← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 69

Sashe 34

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dauki wayanshi ya fice tabi bayanshi da kallo tana tabe baki. Office ya fara shiga ya danyi abinda zeyi kana ya fito cikin asibitin ya duba patient ya rubutama wa inda ya dace sallama ya fice. Masallacin juma'a ya nufa seda aka idar da sallah ya shiga motarshi yaja yabar arean. A (AUN) yayi parking direct office din malam Mukhtasir ya nufa knocking yayi aka bada izinin shiga, da sallama akan lips dinshi yashiga, Yana ganinshi ya mike da fara'arshi yana Mika mai hannu suka gaisa ya nuna mai guri ya zauna, dan murmushi yayi yana zama. "Dr Fu'ad kwana dayawa, kayi wuyar gani" "Lafiya kalau, kasan yanayin aiki se mutum ya yakice" "Hakane fa likita bokan turai, musamman ma aikin ku na ceton rai" Murmushi kawai yayi. Malam mukhtasir yacigaba da magana "Yauwa ga original Admission letter din nata" karba yayi yana dubawa, sauran files din ya Mika mishi yana mai bayani dan yariga yagama mata komai sedai ta jira lokacin da za'a fara lectures. Godiya sosai ya mai yamike yana bashi hannu sukayi sallama. Jiya bayan yashiga daki ya daga waya yakira malam mukhtasir ya nemi alfar mar yasama ma kanwanshi admission, nan ya turamai kudi yace yamata duk abinda yadace. Gidan Abba yabiya Ummi yasamu zaune cikin kujeru "Sannu da hutawa ummi" "Yauwa ya aiki?" "Alhamdulillah" "Ya jikin Muhibbah?, karta ke aiki sosai fa girkinma tabar ma mairo takeyi kawai" "Dasauki ummi tama war ware, Kuma kinsan ba son abincin masu aiki nake ba dan dai girki kawai ai babu wani gajiya" "Toh ciwo be Kori komai bane banda abinka, ai larura ne, Kuma naga kana cin girkin mairo" "Eh ummi gara girkin mairon ina daurewa inci amma bisa larura" Baki tasake tana kallonshi daga haka bata sake cewa komai ba, Dan dama ba fira take dashi ba zatayi dariya da kowa amma bandashi yanzuma yasan saboda Muhibbah ne tayi mai Wannan dogon maganan tun abin na damunshi har ya saba, Shima idan kaji ya sake yanata fira toh shida mummy ne dan jinta yake kamar ita ta tsugunna ta haifeshi. Suna zaune daga shi har ummin kamar kurame ya shige cikin kujera idonshi a rufe kamar me bacci, mekewa yayi yamata sallama tace ya jirata kitchen tashiga ta dauki food flask ta zuba danbun shinkafa ta dauki basket tasa food flask din ciki ta fito ta mika mai tace ya kaima Muhibbah, godiya yamata ya fice. Yau taji dadin zaman gidan sun sha fira da mairo se yamma driver yazo daukanta sukayi sallama tanaji kamar karta tafi. Burner ta dauko tana karama dakin turare taji ana danna door bell, dan dama kulle kofan take seta dai daici lokacin dawowanshi take budewa saboda kar yaita knocking batajiba tana daki. Ajiye burner tayi taje ta bude a cikin idanunshi idonta ya fada nan suka shiga kallon juna......... *Aminiyar ango *Aminiyar ango *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION* *Page 39* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 "S...san...nu da dawowa" tafada a dan rarrabe bakinta na rawa "Yauwa" abinda yace kenan yana shigowa parlourn. Dakinshi ya nufa ya cire kayanshi ya shige toilet, ya jima ciki kana ya fito ya tsaya gaban mirror yana tsane gashin kanshi, shafe jikinshi yayi da mayuka masu kamshi ya feshe ilahirin jikinshi da turarenshi na mufaddal, Jallabiya ya zira ya nufa masallaci Jin an fara kiraye kirayen sallahn magriba. Cikin shigan doguwar rigan leshi dinkin bubu ta fito se zuba kamshi take. Plate ta dauka ta zuba danbun da mummy ta aiko mata dashi ta zuba juice din banana data hada a cup ta nufa parlour ta janyo center table ta dora plate din danbun a kai ta zauna kan kujera tashiga ci. Se bayan isha'i ya shigo parlourn da sallama iya kan lips dinshi, dan kallon inda take yayi na seconds ya dauke kai ya nufa dining ya zauna. Mikewa tayi ta karasa dining din ta dauki plate ta zuba mishi abincin ta ajiye a gabanshi ta juya ta koma taci gaba da cin abincin ta, be ko dago ya kalleta ba seda tabar gurin ya ajiye wayan yashiga cin abincin shi hankali kwance. Sosai taci danbun dan ba karamin dadi yamata ba yaji zogale da hanta ga yaji a gefe. Be wani ci abincin ba saboda shinkafa ce Kuma baya son abinci me nauyi da dadare. Ganin ya haura sama ta mike tashiga tattare dining din, dawowa tayi kan 3 seater ta kwanta tana chatting a group din su na old student tana sakin murmushi "Muhibbah me kikeyi online yanzu? Ina kika baro habibin naki" Cewar Summy. "Kai matsalata dake yarinyan nan sa ido, ina ruwanki mijin ki ko Mijin Zahara?" "Eyyeeee yarinya an girma mijinki ne, keee ni muje private akwai labari". "Hello maman baby" sakon data ajiyemata kenan ta pc. "Aa kakan baby, nidae bani nasha" "Aesha kemun albishir kin kusa haifo mana baby" yadda zataji dadin masifan ta danna voice note "Abinda yafi baby nakusa haifo muku, duk me son babyn tayi aure mana ta haifo zaku dameni da wani zancen ciki, mutum ba daman yayi ciwo indai yanada aure se a dameshi da wani ciki zamu hadu da Aeshan ai hala ku kukamun cikin". Bata san ya shigo parlourn ba seda ya kai hannu gefen kujerar da take ya dauki remote, saurin tura voice din tayi tana mikewa zaune. Kan kujera ya zauna be ko kalleta ba Kuma sarai yaji maganganun da take gayama summy. Mikewa tayi a dan tsorace tace "Seda safe" Da hannu ya nunamata gefen da yake zaune, kallonshi tayi dan bata fahimce abinda yake nufi ba Hannu yasa ya dauka ya mika mata da sauri ta karba ko tsayawa tambayar namiye batayi ba, seda ta rufo kofar ta sannan tasauke nannauyar ajiyar zuciya dan duk a tinanin ta ta zauna gefenshi yake nufi, harta fara tinanin kwasawa da gudu murmushi tayi tana zama bakin gado. Admission letter tafara cin karo dashi bude ido tayi da kyau taga sunanta ne a jiki radau, mikewa tayi tayi tsalle ta fada kan gado tana furta "Alhamdulillah". Wayanta ta dauka ta danna numbern Aesha Ringing biyu ta daga "Hello maman baby" dogon tsaki taja "Matsalata dake kenan wasa" "Eyyyeee Aunty babba" "dama mun kwana biyu bamu raba hali ba, ni ba abinda na kira kenan muyi ba, karki bata mun rai ina cikin farin ciki" "Ah ni dama tunda naga kiranki cikin daren nan nasan akwai labari" "kedai bari ina cikin alkhaeri dumu dumu, Nima Yaya yasama mun Admission a (AUN) Kuma course dinmu daya dake "Masha Allah, ai ina jima nafiki farin ciki sister kice yanzu Koda yaushe Muna tare, dazu Abba kecemun on Monday zamu fara lectures" Wani juyi tayi akan gado "Karshen zaman kadaici ya kare kullum mutum na gida yanzu naga mutane su ganni" dariya Aesha tayi "Nidai bari na barki kije ki kulamun da yayana seda safe" tsaki tayi ta katse wayan. Kamar an tsunguleta ta mike ta bude wardrobe ledojin da zarah ta ajiye mata tun ranan da aka kawota ta fiddo zama tayi gefen bed tashiga bude ledan Turaren wuta ta ciro har kala 5 a wasu kwalabe masu girma ajiyewa tayi ta zaro humra Suma har kala biyar tana bude humran dakin ya dau kamshi murmushi tayi ta dan girgiza kai "Allah sarki umma" ko ba'a fada ba tasan wa innan ne sakon umman. Jiki a sanyaye ta janyo dayan ledan ta bude, hannu ta Kai ta ciro wani red box budeshi tayi ta zaro wata hadaddiyar sarka da dan kunne, rungume sarkan tayi a kirjinta wasu zafafan hawaye suka shiga kwararo mata hannu ta Kai ta dauke su, ta zaro wani katon frame an rubuta *ALLAHU* ajiki se Kuma wani frame Shima yana da dan girma irin Wanda zaka iya sa hoto ajiki ne se Kuma wani agogo kasanshi hoton dawisu ne guda biyu sun hada bakunan su. Tsamm ta mike ta dauko wata 'yar jaka da aka hadomata kananun abubuwan ta ciki, bude kayan tashiga yi sarkar daya bata ranan graduation dinta ta dauko ta hada data hannun ta ta Kai bakinta tayi kissing dinsu ta saki murmushi hade da hawaye hatta abin hannun daya bata duk suna nan maida kayan tayi cikin jakan ta rufe ta maidata mazaunin ta, Wayan daya bata ne a hannunta dan tun ranan da yabata ta cire sim dinta ta maida ciki ta cigaba da amfani da ita, kiss ta manna ma wayan kukan da take rikewa ya kufcemata seda tayi me isarta ta kunna suratul bakara ta ajiye wayan Saman bed side drower tayi azkar ta kwanta zuciyarta cike da tinanin ya mukhy dan a hankali rayuwar su na baya ke dawomata ta dade tana juyi kafin bacci ya kwasheta. Se karfe 10am ta ziro kafafunta kasa tana addu'ar tashi daga bacci, toilet ta nufa ta dan jima ta fito. Kitchen tashiga sharp sharp ta fara kokarin hada breakfast dan yunwa takeji. Potatoes ta fere ta yayyankashi ta barbada flour aciki sannan ta soya ta dauko stick ta tsitsira a jiki. Fridge ta bude ta dauko nama ta yayankashi kanana kanana ta tafasa, ta dauko pan ta zuba oil da kayan miya ta kawo seasoning ta zuba ta kawo naman ta zuba ta juya ta rufe after 5 minutes ta kashe gas din, dining din ta shirya kana ta nufi dakin. Wanka tayi ta shirya ta shafe jikinta da humran da umma ta Aiko mata dashi ta dauki ledan sauran humran da turaren wutan ta fito Tana fitowa Shima yana fitowa karaf idanunsu ya sarke dana juna gabanta ne ya fadi tayi saurin janye idanunta daga nashi a darare tace "In...Ina kwana" "lafiya kalau" ya fada yana taka staircase din, seda ta tabbatar ya isa dining kana itama ta sauko, ajiye ledan hannunta tayi ta karasa dining din tayi serving dinshi kana ta dawo parlourn. A show glass ta jera kwalaban turaren wutan ta dauko wani kwalba ta dura humra ta maida ta rufe ta dauki sauran humran ta maida daki, tana kokarin zama taji ana danna door bell, da fara'a ta nufa kofan dan tasan mairo ce, ai ko ta cinka dai dai tana budewa suka sakarma juna murmushi, hanya ta bata ta shigo suka shiga gaisawa, seda takarasa ta gaisheshi ya amsa
Chapter 34 · 0% Book details