana nawa ne idan layi naja ze zo kanki. Amma inaji haka zanyi, sedai Idan mun hadu gobe school". Daga haka sukayi sallama ta ajiye wayan Ganin 5 tayi ta mike tashiga kitchen, abinci mara nauyi ta dafa mishi ta juye a food flask ta hada mishi zobo ta zuba kankara ciki ta jere a dining, ta nufi dakinta. Wanka tafito, tayi sallahn magrib seda tayi isha'i ta nade pray mat din. Wardrobe ta nufa ta dauko vest tasa ta kawo wandon da iya karshi cinyanta ta zira, tashafa humra ta kawo turare ta feshe jikinta ta nufa parlour. Shigowarshi kenan karar takalminta yaja hankalinshi gurin, idanunshi a kanta yaja ya tsaya yana kallon yadda take taka staircase din a yangance, ko ina na jikinta na motsawa. Suna hada idanu ta saki murmushi ta karasa ganganshi ya wara hannu ta fada jikinshi. Hannunshi ya mayar bayanta ya rungumeta tsam a jikinshi "Sannu da dawowa my heart" "Kina lafiya maman twins?". Dariya mara sauti tayi "Nikam rufamun asiri, dayan dai ya ishemu Alhamdulillah" tafada tana raba hug din, ya rike hannunta suka karasa dining. Yana zama yace, "ko triplet Allah yabamu wllhi ina so" Hararan wasa ta watsamishi "Eh tunda ba tajikin ka zasu fito ba ai dole kafada haka". Dariya me sauti yayi "Injiwa yace bata jikina suka fito ba?" murmushi kawai tayi saboda ta gane abinda yake nufi, ta dauki plate tayi serving dinshi ta turamai gabanshi, ta dale cinyarshi. Abincin ya dibo ya kai bakinta tayi saurin dauke Kai, "no! ni kai na dafamawa, bazan ci ba" "Shine kika kirani Kikace base na siyo abinci ba, yanzu ke me zakici?" "Kar kadamu, nikam banajin yunwa, zobon ne dai dazaka taimaka mun kabarni nasha ko 1 cup ne dana kwana inasama albarka". Tafada tana marai raice fuska "Aa, kigama wayanki, meyasa kafin kisa kan kara baki diba naki ba?" "Ni ai me sanyin ne ya birgeni" "Hakanan ko zaki hakura, it will affect your baby". Baki ta tura, a shagwabe tace, "komai baby! tun bezo duniya ba har kafi kaunarshi a kaina" "Yau naga uwa me kishi da danta" "ba wani kishi, naga an fara nunamun wariyar launin fata ne tun yanzu". Dariya yayi, ya dauketa suka haura dakinshi Taimaka mai tayi, ya cire kayanshi ya daura towel. Taso ta Kuma yin wanka ya hanata wai zatayi mura, dole ta dawo gefen bed ta zauna Yana fitowa yayi sama da ita, tsakiyar gadon ya kwantar da ita Shima ya kwanta gefenta tareda janyota jikinshi. Dan turashi tayi ya kwanta yana kallon ceiling, ta kwanto kan kirjinshi. Hannunta ta tura cikin sumarshi tana yamutsawa, ta hade bakinsu tashiga aika mai da hurt kisses. ta shiga yawo da hannunta duk
Chapter 59 · 0% Book details