Sashe 22
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Muhibbah tama maganan arziki zaka maido mata mara dadi, zuwan Ammar ne ka dena saboda kaga dan uwa". Sun jima suna fira kafin da dai dai su tarwatse zuwa gurin kwanciya. Tun safe suka tashi suka shirya fita kasuwa domin fara siyayyan da ya kawosu, sunayi break fast suka fita a wajen hotel din suka tari taxi zuwa Dubai outlet mall_ Al ain Dubai road. Kayan lefe suka fara hadawa abayas, veils, shoes, bags, jewelries dasauransu kaya suke jida kamar ba gobe muhibbah na biye dasu bata dauka Kuma bata cewa a dauka ko an tambayeta choice din colour cewa take duk colourn da aka dauka yamata se Aesha ce ke daukan mata kasancewar tasan favorite colour dinta, kaya suka hada kamar za'a bude shago har seda Mummy tace a barshi haka ummi tace a barta ta zabi duk abinda take so Wanda ba su daukar mata ba tace "Aa ummi wa innan ma sun isheni haka duk abinda zan bukata kun riga kun siyamun". zagayawa suka dingayi suna kara daukan wasu kayan seda suka tabbatar da sun hada mata kaya na uban gari kafin suka shiga diban kayan da kowa zesa ranan biki da shoes and bags, Suma su Ammar ba'a barsu a baya ba sun zaba nasu kayan, basu suka koma gida ba se magrib. A gajiye likis suka shiga gida tunda kowa ya nufa makwancinshi be fito ba ko dinner yau kowa a masaukin shi yayi basu hadu a dakin su ummi ba. Tun bayan tafiyan su Dubai Fu'ad ya tafi yola anyi Mai Kiran gaggawa a asibiti, se yanzu da yakira mummy bayan sun gaisa take tambayanshi gida shine yake fadamata shida Suhail sun tafi yola. "Toh Allah yabada sa'a" "Ameen Mummy". "Mummy ko kuna bukatan Karin kudi ne" "haba wane kudi Kuma, wa innan sun ishemu". "Duk sanda bukatar haka ta taso dan Allah ki sanar dani". "Wannan ma ya isa, Allah yama albarka" "Ameen". Daga haka sukayi sallama. Tana ajiye wayan tace "Kash abin haushi seda mukayi tafiya ya Fu'ad ze tafi yola inama Muna gida yatafi mu sarara musha iska abinmu" takai karshen magana n tana cije yatsa. Dakuwa Mummy ta mata "ungo nan idan yana nan bakya Shan iskan, toh Aiko kin kusa dena Shan iska gaba daya". Turo lips dinta tayi batare da tace komai ba saboda ta fahimta abinda mummy ke nufi. Ummi tace "Kibarta ai gaskiya take fada matukar yayansu na guri be bari susha iska". Nan Aesha tashiga basu labarin kamun kunnen Daya sa su gaf zasu tawo Dubai aiko su Anas me zasuyi idan ba dariya ba. Washe gari tun safe suka shiga taxi zuwa *Ibnu battuta mall_ sheik Zayed road* Nan ma siyayya sukayi ba kadan ba sun siya kitchen utensils duk wani abun bukatuwa a kitchen seda suka siya basubi ta kan Muhibbah ba tunda ko sun San ko sun tambayeta cewa zatayi batada choice siyayyar su suke hankali kwance ita Kuma tana biye dasu tana Jin kamar zuciyarta zata fashe a duk sanda ta kalla kayan ta tina ba gidan ya Mukhtar za'a kaisu ba siraran hawaye ne suka fara fareti a kuncinta tayi saurin gogesu tana hadiye kukan da takeji na kokarin kufce mata se nanata innalillahi wa inna ilaehi raji'un takeyi akan labbanta. Se yamma likis suka koma masauki, tura kayan sukayi zuwa Nigeria sukuma flight dinsu ya daga se turkey. A *hampton by Hilton cerkezkoy hotel* suka sauka Koda suka tashi dasafe basu bata lokaci ba suka fara Shirin zuwa siyayya, Mall of Istanbul suka shiga nan suka siya furnitures duk abinda ya shafi furniture seda suka dauka suka dan kara siyan wasu kayayyakin suka tura Nigeria. Washe gari flight dinsu ya daga zuwa Nigeria. Numfashi ta sauke ta shaki wani iska me dadi ta lumshe ido ta bude yayin da take saukowa daga matakalan jirgin, tana Janye da akwatinta can nesa da ita kadan ta hango su daddy da sassarfa ta karasa garesu tayi hugging din Abba "I'm back Abbana" "Welcome back Daughter" yafada yana rabata da jikinshi. Juyawa ga daddy tayi Shima tabashi side hug, kanta ya shafa tareda fadin "Miss you my daughter" "Miss you too daddy na" ta karasa maganan tana murmushi. Itama Aesha karasowa tayi tai joining dinsu. Cike da farin ciki suka shiga motocinsu suka dauki hanyan unguwan rimi low cost. Baaba asabe ta gyara gidan tsaf ta shirya musu dining seda suka dan huta sukayi wanka kana suka nufo dining, Muhibbah da Aesha Jin gidan suke ya musu dadi saboda Fu'ad baya nan zasuyi abinda suke so kafin ya dawo. Hidiman biki aka shigayi ba kama hannun yaro hankalin Muhibbah yakara tashi ganin kullum bikin kara matsowa yake kullum da zazzabi take kwana bata walwala se tayi kuka take samun nutsuwa koda yaushe tana daki. Kamar kullum yauma tana kwance tarasa meke mata dadi tayi zurfi a tinaninta bataji shigowa ba seji tayi an dan bubbuga bayanta firgigif tayi ta tashi, murmushi tayi har hakoranta na bayyana "Aunty Zahra kece" Kai ta Jin jina mata itama tana murmushi tace "Nice". "Ke kadai?" "Nida umma ne, tana parlour". Bata tsaya ba tayi parlour cikin sakin fuska ta karasa tanama umma sannu da zuwa, risinawa tayi ta gaisheta ta amsa cikin kulawa. Daki ta koma suna fira da Zahra da Aesha Sega Summy sunji dadin ganinta nan ta jonasu suka cigaba da fira suna kwasar dariya. Umma tace "Hajiya Hafsat dama wata alfarma nake nema a gurinki" . Maido da hankalinta sosai tayi gareta "Ina jinki hajiya Sa'adatu". Seda ta muskuta kana tace "Aron Muhibbah nake so ki bani, akwai wata me gyaran jiki da na dauko daga Maiduguri shine nake so ki bani aronta tazauna a gidan kanwata da take Nasarawa nan cikin gari". Nannauyar ajiyar zuciya tasauke "Banki ba sedai bansan ko Mahaifanta zasu yarda ba". Ummi dake zaune a gefe tace "Bari naje na gwada sa'a ta ko zasu yarda". "Toh Allah yasa a dace" cewar Mummy dan tasan zeyi wuya su yarda, Aiko anyi sa'a bata dade tana lallabar suba suka amince. Koda aka fadama Muhibbah ta hado kayanta ita da Aesha subi Umma dadi sukaji sosai harda tsalle dan sunajin lokacin da Ammar ke waya da Fu'ad yana ce mai yau ze dawo kd ko tsayawa tambayar abinda ze kaisu gidan basuyi ba. Ba karamin gyara take samu wajen matar ba dilka take mata sannan tasa wani ice me kamshi a wuta ta turare mata jiki dashi sannan ta zuba wani ruwan turare a ruwan wankanta tasa tayi wanka dashi, tajika mata magun guna a katon cup tasata a gaba tana kuka tana Sha har seta shanye su Aesha da zahrah suna gefe suna dariya Suma ana musu dilkan sedai ba kamar nata ba wani lokacin Sumy na zuwa ta wuni ayimata dilkan ta koma gida. Kullum se ta dauko ganyan tun fafiya Kwara 7 tashafa musu man Kade a jiki takarashi jikin rushi se ya dau zafi kafin ta Mika ma Muhibbah tace ta manna a kasan ta babu yadda ta iya dole takeyin yadda hajiya hawwaye tace saboda matar babu wasa a fuskanta tana aikinta tsakani da Allah tana kuka haka take manna ganyan nan har seya wuce kafin ta kara gasa dayan ganyen har se ta manna 7 din nan zata kyaleta. Cikin kwana 5 takara fresh tayi kyau sosae Aunty Zainab kanwar umma Bata bari tayi komai sallah kawai ke dagata itama tana bata kulawa bayan Wanda hajiya hawwaye ke bata kullum safe da yamma setayi blending din dabino da kanin fari ta zuba peak milk na ruwa ta bata tasha ko Kuma tayi blending din kankana da kanin fari da peak milk ta bata ko Kuma tayi blending din kankana da peak tabata wani lokacin Kuma ganyen zogale danye takeyin blending ta tace ta zubar da tukan ta juye ruwan zogalen a cup tazuba peak milk na ruwa ko na gari ta bata ta kwankwade su Aesha suyita rokon Aunty ta basu taki se Muhibbah tasha Aunty kecewa ta rage musu kadan ita ko Muhibbah kan dole take Sha tanayi kamar zatayi amai...... *Wae waye (Adon tafiya) Munata tafiya batareda mun wae waye baya ba batare da munji dalilin dayasa Abba ke rayuwa acikin garin yola Amma daddy ke rayuwa acikin garin kd alhali Uwa Daya uba Daya suke, sannan wane dalili yasa suka kafe kaida fata se sun hada yaransu aure bayan sun San basa son junansu hasalima babu wata jituwa a tsakaninsu* *Wanene Alhaji Muhammad BICHI*. [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 29* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Alhaji Muhammad Shu'aib BICHI dan asalin garin Kano ne mazaunin wani karamin kauye me suna *SHERIFAWA* dake karamar hukumar *BICHI* Babban manomi ne yanada tarin dukiya shine na Daya acikin masu kudin kauyen yanada katon gida Wanda ya Kai fegi biyar inda yake kiwon shanaye da tumakai se wani bangare da aka kebe inda dakunan su yake, Matarshi Daya kwal FATIMA ansha kawo mishi mata kala daban daban da sunan an bashi kyauta idan yana so ya aura amma yaki yace zama da mace daya yafi mai kwanciyar hankali musamman da Allah yabashi mace ta gari take bin umarninshi Kuma take kokarin kula mai da