← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 69

Sashe 16

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Aminiyar ango **Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 23* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Emergency room aka nufa da ita su Abba na biye da doctors din, ummi da mummy suna kokarin shiga room din doctors suka dakatar dasu. Hankalin kowa a tashe yake ga Aisha da kukanta ke kara daga musu hankali. Fu'ad hankalinshi ba karamin tashi yayi ba ya goya hannunshi a baya se safa da marwa yake yakasa zaune yakasa tsaye ga kukan Aisha na kara yamutsa mishi kwakwalwa danshi sam baya son yawan hayaniya, ganin batada niyyan yin shiru yasashi daka mata tsawa ae dasauri ta hadiye kukan tasa hannu ta toshe bakinta tana shasshekar kuka kasa kasa. Kasa hakuri yayi yaje yayi knocking emergency room din dan gani yake kamar doctors din basa kokari, Daya dg cikin doctors din ne ya bude kofar yana tambayar lafiya? Fu'ad yace "Sorry doctor karka ga kamar inaso nayi muku shisshigi akan aikin ku amma please kabari na taimaka nima ko zamu samu numfashinta ya dawo". yakarasa maganan yana hade hannuwanshi biyu alaman roko. Girgiza Kai doctor din yayi kana yace "yin hakan yasaba ma dokan asibitin nan". Abba yace "he is a doctor please allow him to help our daughter, bawai mun raina aikinku bane, Allow him to share his experience with you please". "We can't, idan Kunsan danku doctor ne meyasa baku barta a gida ya dubata ba, please allow us to do our work, idan Kuma ba haka ba zaku iya daukar 'yarku zuwa wani hospital din" ya karasa maganan yana nuna musu hanyan waje. Ran Fu'ad ne yakara baci ya dunkule hannu ya naushi iska yana cije lip dinshi na kasa. Nan daddy yashiga rokonsu daker suka amince Fu'ad ya taemaka musu, kowa ka kalla ido yayi jajir se matsar kwalla suke hatta Ammaar da Anas hawaye suke jikin kowa yayi sanyi suna jiran tsammani. Yana shiga ciki yace su dan matsa ya shiga aikinshi cikin kwarewa, cikin iKon Allah befi 20 minutes kanta ba tafara tari tana motsa hannunta numfashinta yaki dae daeta se sama da kasa yakeyi dole seda ya kae ga samata oxygen ya fito dg room din yana goge zufa, Suma doctors din suka biyo bayanshi nan suka shiga Mika mai hannu suna Jinjina ma kwarewar shi, godiya su daddy suka ma doctors din. Ummi tace "ya jikin muhibbahn?". "Dasauki ummi, numfashinta ne be gama dai dai tuwa ba amma in Sha Allah komai ze dawo normal". Sun so su shiga su ganta amma inaa an hanasu dole suka hakura suka tafi gida saboda dare yayi sosai se Fu'ad kawai aka bari a asibitin. Daddy na kwance kan bed yana kallon sama da alama yayi zurfi a tinani, gefen bed din ta dan buga yayi firgigif yatashi zaune yana kallonta batare da ya komai ba. Zama tayi gefenshi tace "Alhaji dama ina so muyi wata magana ne idan babu damuwa". "Ina jinki". "Alhaji kutaimaka ku duba lamarin nan ku janye maganan auren nan kar ya haifar mana da ba ido, kaga daga maganar auren nan yarinyar nan tashiga wani hali ina tsoron abinda ze je yadawo". Tunda tafara magana yake kallonta beyi yunkurin hanataba har ta Kai Aya, yace "kin gama bayanin ki ko akwai saura?" "Ta girgiza Kai". Yace ki tsaya kiji zanmiki magana na karshe akan auren nan wllhi indai ina numfashi muhibbah nada Rai Fu'ad na raye toh aure kamar anyishi angama, ko kiso koki kii aure ba fashi Kuma kar kisake ki kara yimun magana akan auren nan indai ba fatan alkhaeri zakiyi musu ba". Ya karashe maganan ranshi a bace... "Kayi hakuri, Allah ya tabbatar mana da alkhaeri". "Ameeen" ya fada yana komawa ya kwanta. Da safe tun karfe 9 a halin suka tarkato suka nufo asibitin saboda dama ba wani bacci sukayi ba, a reception suka yada zango saboda har lokacin ba'a barsu sun ganta ba ance su bari se an maidata special room, se Fu'ad ne ya shiga ciki ya kirasu video call suna ganinta kwance ga oxygen an makalamata gashi tana nan kwance babu wani motsi ai tuni suka hau koke koke yayi sauri ya kashe Kiran, yashiga aikinshi, oxygen din ya cire mata akayi sa'a ko numfashin ya dai dai ta sedai har lokacin idonta a rufe yake. Be jira an kawo chair din daukar marasa lafiya ba ya sunkuceta yawo waje doctors din suka nuna mai special room din, kan bed ya kwantar da ita yasa mata drip yayi allurori a cikin drip din Bayan ya fita yace su Abba zasu iya shiga amman banda hayaniya, shi zeje gida yayi wanka yadawo Suhail yabishi suka tafi tare. Tana nan kwance har lokacin suka shiga matsar kwalla, Aisha ko idanuwa sun kumbura tsabar kuka se faman karfa fa mata guiwa akeyi amma taki yin shiru. Mummy ta kira su Aunty Asma'u ta sanar musu muhibbah ba lafiya tana asibiti "mummy kuna wane asibitin?". "Manaal specialist hospital". "I will be there in Sha Allah". Kafin kace me asibiti ya cika da 'yan uwa kowa na jimami, har dare kafin aka watse se su ummi Suma suna nan zaune suna jiran tsammani har dare amma muhibbah bata farka ba hakanan suka tarkata suka yi gida jiki a sanyaye. Wajen 10pm tafara motsa hannunta tana kokarin bude ido har ta bude su a kan Fu'ad, tayi saurin runtse idonta muryarta na rawa tace "Yaya". Cikin sauri ya ajiye wayanshi dayake ta operating tun dazu yace "kin tashi". Ta gyada Mai Kai ta makamata yayi ta tashi zaune. tace "ina mummy na?". "Taje ta dawo, kina bukatar wani abu ne?". Ta daga Mai Kai tare da cewa "ina so zan shiga toilet" nurse ya kira ta taimaka mata ta kaita toilet tasamu tayi brush tareda dauro alwala tazo ta gabatar da sallolin daba tayi ba, bayan ta idar ta jima tana addu'o'i tana rokon mafita wajen ubangiji harda hawayenta, Yana zaune yana kallonta duk da besan me take fada acikin addu'ar ba. Gadon ta koma ta zauna ta jingina da bango wasu zafafan hawaye na gangarowa daga idanunta tana daukesu wasu na kara gangara, bece mata uffan ba saboda yasan dalilin hawayen baki ya tabe ya hadama tea ya mika mata takarba Rabin cup tasha ta ajiye sauran akan bed side drower, tana mamakin Fu'ad a ranta tana raya anya shine ko Kuma mafarki take. Cikin muryar tausayi tace "ya Fu'ad ka tausayamun ka taimakeni ka rokamun su daddy su janye maganar auren mu". Ta karasa maganar tana hade hannunta biyu alaman roko hawaye na zubowa a kuncinta. Wani kallo ya watsamata, dasauri tayi kasa da kanta tana shasshekar kuka. "Ce miki akayi ni irinki ne mara kunya". "Amma alkawari bece haka ba, soyayyar kwana daya muka tsara da Kai amma ka jefani a musiba ake kokarin rabani da masoyina, farin cikina, rabani da ya mukhtar tamkar katsemun numfashi ne". Be kulataba ya fice ya turo nurse tayi mata allura, amma fafir taki tsayawa seda yazo yazare mata ido kana ta tsaya, ta koma ta kwanta bacci ya dauketa. Tun 7:am take rokon ya kaita gida yayi mata banza se 9 da doctor yazo yasameshi office yayi Mai godiya sosai sukayi sharing number ya karbamata sallama daga gurin doctor ya dauketa suka nufa gida. Yanayin parking tayi saurin balle murfin motan ta fita tayi ciki suna kokarin fitowa ta shigo kallonta suka shigayi da mamaki tayi karfin hali tace "Mummy nice! Muhibbah ce, autar mummynta ba wai wata bace tayi shigana". Duk dariya sukasa na mikama Allah godiya. Aisha ta rungumeta tasa kuka itama ta mayar mata da runguman kukan da take rikewa ya kwace mata. kuka takeyi sosae har seda abin yaba Aisha tsoro tace "Dan Allah sister kiyi shiru hakanan kinga yanzu kika dawo daga hospital kar kanki yayi miki ciwo". Kukan ta ciga dayi ummi ta karaso ta riketa itama tana sharar kwalla tace "kukan ya isa haka muhibbah, babu inda kuka yataba maganin matsala, kiyi hakuri kinji"?. Kai ta gyada tana shasshekar kuka, Fu'ad da yashigo yanzu ya tabe baki ya nema guri ya zauna yana latsa wayarshi. Suhaila ta kamata tanufa bedroom dinta da ita har lokacin kuka take, Aisha tabi bayan su, mummy se matsar kwalla take daga zaune abin duniya yamata yawa tarasa yadda zata bulloma al'amarin, su Maza babu ruwan su duk wata damuwa akan iyaye mata ke karewa, mikewa tayi ta nufa bedroom ummi tabita da kallon tausayin junansu ita kanta tana cikin damuwan......... *A lallaba please *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 24* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki
Chapter 16 · 0% Book details