← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 69

Sashe 36

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take kasa kasa tarasa me yakeyi har yanzu be fito ba da ya bari da yanzu driver ya sauketa. Tafi minti 10 tsaye kana ya fito motarshi ya shiga ta zagaya ta bude gaban motan ta shiga me gadi ya wangale mai gate yana gaisheshi hannu kawai ya daga mai yaja motar yafice daga gidan. Shiru motar ya dauka babu wanda yayi magana kamar saukar aradu taji muryarshi yace "Wa kika tambaya kikaje gidan Ummi?" Duk da bada karfi yayi magana ba Kuma bada fada ba amma seda gabanta ya yanke ya fadi, shiru tayi tarasa me zatace "Ba dake nake magana ba?" "Babu kowa" tafada a sanyaye. Be Kuma cemata komai ba har suka isa school din. A bakin gate ya sauketa "Allah yatsare" "tnx" abinda yace kenan yaja motar yabar arean. Murmushi tayi ta shiga ciki, da sauban suka fara cin karo saurin hade girar sama da kasa tayi "Barka da safiya beauty" Shida banza duk daya a gurinta dan ko waigawa batayi ta kalleshi ba. Har department dinsu ya bita kana ya juya ya nufa class. Malam mukhtasir taci karo dashi a bakin department din su "Ina kwana" "lafiya kalau kanwarmu, yaya kike?" "Lafiya kalau" ta fada tana wucewa "Dan tsaya mana please Saurin me kikeyi haka?" Tsayawa kawai tayi tana kallonshi "Idan babu matsala ko zaki samun numbern ki?" da mamaki take kallonshi anya yanada hankali kuwa abokin ya Fu'ad ne fa, can kuma tace Koda yake ba laifinshi bane laifin ya Fu'ad ne da yace mai kanwarshi ce ni. "Dan Allah kayi hakuri yaya baya barinmu rike waya ko Assignment zamuyi sedai muje cafe ko Kuma ya bamu nashi muyi" "Hakan ma yayi wannan tarbiyya ne me kyau, toh Kona mama ne ki bani akwai maganar da nake so muyi ne" "Allah sarki gashi ko ban haddace numbern Ummi na ba, amma zuwa gobe idan ban manta ba zan rubuto a paper" bata jira amsarshi ba ta wuce class. Kusa da Aesha ta zauna ranta a jagule "lafiya kuwa matar Yaya?" "Lafiya kalau, me kika gani?" "Naga kin shigo rai a bace ne" "Babu komai ke Kam, amma dan Allah kidena kirana da matar yayan nan a class kar mutane su kama". Karfe 10 suka fito daga class suna zaune da wata Kawarsu dasukayi A kunne Aesha ke rada mata "Wai yau meke damunki ne? badai yayana bane ya batamiki rae?, ko Kuma babynmu ne ke wahalar mana dake, yake samana ke bacin rai kinsan masu ciki akwai saurin fushi". Tsungulinta tayi a cinya tako saki kara mara sauti Muhibbah tayi dariya "Kadan namiki karki kiyayeni da wannan maganan kiga yadda zamuyi dake". "Assalamualaikum" Kusan a tare suka dago su duka ukun, akan sauban suka sauke idanunsu, dauke kai tayi, Umaina tace "Wa alaekumussalamu warahmatullah". "Dan Allah idan babu matsala ina son magana dake, Kona minti daya ne" dogon tsaki ta buga twsssss "Just 1 minute please" ya fada yana hada hannayenshi biyu alamar roko. Umaina ce tace "Karki ce nayi miki shisshigi tunda ya hadaki da Allah ki saurareshi ko Yaya" harara ta watsamata tareda daga mata hannu, Jan bakinta tayi tai shiru batakara cewa uffan ba. "Ko sunanki ki daure ki fadamun ki tausayamun tun jiya da na dora idanuna a kanki naji cewa a raina in Sha Allah nayi mata" a hassale ta mike ta bar gurin fuuuuu, Aesha tabi bayanta, Umaina ta bisu da kallo. Dawo da hankalinshi wajen Umaina yayi "Dan Allah ki shawomun kanta please" Kai ta Jin jina "okay I will try my best" "Nagode zuwa gobe zan dawo in Sha Allah". Jinjina Kai tayi itama ta mike tabi bayan su. Shiru yayi yana tinani dagaske dai ba matar aure bace tunda da matar aure ce da kawarta nan ta kara fadamishi. "Haba Fateema miye haka? Wulakanci babu kyau Koda bakya son shi at least ko hakuri kika bashi zeji dadi". "Dan Allah Umaina ki kyaleni naga kema macece zaki iya karbar soyayyar shi idan ya miki, jiya ba'a yi mai magana bane yaki sauraren mutane" "Sister calm down ki rabu dashi ze gaji ya kyaleki, Umaina wannan mutumin da kike gani dan rainin sense ne jiya babu abinda bamu ce mai ba yaki ji kema ki fita batunshi kawai". Ajiyar zuciya tasauke "Toh ai bansaniba, ai shikenan". Koda suka tashi sun fito sun fara takawa zuwa inda drivern su yayi parking sukaga wata mota ta tsaya gabansu glass din motan ya sauke "ku shigo na kaiku gida" cewar malam mukhtasir "Mun gode ga driver can na jiranmu" tana Kai nan ta wuce. Tana gani aka sauke Aesha kamar ta bita, juyawa yayi itama ya sauketa gida. A parlour tasamu mairo "Sannu da dawowa hajiya" "Yauwa Aunty mairo, ya zaman shiru?" "Alhamdulillah" "Nace miki kisaki jikinki, kin zauna shiru ko tv base ki kunna ba ya dan debe miki kewa" ta fada tana karasawa ta kunna tv din. Ita dai murmushi kawai tayi. Seda tayi wanka kana ta dawo dining tayi lunching, fira suka shigayi ita da mairo wajen 5 mairo tace "Ina so zan tafi" "Kai Aunty mairo tun yanzu?" "Yamma tayi hajiya" "Toh shikenan Allah yatashemu lfy" har tsakar gidan ta rakota tasa driver ya kaita kana ta juyo ta dawo parlourn. Abinci mara nauyi ta dafa taje tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigan material me santsi tasa hula rabin kwantacen gashinta a waje ta shafe jikinta da humra. Serving dinshi tayi itama ta zauna tana cin nata a hankali Ta kasan ido yake kallon ta sosai yaci abinci kana ya tashi ya koma parlour, harta fara taka staircase taji yace "Hado mun coffee" dan turo karamin bakin ta tayi ta koma kitchen ta hado mai Center table ya nunamata ta ajiye a Kai ta wuce. Brush tayi ta canza kayan jikinta zuwa na bacci ta haye gadon bata jima ba bacci ya kwasheta dan ba karamin bacci takeji ba. Ya jima zaune yana aiki ta wayanshi yanayi yana sipping coffee dinshi seda ya kammala ya mike ya nufi dakinshi, toilet ya nufa yayi brush ya dawo ya feshe jikinshi da turare ya fito daga dakinshi. Hannunshi ya daura kan handle din kofar yana murdawa yajita bude a hankali ya kutsa kanshi ciki, a hankali ya karasa kan bed din ya haura rungumota jikinshi yayi, ita ko har wani gyara kwanciya take a kirjin shi tana cusa Kai tana shakar kamshin shi cikin bacci. Wani shock yaji ajikinshi saboda yadda take narke mai a jiki. Shin Shinar wuyanta yake yana ya mutsa gashin kanta yashiga yawo da hannunshi a jikinta hannunshi ta rike a hankali ta bude idanunta dakin duhu bata ganin komai "Waye ne?" "Ki nutsu wa kike tinanin ze shigo dakin ki a daren nan". Kara wara idonta tayi ashe ba mafarki takeyi ba se yanzu taji kamshin turarenshi Zame hannunshi yayi daga nata ya cigaba da yawo dashi a jikinta. Kuka tasa "Dan Allah Yaya ka kyaleni bacci nakeji" "cigaba da baccin ki ni ban hanaki ba" Jin bashida niyyan denawa tasaki kuka me sauti "shiiii yimun shiru wani abu namiki kikemun kuka" yayi maganan yanayin kasa da hannunshi. Cikin kuka tace "Dan Allah Yaya kabarni" "Ni ba wani abu zan miki ba sadakina na zo mora". "Wayyo Allah mummy na, Allah zan biyaka sadakin ka zan dawo ma da kudinka ka kyaleni" saura kadan dariya ta kufce mishi ya fiske. "Dama ana dawo da sadaki ne banida labari?, fadamun inda kikaji an tabayin haka" yana maganan yana yin kara kasa da hannunshi. Ban karewa tayi tana ihu "Wallahi Yaya banida tsarki, period nakeyi" "Toh bari na duba da kaina na gani" ya fada yana zare rigar baccin jikinta......... [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION* *Page 41* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 Ganin tana neman sume mishi yasashi sakinta yana fadin matsoraciya kawai. dasauri ta janyo blanket ta lullube har kanta. Ficewa yayi daga dakin yajanyo mata kofar ya rufe ya nufi bedroom dinshi toilet ya fada ya sakarma kanshi ruwa ya dan jima a toilet din yafito daure da towel kayan bacci ya zira ya haye gado ya kwanta lumshe ido yayi yanajin kamar har yanzu tana kwance a kirjinshi. Kuka taciga da rerawa har bacci ya kwasheta bata dena sauke ajiyar zuciya ba Da ciwon Kai ta tashi saboda kukan da tayi daren jiya a daddafe ta hada breakfast tayo wanka tayi Shirin school A dining ta sameshi a sanyaye tace "Ina kwana" "lafiya kalau" ya fada ba tareda ya ko Kalli inda take ba Serving dinshi tayi ta tura mai gabanshi kana ta hada tea tana sipping tanajin kanta kamar ze cire, ido ya dan tsuramata na seconds ya dauke kai ya cigaba da cin abincin shi. Can ya mike ya nufa kitchen har lokacin bata shanye tea din ba hannunshi rike da first aid box ya fito, dago kanta tayi suka hada ido sun kai minti 1 suna kallon juna kana ta danyi kasa da kai A kan dining ya ajiye box din ya bude ya dauki paracetamol ya mikamata, bata fuska tayi "Nifa lafiyata kalau" wani mugun kallon da yake mata yasa tayi saurin karba ta balli biyu ta watsa a baki ta kora da tea tana yamutsa fuska.Ganin ya ciro allura yana kokarin fasa paracetamol ya zuka a siringe din tayi saurin mikewa tana zare ido kamar tayi karya, tsayawa yayi yana kallonta tafara girgiza Kai "Dan Allah kabarni wllhi lafiyata kalau kaina kawai ke ciwo zanji sauki" kafada ya dage ya dauki box din ya maida. Ya dawo ya zauna ya ciga da cin abincin shi hankali kwance Dakinta ta haura ta dauko jaka tazo ta tsaya dan nesa dashi "zan tafi, karfe 8 mukeda lectures" Kai kawai ya jinjina. "Kuma yau lecture daya garemu dan Allah zan biya gidan ummi" tayi maganan tana marai raice fuska amma gabanta faduwa yakeyi a tsorace take. Shiru yayi ba tareda yace mata komai ba. "Dan Allah inje???" Ta kare maganan da sigar tambaya. Daga mata Kai yayi alamun eh, da fara'arta tace "Tnx" ta fice. Sauri sauri tashiga school din tanayi tana duba agogon dake daure a damtsen hannunta 5 minutes to 8 takoyi sa'a lecturer be karaso ba General mathematics MTH 101 suke dashi 2 hours suka kwashe a class.
Chapter 36 · 0% Book details