Sashe 7
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tun safe ya kufecemata, Aa maamana wani Abu yafaru ne? yayi maganan cikin sigar tambaya daker ta hadiye kukan ba ya fu'ad bane, wani Abu yayi miki ne, shine ya koranmun driver yace dole shi ze kawoni school kawai saboda raina ya baci. Maamana gidan rikici toh kiyi hakuri yayanki yanaji dake ne shiyasa Amma yanxu ya kike so ayi? Nidae Abba kace ya dawo gida yabar asibitinshi Kuma akwai marasa lafiya toh aini dah idan kika gama exams nan garin zan dawo dake na nema miki Admission kucigaba da school keda Khadija, toh nayarda amma se kabar ya fu'ad a gurin daddy shima murmushi yayi yace maamana akwai wayau toh shikenan haka za'ayi tana shirme yana biyemata kafin tace bye bye ta sauke wayan tana sakin murmushi se yanzu taji zuciyarta tamata sanyi *Sumayya* Ajiyar zuciya tasauke tamatso kusa tadafa kafadar muhibbah tace "kawata kenan dama nasan ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki duk akan ya Fu'ad kike wannan damuwan se kace ba mace ba zaki zauna yana bakantamiki rai duk abinda yakeyimiki da gangan yakeyi saboda yaga idan yayi kinajin haushi amma da ace idan yayi miki kina danne abinda kikeji a zuciyarki da baze karaba nidai shawara nake baki idan kika cigaba da tada hankalinki baze ma so yakoma garinsu ba da gayya ze dinga miki abinda yasan bakya so" numfashi taja kafin tace banki ba summy amma bakisan damuwar da ya fu'ad yake samun ban... Ringing din wayanta ne ya katse maganan dasauri ta kara wayan a kunnenta murmushi me sauti tasaki tana fadin ina karasowa yanxu my husband to be, tana ajiye wayan ta mike summy ya mukhtar na jirana a waje mu karasa bata jira cewanta ba tayi gaba summaya tabi bayanta. *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 12* *Mukhtar* Tsaye yake jikin motarshi ya harde hannunshi daya a kirji ya dukar da kanshi kasa yana operating phone dinshi, cikin sanda takaraso ta fisge wayan kafin ya dago harta buya bayan motocin dake fake a gefenshi waige waige yashigayi be gantaba se kawarta dake tsaye tana murmushi kana yace malama kifito naganki, fitowa tayi tana dariya tana tambayarshi ya akayi ya gane itace ta fisge mai waya "Yace yaxa'ayi nakasa gane kece nasan babu Wanda zemun wasan nan se ke kin girma amma har yanxu bakibar abin yara ba yafada yana lakace mata hanci, turo baki tayi a shagwabe tace nidai bana so kuke cewa na girma ni babu wani girma da nayi, yace kin girma mana tunda gashi har kin fara tsayuwa da saurayi dasauri ta rufe fuska tana dariya tace to natafi tunda haka zakace ta juya zata wuce yayi saurin riko hannunta juyowa tayi tana kallonshi kana tayi saurin kwace hannunta tana turo baki" Kunnuwanshi ya rike yace gwiwowina a kasa wife to be na tuba bazan sake ba kara shagwabe fuska tayi tana dira kafa tareda make kafada tace aa, kneeling down yayi yayi fuskar tausayi yace nacefa na tuba dear dasauri tace haba shalele please katashi mana yace aa baxan tashiba har se kince kin hakura tace wllhi na hakura Dan Allah katashi kar mutane sufara kallonmu, Mikewa yayi yana murmushi yace thank you my princess itama murumushin tayi tace Kai din rayuwa tace ya mukhy idan narasaka bansan inda zansa kaina ba mutuwa zanyi, hannunshi yasa akan lips dinshi yace shiiiiii bana son kike ambaton mutuwa idan kika tafi kika barni to ni zaman mezan zaunayi a duniyan ina tabbatar miki idan narasaki bazan taba aure ba har abada, akwai abubuwan da baki yayi kadan wajen fadansu sedai a gansu a aikace mallakarki matsayin mata shi ze bani damar nunamiki irin kaunar da nake miki a aikace dan Allah Dan lelena kadena fadan haka bazaka taba rasani ba nidin mallakinka ce domin Kai kadai aka halicceni tafada tana kallon cikin kwayar idonshi hawaye na bin kuncinta shima cikin kwayar idonta yake kallo babu ko kiftawa yana hango tsantsar gaskiyar abinda ke fita daga bakinta ji yake kamar ya rungumeta tsabar kaunarta dake azalzalar Zuciyarshi hannu ya Kai ya daukemata hawayen fuskanta itama duk bugun zuciyarta wutan kaunarshi kara ruruwa yake a zuciyarta. *Sumayya* Gyaran murya tayi ganin takaraso inda suke amma basu ma san da ita ba tsabar yadda suka shagala a kallon cikin kwayar idanun juna kowa da abinda ke sakawa a ranshi, summy ce tace sannu Romeo & Juliet kun barni a tsaye kmr gunki over 1 hour kunata Shan soyayyarku kunma manta dani, murmushi mukhtar yayi eyyyaaa sorry kawarmu a gafarceni laifina ne, tace aa bakada laifi laifin wannan yarinyar ne tunda tare muka tawo da ita tayi maganan tana hararta eh dama gani karkataciyar kuka me dadin hawa dole kice shi beda laifi seni Murmushi yayi yace muhibbah gidan daru yanxu dai kawarmu na ari bakinta kiyi hakuri, murmushi tayi tashiga gaesheshi ya amsa cikin kulawa kafin ta juya ga muhibbah tace malama mutafi ko dan na gaji da tsayuwarnan wllhi, kafin muhibbah tayi magana mukhtar yace kushiga muje mall kuzaba abinda kuke so se in sauke ku gida ya bude mata murfin motan tazo shiga motan daga kan dazatayi idanunsu ya sarkafe dana juna gabanta ne yayi mummunar faduwa taji kamar kasa ta tsage ta shiga tsabar tsoron daya kamata jikinta ya hau kar Karwa tasan yau tashiga uku har lokacin idonsu yana sarkafe dana juna Mukhtar ne yace wai meke faruwa ne muhibbah me kike kallo ganin mukhtar ya Kai kallonshi inda muhibbah ke kallo yasa fu'ad saurin dauke kai danma karsu hada ido, dama tuni summy ta bude baya tashige ta hakimce jiki a sanyaye tashiga motar ya kulle kofan ya bude mazaunin driver yashiga yaja sukabar gurin ya fahimce sauyi tattare da ita amma dasun hada ido seta sakar mai murmushi A wani babban shopping mall yayi parking ya fito ya bude mata itama summy tafito suka nufa ciki yana dan Janta da fira chocolate dasu sweet kawae ta dinga dauka yace Sha zumamu kenan babu abinda kike so se chocolate kawae daga mai kai tayi tace bana bukatar komai wa innanma sun isa a ranta tace meze kaini daukar wani abu a gane naje mall nakarama kaina laifi wa innanma a jakata zan zubasu babu me gani, ya dubi summaya yace kema kin biye kawarki baki dauki komai ba se kayan zaki ko, murmushi tayi batare da tace komai ba karasawa sukayi suka dauki ice cream kafin sukaje yayi payment suka fito daga mall din. Summy na baya zuciyarta fal tausayin masoyan nan biyu irin kaunar da sukema junansu tana tinanin idan a kayi yunkurin rabasu wane hali zasu tsinci kansu a ciki, lallai duk wani masoyin daya rasa masoyinshi ya cancanci a tausayamishi tana Jin labarin soyayya ashe duk shirme ne se yau taga real masoya da idanunta, har kofar gida suka kaita tasauka tana ma mukhtar godiya, seda ta tsaya ta boye ledar shopping din cikin jaka dan tasan umma se ta tambayeta inda ta samosu Kuma batada bakin bata amsa kafin tanufa cikin gidan A hankali take Shan ice cream dinta gaba daya hankalinta baya jikinta dan tasan yau tagama shiga ukunta, kallonta yayi yace Sha zumamiya kawai waike yaushe zaki dena Shan zaki murmushin yake tayi tace ai Kam babu Rana bare wata dariya yayi yace ai Kam kin kusa denawa ganin sun kusa karasawa gida yasa tayi sauri ta shanye ice cream din ta boye ledar shopping din cikin jaka itama, a kofar gida ya ajiyeta ta fito tana daga mai hannu tace take care dear murmushi yayi yace luv you princess kana yaja motarshi tana tsaye tana murmushi seda tadena hango motarshi daga unguwar kafin tayi knocking gate din seda Mai gadi ya bude mata yana mata sannu da dawowa kafin gabanta yacigaba da faduwa yauwa ta amsa a takaice tasa kanta cikin gida. Bakinta dauke da sallama tashiga parlourn Fu'ad da Suhail ne zaune a parlourn suna firan kwallon jiya da aka buga Manchester vs real Madrid karasowa inda suke tace sannunku Suhail ne yace yauwa muhibbah an dawo lafiya, lafiya kalau Yaya tafada cikin sanyin jiki, kana tayi hanyan bedroom dinta taji yace keee tsayawa tayi kafin ta juyo tace na'am ya fu'ad idan kin canxa kaya kinyi lunching kisameni bedroom zuciyarta ce tayi wani tsalle kamar zata fado kasa yace kin kureni da ido ko bakiji abinda nace bane cikin rawar murya tace najiii. *Fu'ad* Tun isowarshi gate din makarantan ya hakimce jikin mota ya hango sanda tafito daga cikin school din amma da maamakinshi yaga ta nufa gurin wani da murmushinta yayinda yaga kawarta ta tsaya daga gefe, duk abubuwan da suka faru tsakanin muhibbah da mukhtar akan idonshi ne duk da bayajin abinda suke fada amma ya fahimce kalamai masu dadi suke musaya a tsakaninsu sannan ya fahimta shine wanda take fadama Abba akwai wanda take so tabbas babu tantama shine wannan, kanshi ya daure yayinda suka hada ido Kuma ta iya shiga motar a kan idonshi tabarshi a tsaye, yaushe yarinyarnan ta rainani haka ko tamanta waye niiii dama yasaba zuwa zuwa gate din makarantan suyi firane? Dama ba karatu takeyi ba saurayi take biyewa? Ganin bashida amsar tambayoyin yasashi buda motar yashiga yajata da gudu ya koma company be shiga ciki ba ya danna kiran Suhail babu jimawa yafito suka nufi gida har suka gama lunching bata dawo ba Kuma yatambayi mummy tace bata shigo ba bare yace ko tana bedroom dinta ne tunda yanxu bata cika fitowa ba har suka koma parlour suka zauna shiru bata shigoba abin nata yakara bashi maamaki yayi tinanin ze zo yasameta gida tunda sun rigashi tawowa toh inaaa suka tafi yana tsaka da tinanin yana biyema Suhail suna firan kwallon kenan se yaga shigowarta................. *Aminiyar ango ceeee *[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 13*