Sashe 53
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tare suka ci abincin cikin so da kaunar juna har juice din tare suka shanye yanata santi kan suka koma parlour kan kujera ta zauna ta zabga tagumi Hannu yasa ya tallabo habarta "pretty ya akayi ne? Waya tabamun ke?" Ya fada yana zama gefenta Hawayen dake makale a idanunta ne suka silalo, yasa hannu yana share mata "Ya salam bloody meyafaru? Ko cikin ki ke ciwo?" Ta girgiza kai "Kanki ne?" Takara girgiza kai "Toh menene" ya fada yana dan bubbuga bayanta alaman rarrashi "Gida nake son zuwa ina son ganin Mummy" Lakace hancinta yayi "Heebbah kullum yarinya kike komawa, toh miye abin kuka, ki bari Saturday semu tafi tare uhmmm" Shi kanshi yasan tayi mugun kokari tunda aka kawota shekara daya kenan cirr bataje gida ba Murmushi tayi ta kwanto jikinshi "Thank you dear" peck yamata a goshi "It's my pleasure" A hankali taji maganin data hada yafara aiki tafara jin chanjin feeling, Shima hakan ne ta bangaren shi tun yana biye mata suna fira har yakasa hakuri ya dagata cilak suka haura dakinshi, kan bed ya kwantar da ita shima ya haura gadon suka shiga romancing juna seda suka ruda juna duk suka fita hayyacinsu kan suka shiga wata duniya sun jima sosai kan ya mirgina ya kwanta gefenta tareda janyota jikinshi ya matseta sunata faman sauke numfashi, tare suka yi wanka suka shige blanket suna manne da juna har bacci ya kwashe su. Wajen 7 ta shiga kitchen ta sama mai breakfast bayan ya fice ta koma dakinta ta kwanta bata jima da kwanciya ba bacci ya kwasheta dan dama jiya da dare ba wani baccin kirki sukayi ba. Wajen 12 ta tashi ta shiga kitchen kayan dazata bukata na yin alkubus ta fiddo su kusa da ita Bowl ta dauko ta zuba flour 4 cups, 2 spoons of sugar 1 tea spoon of salt, 1 tea spoon na baking powder ta zuba sannan ta kawo yeast 2 table spoon ta zuba ta zuba 4 table spoon of oil sannan ta kawo 2 cups of water ta zuba ta kwaba bata kwabashi da kauri sosai ba sannan beyi ruwa ba. Gwan gwanaye ta dauko ta shafa musu oil ta zuzzuba kwababen flourn ta daura tukunya ta zuba ruwa ta kawo basket na karfe ta daura kan tukunyan ta jera gwangwanayen ciki ta rufe ta barshi 15_20 minutes kan ta sauke ta dauko wata hadaddiyar kula ta zazzage a ciki. Pot ta daura kan gas ta zuba manja da kayan Miya seda suka soyo ta kawo gandanta dama already ta dafa shi ta zuba ta kara soyashi kadan ta kawo seasoning da spices ta sa kana ta zuba ruwa ta rufe seda gandan ya kara dahuwa ta dauko busashen Kifi ta zuba ta rufe seda ruwan ya ja baya sosai ta kawo alayahu tasa ta barshi for 10 minutes kan takashe gas din ta dauko kula ta juye miyan ta dauko hadadden basket ta jera kulolin ta nufi dakin Wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigan leshi anyi mata dinkin bubu ta kafa dauri ta kawo gyalenta ta yafa tasa face mask ta rataya jakanta ta nufa kitchen ta dauki basket din ta fice. A bakin gate din Meddy hospital driver yayi parking ta sauka ta karasa cikin asibitin tanata wuce nurses suna zirga zirga ba wani sanin asibitin sosai tayi ba dan tunda sukayi aure sau daya tazo. Kai tsaye office dinshi ta nufa tana kokarin daura hannunta akan handle din kofan wani security ya karaso "Hajiya lafiya?" Dan kallanshi tayi "Bangane lafiya ba da akayi me?" "Ya zaki zo babu neman excuse kai tsaye kice zaki shiga office din boss" Kallon ban fahimta ba ta bishi dashi kamar zatayi magana kawai tafasa ta daura hannunta kan kofar "ya ana miki magana amma still kina kokarin shiga ko bakyaji ne?" Wata nurse ce ta kara so ta rike hannun nata "Sorry madam! Ki bari asanar dashi yanada bakuwa idan yace a barki ki shiga seki shiga" Ranta ne ya zo wuya cikin fada tace "Saboda nazo gurin mijina shi ne sena jira anyi mun iso?" Da mamaki suke kallonta Jin tace mijinta su a iya sanin su basu taba Jin labarin auren boss ba kodai hankali take son raina musu dayan nurse din ta bude baki zatayi magana se gashi ya fito daga office din dan dama yana kallon abinda ke faruwa ta CC TV tana ganin fitowarshi ta fada jikinshi tasaki kuka me sauti yasa hannu ya rungumota kallon da ya watsa musu yasa kowa ya kama gabanshi suka tafi suna kus kus din dama yanada aure ganin basuda cikakken bayani akan zancen kowa ya cigaba da aikinshi. A doguwar kujeran dake office din ya zauna tareda yimata masauki akan cinyarshi ya kai hannu ya cire mata face mask din fuskarta ya hada goshin su hancinsu na gogan na juna "Sorry madam laifina ne da ban bari sun san matsayinki ba, I'm so sorry" Ajiyar zuciya tasauke ta gyara kwanciyarta kan jikinshi yasa hannu ya zame dan kwalin kanta hade da gyalen yana shafa kanta ganin yana neman zarcewa tayi saurin mikewa ta tsugunna ta dauki dan kwalinta ta daura ta janyo karamin table ta fiddo kulolin ta daura a kai. Plate ta dauka tayi serving dinsu ta haye cinyarshi ta shiga bashi alkubus din tana bashi tana ci har suka koshi kan ta sauka ta bude fridge din dake office din ta dauko ruwa ta zo ta zuba ta mika mai ya karba ya sha kan yabata itama tasha. Kanta ta daura kan kafadar shi "Hearty" "bloody ya akayi ne?" "Kwanan nan ina kewan Mummy na" "Eyyyaaa sorry jibi zakije ki ganta in Sha Allah laifin hearty kine be so kiyi nisa dashi shiyasa kika dau tsawon lokaci bakije kinga mummy ba" "Kasan menene?" "Aa sekin fada" "I LUV YOU" "LUVS YOU TOO Hayateee" ya fada yana tallabo kanta tana kokarin yin magana ya hade bakinsu yashiga bata hurt kisses seda yayi me isanshi kan ya barta ta binne kanta a kirjinshi yasa hannuwanshi ya zagaye kugunta suna maida numfashi. Tsamm ya mike "let's go" kulolin ta mayar cikin basket din ta gayara daurinta ta yafa gyalen bata sa face mask ba suka fito hannunsu cikin na juna har leke ake a ga matar boss duk inda suka wuce se faman miko gaisuwa ake. Mota suka shiga yaja suka bar asibitin seda suka biya mall sukayi masu mummy tsaraba kan suka fito daga mall din hannun su gimtse dana juna yana tsokanarta tana murmushi daga kan da zatayi idanunta suka fada cikin na Mukhtar gabanta ne ya yanke ya fadi ta juya ta Kalli Fu'ad ta kara waigowa ta Kalli mukhtar taga har lokacin ita yake kallo ja tayi ta tsaya, ya juyo yana tambayarta lafiya amma ta kasa magana tana tsoron ta karasa wajen Mukhtar su gaisa tayi laifi Kuma tanajin idan ta fiske ta tafi bata kyauta ba tunda har sun hada idanu Ganin ta kafe guri daya da ido yasa shima ya juya ya Kalli gurin Mukhtar ya gani tsaye yana murmushi kallon kallo suka shigayi ita kam duk ta rude har idanunta sun cika da kwalla dan tasan yau seta gamu da fushin Fu'ad da mamakinta se gani tayi Mukhtar ya nufo suuuuuu.... Hannu ya Mika ma fu'ad "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" "Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh" gani tayi Fu'ad ya sake sun gaisa da mukhtar, a sanyaye tace "Ya Mukhtar ina wuni" "Lafiya kalau Muhibbah kwana dayawa" "Lafiya yasu umma da Aunty zahrah?" "Suna lafiya kalau" "Dan Allah ka gaisharmun dasu" "Zasuji idan mukayi waya dake anyi mun transfer a gurin aiki na dawo nan" "Eyyyaaa Allah yataimaka" Ita dai duk a tsorace take gudun ta cika magana tayi laifi Hannu ya kara mika ma Fu'ad kan sukayi sallama ya wuce suma suka nufi mota har suka isa gida babu wanda yayi magana yana tuki amma hankalinshi na kanta ganin yadda tayi shiru Yana yin parking ta bude murfin motan ta fita. booth ya bude ya kwashi ledojin ya nufa ciki ta mara mai baya har dare be kulata ba duk se ta damu daurewa tayi tashiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kana nun kaya wando ne iya cinya se karamar riga me hannun vest ta feshe jikinta da turare ta dauki wayanta ta nufi dakinshi murda handle din kofar tayi tashiga bakinta dauke da sallama ta samu har ya kwanta ta karasa ta kwanta a bayanshi yanajinta amma be koyi motsi ba Hannu ta Kai ta rungumeshi ta fashe da kuka "hearty I'm so sorry kayafemun please" Juyowa yayi suna facing juna yasa hannu Shima ya matseta a jikinshi "wayace kinyimun laifi ni bakiyimun laifin komai ba naga tunda kika hadu da Mukhtar mood dinki ya canza shine na barki har ki dawo normal" "Yaya ba saboda ya mukhy bane naga kamar na batama rai ne shiyasa jikina yayi sanyi amma ina tare da farin ciki na me zesa nayi tinanin wani namiji, ai duk wani namiji bayan ka toh mace nake kallonshi......" Murmushi me sauti yayi yakara matseta a kirjinshi ya hade lips dinsu daga nan suka shiga wata duniya Washe gari bayan sunyi break fast tare suka fita ya sauketa gidan ummi shi Kuma ya wuce asibiti "Yayanki yace gobe zaku tafi KD ko?" "Eh Ummi shine ma nazo yi miki sallama" Kafin Ummi tayi magana Aesha tace "Dan Allah da Yaya wani ne da base mu tafi tare ba tunda anyi hutun school" "Allah ya hadaki da yayan naku zakiyi bayani" saurin toshe baki tayi tana dariya "Ni kaina ina son zuwa KD nan tun bikinki rabona da zuwa" "Ummi ki shirya mutafi gaba daya mana" "Aa kuyi tafiyarku zanje daga baya in Sha" "Toh shikenan ummi" "Yauwa Aesha dan bani wayanki mana" Mikamata wayan tayi ta mike ta nufi dakin Aeshan, wata number tasa tashiga dialing seda ta kusa katsewa kafin akayi picking ta jima tana waya kan sukayi sallama ta goge numbern ta nufo parlourn tana murmushi Se yamma ya shigo gidan seda suka jira Abba yadawo sukayi mai sallama kan suka tafi Ummi ta bata kaya niki niki tace ta kaima mummy ta karba tayi godiya suka fice. Kayansu ta shirya musu a akwati kallonta kawai yakeyi yadda take faman loda kaya