Sashe 29
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Bakinta dauke da sallama tashiga parlourn, ganin bataga kowa ba ta nufa dakin Aesha a kwance ta sameta tana faman sheka dariya, har Muhibbahn ta matso kusanta bataji zuwanta ba Hannu ta Kai ta zare wayan, a firgice ta dago ta Kalle Muhibbah suka sakarma juna murmushi "Laa sister yaushe kika shigo?" "Uhmmm ina Zakiji shigowa ta kina waya da abin kauna" "Ni nace miki da saurayina nake waya?". "Oho koma dai waye idan tayi wari ma ji" ta Kai karshen maganan tana mika mata wayan. "Bazama tayi warin ba" Wayan ta kara a kunne sukayi sallama kana tayi hanging call din. "School mate dina ne, senior na ne a school bakisan Yakub bane ko lokacin Muna school mutane dayawa na tinanin akwai alakar soyayya tsakaninmu kuma babu wata alakar data wuce ta friends tsakanina dashi". Murmushi tayi tana girgiza Kai "Bazan tabbatar ba nima, lokaci ne ze tabbatarmun da gaskiyar abinda ke tsakaninku, amma Allah ya taimakeki kar a rabaki da abinda ki kafi kauna" tayi maganan tana rau rau da ido kamar zatayi kuka. Ajiyar zuciya tayi dan tasan inda ta dosa "kowa da kaddararshi Muhibbah duk yadda rayuwa ta zoma bawa toh ya bida ita a haka yayima Allah godiya" Ka Kalo murmushi tayi tariko hannun ta "Muje kar Ummi tayi fushi da diyarta, banje bedroom din taba nayo nan". A parlour suka tarar da a halin gidan guri tasamu ta zauna tace "Ummi ina wuni" tafada cikin sanyin jiki tana yin kasa da Kai, ji tayi tana masifar Jin kunyan ummin. "Lafiya kalau Muhibbah, ya bakon guri". Yatsun hannunta ta shiga wasa dasu batare da tace komai ba. Dariya Ummi tayi "Aa wai yau ni Muhibbah ke Jin kunya" gyalenta ta janyo ta rufe fuska takasa cewa uffan. Aesha tace "Ummi so take kice kinyi sa'ar sirika, alhalin munsan komai". Dukan wasa ta kaimata tana harararta. Dakuwa Ummi tamata "Toh da banyi sa'ar sirikar bane, rabu da ita Muhibbah tasan ke ba irin ta bace mara Jin magana" gwalo tama Aesha tana dariya kasa kasa. Shikam Fu'ad bazakace yana parlourn ba hankalinshi na kan wayarshi yana Jin abinda sukeyi amma ko dago Kai ya Kalla idan suke beyi ba bare ya nuna yaji abinda suke cewa. "Aunty Asma'u yaushe zaki koma gida?". "Yau naso na tafi Aunty Maiminatu ta dinga Jana da fira ta hanani tafiya kinga ita dazun nan tayi tafiyanta gidanta, Suhailat ma mijinta yazo ya dauketa sun barni ni kadai, Amma gobe da wuri zan tafi in Sha Allah" "Eyyyaaa big brother fa ko shima ya tafi ne?". Aesha tace "Ya Suhail ai tun jiya ya tafi daddy nata kiranshi aiki yamai yawa". "Allah sarki Mummy na Aunty Asma'u goben ki biyo mu tafi please" Saurin dagowa yayi ya kalleta kawai idanun su ya sarke dana juna hawayen dake kwance a idanunta suka silalo, wani siririn tsaki yaja ya mai da kanshi ga abinda yakeyi. Dariya sukayi gaba dayansu Aunty Asma'u tace "Sannu Muhibbah toh se kin dawo" Ummi tace "Ashe dai keda Aesha duk tafiyarku guda wajen shirme, Amma gaki ga mijin naki a gefe idan ya yarda toh se kin dawo" ta karashe maganan da zolaya. Aesha tace "Ummi kyaleta zanma rakata air port idan kinje wata nawa zakiyi ki dawo" tayi maganan tana dariyar mugunta. Harara ta watsamata tana Shirin yin magana Abba ya kutso kanshi parlourn bakinshi dauke da sallama duk suka amsa ya nemi guri ya zauna suka shiga mai sannu da zuwa. Se yanzu Fu'ad ya dago yama Abba sannu da zuwa tare da gaisheshi ya amsa cikin kulawa. "Abba ina wuni" "lafiya kalau maamana, ya bakunta?" Kasa tayi da kanta gaba daya se taji kamar ta nitse a kasa kunyan Abban yakamata. Ummi tace "Alhaji munfa zama sirikan Muhibbah yanzu kunyarmu take ji" Na lura da haka tunda har na shigo Muhibbah Bata zo da gudu ta tarbeni ba, Zo nan ki zauna kusa dani maamana ni ba sirikin ki bane Abbanki ne ni har yanzu, kin ji ko?". "Kai kawai ta gyada tana zama gefenshi inda ya nuna mata, Allah yasani gaba daya kunyarshi shida Ummi takeji gani take kamar zasuyi tinanin ko wani abu yashiga tsakaninta da ya Fu'ad alhalin Kuma ko maganan minti daya be hadasu ba. Tashi Abba yayi ya nufa dakinshi seda ya watsa ruwa ya shirya kana suka tafi masallaci da Fu'ad da Ammaar basu dawo gidan ba seda akayi isha'i. Duk mutanen gidan dining suka hallara domin yin dinner, ita dai Muhibbah cakulan abincin kawai take har yanzu bata dawomata kamar baya ba kawai addu'a take Allah yasanya yamata zuciyarta "Aunty Muhibbah ya bakyacin abincin" Taji muryar Ammar na mata magana.Dan zaro ido tayi "Kai ya Ammar wane irin Aunty" tafada tana rufe fuska. "Ehmana kefa yanzu duk family nan kece babba girma ya kamaki tunda kina auren babban Yaya". Hada ido yayi da Fu'ad ya watsa mishi wata uwar harara dinke bakinshi yayi be kara cewa komai ba. Abba yace "Idan kun gama dinner a sameni a parlour" yafada yana mikewa. Mutanen gidan gaba daya sun hallara parlourn Abba Fu'ad da Muhibbah zaune gaban Abba da Ummi, Abba yafara nasiha "Fu'ad ga Maamana nan a matsayi na daban a gurinka kai ne babba Kuma Kaine namiji ka kasance me adalci ga iyalanka kayi kokarin sauke hakkinsu ka kyautata musu Allah seya kara budama, ban yarda da duka ba idan wani laifi tama daya gagara ku sulhunta a tsakaninku toh kasanar dani amma idan naji labarin duka zanbatama rai fiye da tinaninka" seda yaja fasali kan yace "Fatima" Saurin dago kanta tayi ta kalleshi da jajayen idanunta da suka rine tsabar kuka Jin ya kira sunanta Kai tsaye tasan maganar daze mata me Muhimmanci ce dan ko Muhibbah baya kiranta dashi bare Fateema "Na'am Abba" ta amsa da dasashirya muryarta data dishe tsabar kuka "Gaki ga yayanki matsayin mata da miji kiyi mishi biyayya kiyi kokari ki sauke duk wani hakki da Allah ya doramiki kisani aljannar ki na karkashin kafan mijinki dan haka ki bishi, idan har yayi miki laifi kisanar dani zanyi kokarin ganin komai ya dai daita, Allah ya muku albarka yabaku zaman lafiya Allah yasa muyi alfahari da ku". Ummi ce ta juyo garesu "Muhibbah zan fara da cewa kiyi hakuri domin shi zaman aure dan hakuri ne har yau har gobe muma iyayenku hakuri muke matukar kikasa hakuri a zaman aurenki toh zaki zauna lafiya da mijinki amma akasin haka Koda yaushe za'a dinga Jin kanku, karki kasance me yawan Kai kara domin mu da kuke kawomana kara zamu gaji sannan Kuma zaku manta da wani abu ya hadaku amma mu munanan rike dashi, kizama me kula da dukiyar miji banda almubazaranci kidinga tattala kayan miji, kizama me biyayya ga mijinki indai kika dauki halayen mahaifiyar ki mijinki baze taba kuka dake be, domin mummynku mace ce me hakuri da kauda Kai da tsananin biyayya, ki zauna lafiya a gidanki Allah ya albarkaci aurenku yabaku zuri'a dayyiba". Hannu Muhibbah takama ta damka a hannun Fu'ad, wani shork sukaji a tare suka dago idanunsu ya sarke dana juna kasa tayi da kanta tana shasshekar kuka, Ummi tace "Ga Amanar Muhibbah a yanzu bata da Wanda yafika kusanci da ita, banda duka matsayinta na yanzu ya banbanta dana baya, ka kula da hakkin matarka kar inji kar in gani Allah yamuku albarka yama aurenku albarka yabaku zuri'a dayyiba". Gaba daya kowa jikinshi yayi sanyi sautin kukan Muhibbah kawai ke tashi "Fu'ad ku tashi ku tafi dare yayi" Jin jina Kai yayi ya mike rike da hannunta yana musu godiya kafin yamusu seda safe. Seda yazo shiga motan ya sake hannunta ya zagaya yashiga itama tabi dayan bangaren tashiga ya yaja motar yafice daga gidan. Babu abinda ke tashi a motan se sautin kukanta, waigowa yayi ya dan kalleta tayi saurin rage sautin kukanta, Jin kukan na hawa mai kai ya gangara gefen titi yayi parking ya juyo yatsareta da birkitattun idanunshi masu tsoratata "Will you shut up! Kinyimun shiru ko sena saukeki anan" hannu tasa ta toshe bakinta dan tasan ba karamin aikinshi bane yabarta nan din tunda ya furta gashi sunyi nisa da gidan Abba. Dogon tsaki yaja ya koma kan titi ya ja motar suka dau hanyan gida........[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 35* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Suna isa gida kowa yayi dakinshi, towel ta daura tashiga toilet wanka tayi ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta haye bed, wayanta ta janyo tashiga watsapp suka hau chatting da Aesha seda taji idonta tsabar bacci kafin tama Aesha seda safe ta kashe datan ta kwanta batafi 5 minutes ba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita. Yana shiga dakinshi wanka yayi ya zauna a gefen bed ya janyo karamin center table dake dakin ya daura system dinshi a Kai yafara aiki seda yaga yaci karfin aikin kana ya kashe system din ya kwanta. 10 minutes after 7 ta tashi kafafunta ta ziro kasa tasa takalmi tashiga toilet ta wanke fuska ta nufa kitchen, dube dube tashiga yi a kitchen din komai