← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 69

Sashe 38

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sun jima suna kallon juna ta girgiza mai kai, dauke kanshi daga kallonta ya hadiye wani abu me daci hannunshi na rawa ya fara rubutu............... *Innalillahi wa inna ilaehi raji'un haba Abba ka yanke danyan hukunci* * Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION* *Page 42* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 Gimtse bairon yayi a hannunshi yayi kasa da kanshi ya rasa ta ina ze fara. "Me kake jira?, maza rubuto ka bani" yayi maganan cikin daga murya. Gaban Abba ta karasa ta riko hannunshi ta fashe da kuka "Abba dan Allah kayi hakuri wllhi babu laifin Yaya duk abinda ya faru laifi na ne ni na janyo har ya kai hannunshi jikina kanada iKon ka yanke duk wani hukunci a kain...." Tsawan daya dakamata yasata ja da baya da sauri "kinyi mun shiru ko sena saba miki". Gefe ta koma ta raku be tana kuka me taba zuciyar me karatu. Paper ya yaga ya dora kan littafin yana kokarin rubuta sakin kamar yadda mahaifinshi ya umurceshi, a zafafe Ummi ta karasa daf dashi ta fisge bairon ta juyo wajen Abba tareda karasawa ganganshi tana hawaye "Dan Allah Alhaji kayi hakuri mu bi komai a hankali kar ka yanke hukunci cikin fushi" be ko kalleta ba ya juya da niyar barin gurin se kuma ya tsaya batareda ya juyo ba "Kar ka kuskura inkara ganin kafarka cikin gidana matukar ba takardan ta zaka kawomun ba, ita kuma 'yar gold din da kake so kafadamata iyayenta su tsaida lokaci daddynku zasu zo su nema ma aurenta, kaje Allah ya hada kowa da rabonshi na alkhaeri" yana kai nan ya wuce yabarsu tsaye cirko cirko. Tana ganin Abba ya haura sama ta karaso gabanshi ta zube kan guiwowinta ta riko kafafunshi "Yaya dan Allah kayi hakuri banyi tinanin zuwana gidan nan ze haifar ma Abba mummunan fushi ba, kayi mai biyayya ka aikata abinda ya umurceka, ka aure wacce take son ka kake sonta muyi fatan hakan yazama shine mafi alkhaeri a rayuwarm..." Kuka ne ya sarketa ta kasa karashe maganan. "Aesha kamata ku je daki" karasawa tayi ta rikota suka nufa daki. "Kaima kayi ka tafi gida dare yayi". Sallama yamata ya fice, Shima ammar ya huta dakinshi ummi Kuma ta nufi dakin Abba. A gefen bed ta dan zauna "Alhaji kayi hakuri wannan abu ya faru ne bisa kuskure kar ka yanke hukunci cikin fushi kar a gyara barna da barna mubi komai a hankali saki bashi bane solution yanzu idan an rabasu a haka zatayi rainon cikin har ta haifeshi a gaban mu kana da iKon ka dauki duk matakin daka ga ya dace amma dan Allah banda saki" ta kai karshen maganan tana hada hannayenta biyu alamar roko. "Toh se me? Akanta aka fara haihuwa a gidan iyaye? Tsabar rashin tausayi yasan tana dauke da juna biyu yamata wannan marukan, toh nagama maganata ya rubutonmun takardan diyata shine kwanciyar hankalinshi ai bashi kadai bane namiji a duniya ba, idan har maganan data kawoki kenan ki bani guri". "Allah ya huci zuciyarka" abinda ta fada kenan ta baro dakin tareda rufo mai kofa. Se kai kawo take a daki takasa tsaye takasa zaune tana tsoron kasancewar wannan hukunci da Abba ya yanke dama abinda take tsoro kenan tun farko shiyasa taki auren amma Alhaji ya nuna babu fashi yanzu Kuma seda rabo ya ratsa ace za'a raba auren bazata taba fatan haka ba. Tunda Ummi ta fita daga room din ya shiga tinani a zuciyarshi yake maimaita kalman ummi cewa Muhibbah na dauke da juna biyu Yana isa gida a daddafe ya haura dakinshi a gefen bed ya zauna ya dafe goshinshi yanajin kanshi kamar ze fado tsabar yadda yayi mai nauyi, kwanciya yayi yana Kallon ceiling yana ta faman sake sake wata zuciya na ce mai ya rubuta sakin kawai dama wani lokacin se an bata ake gyarawa. Wata zuciya Kuma na garga darshi akan kar ya sake dan idan yayi sakin ma be tsira ba indai gurin Abba ne Karin wani laifin ne dan yanzu yana cikin bacin rai ne yasan zuwa safe ze sauko. A bakin gado Aesha ta zaunar da ita itama ta zauna gefenta. Hannun Aesha ta riko tana sake fashewa da kuka "Sister laifina ne wllhi laifina ne muna zaune lafiya nice na janyo duk abubuwan nan da suka faru". Lallashinta Aesha keyi bata tsananta tambayarta me ya hadasu ba tunda da ace tana so aji da tun da Abba ke fada zata fada mai sannan Shima ya Fu'ad din da yana son fitar da sirrin su daya sanarma Abba abinda ya hadasu. Rarrashinta taitayi har tasamu tayi shiru tana ta faman ajiyar zuciya. Jiki a sanyaye ya tashi yayi wanka yayi Shirin fita aiki, parlourn kasa ya sauko ya dan Kalli dining yaga tun kulolin jiya ne a gurin ya fice yaje ya shiga mota ya yaja yabar gidan. A restaurant ya tsaya yayi breakfast kana ya karasa asibiti. Suna zaune a dining suna breakfast banda Muhibbah da Aesha taita rokonta suje suyi breakfast taki tun asuba da tayi wanka tayi sallah ta haye gado ta nade cikin blanket. "Ina Muhibbah ne?" Cewar Abba "Tana daki nayi nayi taki fitowa" "je ki kiramun ita" bata fi minti biyu da tafiya ba se gasu sun fito su biyu. "Abba Ina kwana" "lafiya kalau". "Ummi Ina kwana" "lafiya kalau ya jiki jikin" "Dasauki alhamdulillah" ita dai ta amsa ne amma tasan lafiyan ta kalau, kukan da tayi ne ma yake son haifar mata da zazzabi. Tana Shirin gaishar da Ammar yayi saurin cewa "Barka da safiya" murmushi tayi "Lafiya Alhamdulillah". Jan kujera tayi ta zauna, Aesha tayi serving dinta Chokali tasa ta diba abincin amma takasa kaiwa bakinta kawai hakanan taji tana tinanin ya Fu'ad batasan a wane hali ya kwana ba waze hada mai breakfast? Ina zeje yayi breakfast din?. Ita dai tasan ba son Fu'ad take ba amma tun jiya tausayinshi ya shigeta. Muryan Abba ta tsinkaya "Ci abincin mana maamana, ko be miki bane laraba ta dafa miki wani?" Kai ta girgiza "Aa Abba wannanma yayi" tana kai nan ta shiga cusa abincin tana hadiyewa daker. Koda tagama bata zauna parlourn ba ta koma daki ta kwanta saboda basuda lectures se Kuma Monday. Karfe 4 ya tashi daga aiki ya nufo gidan Ummi yasan Abba be riga ya dawo ba. A parlour ya sameta kwance kan cinyar ummi tana sanye da wani material maroon colour anyi mata dinkin riga da wando ko hula babu akanta gashin kanta a tsafe ya kwanta gaban goshinta. A kujeran dake facing dinsu ya zauna ya shiga gaishar da Ummi. Dasauri ta mike zaune batare da ta kalleshi ba tace "Ina wuni" can kasan makoshi yaja tsaki ya dauke kai. Mikewa tayi ta nufi stairs ya bi bayanta da kallo harta bacema ganinshi. Se gaf magrib ya mike "Ummi bari na wuce" "Toh se Allah ya kaimu". Yana Shirin shiga mota motar Abba ta kunno kai gidan, dafe goshinshi yayi a kan lips dinshi ya furta "Oh my God". Kafin yayi yunkurin shiga mota har Abba da Ammar sun fito daga motan sun nufo hanyan parlourn. Risinawa yayi ya gaida Abba be amsa ba se umarnin biyoshi kawai ya bashi. A parlourn shi ya zauna kan carpet yana jiran fitowarshi, seda ya dan jima kan yafito ya zauna kan kujera. Gaisheshi ya Kuma yi, ya amsa a dan sake. "Fu'ad" "Na'am Abba" "Wllhi! Wllhi!! Wllhi!!!" Kaji nace wllhi har sau uku ko?" Dasauri ya Jin jina kai. "Idan ka sake ka kara mai maita kuskuren da kayi jiya to tabbas kaida Muhibbah har abada indai matsayin mata da miji ne, Kuma senayi munmmunan sabamaka, bazan ja zancen da nisa ba amma idan kana ganin wasa ne mu zuba nida kai banda shirme mace harda ciki ka dauki hannu kaita kwadamata babu tausayi" saurin dagowa yayi ya Kalla Abba a ranshi yace ciki Kuma?. Fada yayi mai kana Kuma ya koma nasiha "dukan mace bashida amfani idan kasaba bazaka iya denawa ba abu kadan zaka Kai hannu jikinta itama idan tasaba da dukan idan baka duketa ba baza taji dadi ba ta dinga nemanka da fada kenan har se ka taba lafiyar jikinta, Wawan namiji shike dukan mace, tashi kaje duk lokacin da mamana taji tana son dawowa zata dawo amma bazan matsamata ba. Godiya Yamai tareda sallama ya fice da sauri Jin an kira sallahn magrib. Wasa wasa har kwana 5 Muhibbah na gidan Abba sedai suje school su dawo tanajin dadin yadda Ummi ke kula da ita bata wani aiki sedai kawai a dafa taci hatta serving dinta Aesha keyi. Abba be mata maganan komawa gida ba yadai cema Ummi duk lokacin data ke son komawa maimunatu ta rakata idan Kuma tace bazata koma yanzu ba karta matsamata. Koda ummi ta fadamata sakon Abba taji dadi tunda ya sauko sedai tace bazata koma yanzu ba tun daga nan bata kara yimata maganan komawa gidanta ba. Ranan kwana na biyar din ne bayan tadawo daga school tayi lunching ta haye gado ta kwanta taji an janyota kiiiii tana neman faduwa kasa a zabure ta mike tsaye ta kai kallonta ga Aunty Maiminatu, ita kanta Aesha dake gefe seda ta tsorata dan bataji shigowarta ba se ji tayi ana Jan kafan mutum. "Eh kalleni da kyau, ke wace iri ce? Wane irin kunne gareki da bakyajin magana?" Shiru tayi dan batasan akan me take magana ba "Kina zaune har tsawon kwana biyar a gidan nan yin mene? Wa kika bar wa mijin naki? Shikenan kince mijinki ya karo wata kenan Sha Sha Sha se nan gaba abin yazo ya dameki bancin kin riga kin baro shiri tun rani, kin san adadin 'yan matan dake farautar mijinki a kullum? Kinsan adadin 'yan matan dake burin auren mijinki? Wasu burinsu Koda magana ya musu suji dadi, ke kin samu daman mallakar miji kamar ya Fu'ad kalar mijin da dubbanin mata ke fatan samu dare da rana amma kin tsaya shirme. Tunda yasamu kofar da har Abba ya furta su daddy zasu je su nema mai aure ai shikenan kuma se wani iko daga Allah kiga ba'a dauko miki kishiya ba". Hawayen dake kwance a idanunta ne suka samu nasarar gangarowa batasan lokacin
Chapter 38 · 0% Book details