Sashe 30
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a jere gwanin sha'awa takai hannu ta bude freezer taganshi cike da kayan bukatun girki kamar dama tun can akwai mutane a gidan duk abinda take bukata akwaishi cikin freezern Kaza ta dauko ta wanke tasa a tukunya ta daura akan gas ta zuba garlic, citta, cloves, seasoning and spicy ta rufe tukunyan ta koma upstairs ta fara gyara dakinta seda ta gyarashi tsaf kana ta sauko daga stairs ta gyara parlourn kasan ta fesa room freshener ta kunna turarukan wuta parlourn ya dauki kamshin dadi. Koda ta koma kitchen din tasamu har kazar ta nuna ta kashe gas din ta sauke tukunyan, bowl ta dauko ta cire naman daga roman ta zuba man gyada a pan ta Dora a gas tafara soya Kazan, seda tagama suyan, tayi grating kayan Miya sannan ta dora karamin tukunya a gas ta zuba man gyada, sannan ta zuba kayan miyan ta kawo spicy da seasoning ta zuba ta yanka albasa me dan yawa ta zuba ciki ta kawo soyayyen Kazan ta zuba ta dauko roman ta zuba kadan ta juya kana takawo murfi ta rufe pot din 5 minutes ta bashi sannan ta kashe gas din. Irish potatoe ta dibo ta fere ta yayyankashi a tsa tsaye ta fasa kwai a bowl ta shiga tsomashi cikin kwai tana soyawa, ta zuba a wata hadaddiyar food flask ta shirya dining din, ta nufa dakinta. Wanka tayi ta shirya cikin atampha dinkin borno style straight skirt se riga iya guiwa taji stones ta feshe jikinta da turare ta nufo parlourn se zuba kamshi take. A dining ta sameshi a zaune yana danna wayanshi, lallaima mutumin nan ni kake zaman jiran na zuba ma abinci to da ban girka ba fa tayi maganar a cikin ranta, wata zuciya tace mata da bakiyi ba ai da se kisan abinda zaki fada mai ya hanaki yin breakfast din. Karasawa dining din tayi daf dashi ta tsaya tace "Ina kwana" "Lafiya" ya amsa da kalma daya batare da ya dago ya kalleta ba Plate ta dauka ta shiga zuba mishi soyayyan potatoe da chicken pepper soup ta ajiye a gabanshi ta dauko wani plate din tayi serving kanta taja kujera tazauna tashiga cin abincin takasan ido yake kallon yadda take cin abincin a natse cikin sanyin jiki, yana Kai abincin baki ya dan dago Kai ya kalleta suka hada ido ji tayi gabanta ya yanke ya fadi ta rasa dalilin dayasa duk lokacin da zasu hada ido se gabanta ya fadi Dauke idonshi yayi daga kallonta ya dan ja siririn tsaki ya cigaba da cin abincin shi, yana gamawa ya mike ya fice daga parlourn batareda yace mata uffan ba Mikewa tayi ta tsaya jikin window parlourn seda taga yaja motarshi ya fice kana ta girgiza Kai, yaushe za'a hada wannan me fadin ran da Mukhtar ina bazasu taba haduwa ba ma, tattare kayan tayi ta Kai kitchen ta wanke kayan da aka bata ta maida ko wanne mazauninshi. Handle din kofan ta kama se tazo zata murda seta fasa babu abinda kirjinta yake se bugawa gani take idan tashiga dakin zata ganshi a ciki ko Kuma yazo ya ritsata a ciki, shahada tayi ta murda handle din kofar ta shiga kamshin turarenshi na mufaddal ne ya daki hancinta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, dakin tsaf tsaf Shima babba ne girman su kusan daya dana ta furnitures din dakin white colour hatta curtains din dakin white, bed sheet ta canza mai ta gyara dakin duk da ba wani dirty yayi ba ta dauko burner ta jona tasa turare ta fesa room freshener kana ta kullo dakin ta fito Bed dinta ta fada tashiga chatting Aesha ke bata labarin tasamu admission a (AUN) Apti American university. "Nifa?" "Toh gaskiya banji Abba ma yayi maganan school dinki ba. Saurin mikewa tayi daga kwanciyar da take, Jin maganan ta watsapp baze mata ba yasa tashiga dialing numbern Aesha, Ringing biyu ta dauka "Hello! Matar Yaya" "kina nufin Abba ko maganan school din nawa bayayi?" "Eh gaskiya banji yayi maganan school dinki ba nadaiji yana cewa ya Fu'ad ze neman miki school din da yake so" Bata barima ta kai karshen maganan ba ta kashe wayan Numbern Abba ta shiga dialing be dagaba seda ya tsinke kafin ya biyo call din tana dauka tasa mai kuka, hankalinshi ne ya tashi "Maamana lafiya?, me ke damunki?, yayanki ne ya miki wani abu? Ko dukanki yayi?". Ya jero mata tambayan a kidime "Abba Aesha tace "ansama mata admission" amma wai banda ni" ta Kai karshen maganan tana shasshekar kuka "Toh miye abin kuka anan, kema za'a sama miki in Sha Allah, Amma kiyima yayanki magana seya nema miki a school din da ya mishi" "Abba nafi son school din da Aesha tasamu" "Kima yayanki magana idan hakan ya mishi shikenan" yana Kai nan ya kashe wayan, yasan ko yasama mata admission a (AUN) ba lallai Fu'ad ya barta taje school din ba ze iya cewa gara yasama mata school a nan jimeta. Kuka taciga da yi Allah yasani bazata iya ma fu'ad magana ba tsoro takeji gashi bata da numbernshi bare kota text message ne ta tura mai sako, seda taji kiran sallah kana ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala ta zo ta gabatar da sallahn azuhur. Qur'an ta dauko ta karanta ta dan kwanta tayi bacci seda tayi la'asar kana ta sauko kasa, karfe biyar tashiga kitchen tafara Shirin dora dinner. Kasancewar tasan baya cin abinci me nauyi da dadare yasa ta shiga shirya soyayyiyar taliya Nikakken naman kaza ta dauko bowl ta zuba aciki kawo spices da kayan Miya ta zuba tayi mixing dinsu tazo tayi moulding dinshi tasa a oven kafin ya gasu ta dauko tukunya ta daura a gas ta zuba ruwa takawo gishiri da man gyada ta zuba ta rufe seda ruwan ya tafasa kana ta zuba taliya ta barshi ya tafasa for 8 minutes sannan ta juyeshi a basket. Pot ta maida kan gas ta zuba man gyada onion da kayan miya ta kawo spices da seasoning ta zuba ta jujjuya, oven taje ta dauko naman Kazan tazo ta juyeshi cikin pot din ta jujjuya ta kawo taliyan dake basket ta zuba ta jujjuya ta barshi for some minutes ya dan kara dawuwa kana ta sauke ta zuba a food flask. Kwakwa ta fere tayi grating dinta ta zuba cikin blender ta kawo ruwa kadan ta zuba ta zuba condense milk ta kawo hollandia yoghurt ta zuba ta zuba madaran gari tayi blending din su ta tace tasa a fridge. Wanka tayi ta tada sallahn magrib tana zaune tana azkar seda tayi isha'i ta nade pray mat din ta zare hijjab din jikinta ta tsaya gaban mirror tayi shafa ta kawo humra ta shafe jikinta dashi ta nufa wardrobe ta dauko kaya ta shirya cikin kana nan kaya 'yar karamar riga ce me hannun vest se wando iya guiwa ta feshe jikinta da turare ko hula batasaba ta nufo parlourn kasa. Yana tashi daga asibiti ya nufa gidan Abba ya gaishe su seda yayi alwalan magrib ya musu sallama a masallacin unguwar su ya tsaya yayi magrib be shigo gida ba seda yayi isha'i yana shigowa be tsaya parlourn ba ya nufi dakinshi, wanka yayi ya shirya cikin vest da wando three quarter ya feshe jikinshi da turarenshi na mufaddal Ta dukar da kanta tana operating phone dinta kamshin turarenshi ne ya sanar da ita karasowarshi, Kai ta dago ta kalleshi karaf suka hade ido tayi saurin dauke Kai tanajin yadda kirjinta ya buga da karfi daker ta bude bakinta da yamata nauyi tace "S..san. nu da dawowa" tafada cikin dan rawar murya "yauwa" yafada yana Jan kujera ya zauna. Taliyan ta zuba mishi ta dauki cup ta zuba mai juice din data hada sannan ita ma ta zuba nata ta shiga ci Taliyan ya faraci yayi 2 spoons a ranshi yace ya akayi yarinyan nan ta iya girki haka baki ya dan tabe ya daga kafada alamun ita tasani ya cigaba da cin abincin shi, juice din ya dauka yana kaiwa baki ya lumshe ido, yaci taliyan babu laifi amma yafi Shan juice din. Parlour ya koma ya barta nan, muryarshi taji yana kiranta "Keeeee" can kasa taja tsaki kana tace "Na'am" "idan kin gama ki hadomun coffee, kisa lemon kisa sugar kadan". Batace komai ba ta nufa kitchen ta hada mai coffee ta dauki lemun tsami ta yanka guda daya ta matse a ciki ta zuba 1 tea spoon na sugar ta kawo mishi, karba yayi yafara siping A kujera ta zauna ta cigaba da danna wayanta dan Allah yasani tsoron dakinta takeyi gidan shiru babu motsin mutane gashi dare beyi sosai ba gara ta zauna a parlourn tunda Fu'ad na zaune Koda baza suyi magana ba dai zataji motsin mutum. Ko kallon inda take beyi ba itama bata juya inda yake zaune ba Wayanta ne ya dau sauti me dadi First love sunan daya bayyana akan screen din wayan, cikin shagwaba ta dauki wayan "Hello mummy na" seta sa kuka "Muhibbah miye Kuma abin kuka" "To ba kin manta dani ba, dazu Kuma na kiraki bakiyi picking ba, Daddy Kuma nasan ko na kira a lokacin baya gida" "Rigimar ki tasa naki kiranki nabari sekin dan saba da garin, dazu Kuma wayan bata kusa dani shiyasa". "Ya Daddy, Shima ya Anas sau daya ya kirani" "Lafiya kalau muke Anas yayi missing dinki bakiga yadda yadawo so silent ba babu abokiyar rikici" "Allah sarki my ya Anas" "Fatan dai kin dena koke koken banza?" Dariya tayi Bata reda tace komai ba. "Ina yayanki? Ftn yana lafiya" Seda ta dan kalleshi kafin tace "Lafiya kalau" "Haka ake so, Allah yakara mai hakuri dan seya yi hakuri dake" kukan shagwaba tayi Kai Mummy nidai nake hakuri" dariya tayi sosai "Dama nafi so ki zama me hakuri da juriya a gidan mijinki, duk wani gidan aure cike yake da kalubalen rayuwa idan akayi hakuri se a zauna lafiya amma akasin haka gidan nan ze zama me karancin zaman lafiya farin ciki yanayin kaura ne a rayuwar ma'auratan da basu hakuri da juna, zaman gidan aure yana bukatan hakuri, juriya, uzuri, tausayi, kulawa, so, kauna, biyayya wa innan abubuwan guda 8 suna daga cikin matakan da duk ma'auratan da