Sashe 4
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga my yaya (A planner/Angon Fateema Kuma Abban Fateema) har gaban gobe ana kyawun tare* *Page 6* "Bangaren su daddy ma haka ne ta kasance sun dau tsawon lokaci suna tattauna muhimman abubuwan da ya kawo Abba seda suka kammala kafin kowa ya wuce makwancinsa" Karfe 8:30am tafito shirye cikin uniform dinta, parlourn daddy ta nufa bakinta dauke da sallama seda aka bata izinin shiga kafin ta shiga risinawa tayi tareda fadin " Ina kwana Abba?" "Lfy kalau mamana, xa'a tafi school din kenan" Eh Abba, toh Allah yabada sa'a Ameen ta amsa dashi kafin ta juya ga daddy shima ta gaesheshi addu'a yayimata kafin ta juya ta fice. "A dining tasami a halin gidan karasawa tayi cikin sakin fuska ta gaeda mummy kafin ta juya ga su Suhael Suma ta gaeshe su da mamaki mummy take kallonta ganin bata zauna breakfast ba tajuya tanama mummy sallama, har ta Kae bakin kofa mummy takirata juyowa tayi takara so inda take Lafiya zaki fita bakiyi break fast ba? Lafiya kalau mummy inada paper by 9 and now it almost 8:45 idan muka fito paper zan siya snacks a cafeteria tana kai nan ta fice daga parlourn binta mummy tayi da kallo tana Mata addu'ar samun nasara a exams dinta. "Dasauri ta bude motan tashiga tana fadin I'm sorry malam bala namanta nafadamaka yau se 8:30 zan tafi school nasan tun 7:30 kana jirana, murmushi yayi yace babu komae hajiya karama nayi tinanin ko bakida Lafiya ne najiki shiru seda nayi sallama parlour natambayi hajiya babba take cewa najiraki kina fitowa ya fada yana danna hancin motan waje, Lafiya kalau nake mun fara exams ne zan dinga fadamaka lokacin dazaka dinga fitowa" Seda taga ya hau kan titi kafin tabashi umarnin yayi gudu saboda takusa makara, ae Kam gudu yake kamar ze tashi sama kasancewar school din bawani mugun nisa ne tsakaninsu da gidanba yasa cikin mintina kadan Suka Isa fita tayi daga motar tana fadamishi lokacin daze dawo daukanta saboda yanxu tsarin lokacin zuwansu da tashinsu ya canza tana gama fada tashige cikin school din. "Saura 5 minutes a Fara exams ta shiga hall din haka yasa batasamu damar gaesawa da Aminiyar ta Sumayya ba Kuma ba seat daya yau zasu zauna ba saboda according to exams number kowa ze zauna, karfe 9:00am Suka soma exam din. "Daddy ne yafito parlourn ya dube Suhael yace su tafi company tareda Fu'ad shikuma suna tare da Abba" Basu jima ba Suka shirya sukayima su mummy sallama Suka nufi company. Karfe 11 suka fito daga hall din ita da Sumayya, dafe cikinta tayi tana hamma tace wash mukarasa cafeteria wallahi tun muna exam nakeji cikina na juyawa yunwa nakeji, rike hannunta tayi suka karasa cafeteria suka siya snacks da drinks Suka dawo main class dinsu suka zauna suna ci suna fira "A gogon dake daure a damtsen hannunta ta duba 10 minutes after 12, dasauri tamike tana goge baki da tissue paper tace tashi mu tafi driver nasan yanzu yana jirana, A bakin gate Sukayi sallama tashiga mota suna dagama juna hannu itama bata jima ba aka zo daukanta". Parlourn tashiga bakinta dauke da sallama babu kowa hakan yasa ta wuce bedroom dinta uniform tacire ta daura towel tashige toilet, seda tayi wanka tayi sallah kafin ta nufo parlourn a zaune tasamu mummy tana kallon tv risinawa tayi tace "Sannu da gida mummy, yauwa muhibbah ya exam din? Alhamdulillah amma babu dadi ta fada tana zama a dining murmushi mummy tayi tace kowa kafin yazama wani a duniya seda yasha wahala haka Suka dinga fira tana cin abinci tana kammalawa tace ma mummy bari tashiga ciki tadan yi bacci. "Bata farkaba se bayan la'asar, alwala tadauro ta gabatar da sallah bayan ta idar ta nade pray mat din ta ajiye kafin ta dauko littafanta ta barbaxa saman bed tana dubawa se gaf magrib mummy ta murdo handle din kofan tashigo dagowa tayi ta kalleta tasakarmata murmushi tace najiki shiru ne nace badae bacci kikeyi ba har magrib ya kunno Kae" Itama murmushi tayi aa mummy natashi tun dazu karatu nake dan tabawa gaba daya kaina yayi chaji gobe inada biology by 9 Kuma idan na fito karfe 12 inada (Adab). Eyyaa Sannu shalelen daddy exam din nan yazo lokaci daya ga waec ga mbais ki dage Allah ya taemaka, Ameen mummy na tafada tana mikewa jin ana Kiran sallahn magrib Nikam mummy banji motsin su daddy ba ko sun fita ne? Eh sun Dan fita da Abbanku Amma sun dawo shine ma yace na fadamiki karfe 8 kisameshi a parlournshi, Toh Allah ya kaemu tafada tana tattare littatafanta, Ameen ta amsa dashi kafin ta bar dakin. "Wanka tayi tadauro alwala ta gabatar da sallah tana zaune har aka kira isha'i mikewa tayi ta gabatar da sallahn kafin ta bude wardrobe tadauko Kayan daxatasa gaban mirro ta tsaya tashafa body lotion tashirya cikin riga da skirt na atamfa golden ta fesa turare har tanufa hanyan fita se Kuma ta tuna gurin daddy zataje tasan idan yaganta babu dan kwali seya mata fada dasauri ta dauki dan kwalin ta daura ta nufa parlour da mamaki taga babu kowa Bata kawo komae a ranta ba ta nufa dining tazuba abinci taci cikin hanzari saboda taje tasamu daddy. "Bakinta dauke da sallama ta shiga parlourn daddy gabanta ne yayi mugun faduwa ganin a halin gidan gaba daya a parlourn, daddy da Abba suna zaune a 3 seater se mummy a 1 seater Fu'ad kuma yasamu guri kasa kusa da kafafuwan daddy ya zauna Suhael shima yana kusa da Abba yayinda Anas Kuma ke zaune wajen kafafun mummy, Lafiya? Ganin batada amsar tambayan yasa ta samun guri daga dan nesa tazauna tana facing din su Abba, Ido Suka hada da Fu'ad tayi saurin dauke kanta ita dae tunda yazo banda gaesuwa babu abinda yake hadasu, risinawa tayi tasoma gaeda su Abba Suka amsa cikin sakin fuska" Abba ne yafara magana dacewa Alhamdulillah a gaskiya najima banyi Farin ciki kamar na kwanan nan ba abinda muka dade muna fatanshi Kuma muna burin kasancewarshi se gashi Allah ya amsa mana addu'o'inmu yacikamana burinmu fatan mu Allah yasa munada rabon ganin wannan rana me cike da Farin ciki ita dae kanta na kasa tana wasa da yatsunta jifa jifa idan ta dago se su hada Ido da Fu'ad Daddy ne yacigaba da maganar fuskarshi dauke da fara'a da kaganshi kasan yana cikin farin ciki babu abinda zancema Allah se godiya abinda yasa muka taraku anan ba wani abu bane face Muna so mu sanar daku cewa mun tsaeda ranar auren Fu'ad da muhibbah domin idan akwae me wani shirin ya soma dasauri ta dago cike da mamaki tasauke idonta akan Fu'ad shima ita yake kallo da mamaki ji tayi maganar ta daki dodon kunnenta ya yimata nauyi a kirjinta duniyar tayi mata duuuum komae yatsayamata cak.............[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* Dedicated to *my lovely brother* *Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare* *Page 7* "Kuka ta fashe dashi tana girgiza kae tana fadin wllhi daddy bana sonshi bazan iya aurenshi ba nashiga uku na da kallo Suka bita abin har yaso yabasu tsoro yadda take kuka tana fadin Bata sonshi" Shiru dakin ya dauka se sautin kukan ta dake tashi Abba ne ya mike ya nufeta ya rikota ya mikar da ita tareda zaunar da ita akan kujera "Yi shiru mana mamana kukan ya isa haka nutsu ki fadamun me yayan naki yamiki da bakya sonshi fadamun inji idan laefi yamiki da kaena zan hukuntashi a gabanki ki gani, A jiyar zuciya tasauke tana goge hawayenta tace Abba ni bana son ya Fu'ad mugu ne baya sakin fuska ko dariya seya ga dama yakeyi lokacin da ya zauna a gidan nan harda belt yake dukana ni natsa neshi ma kwata kwata gara ko almajiri ne a aura mun Kuma ma inada wanda nake so dan Allah Abba Kar ku auramun ya Fu'ad ta karashe tana kallon Fu'ad tana sakin sabon kuka, wani Abu ne ya tokare Mae zuciya wato data aureshi gara ta aure almajiri, Allah ya kyauta Nima na aureki mexanyi dake ya fada a zuciyarshi yana cije lips dinshi na kasa tareda fitar da wani iska me xafi" Shi har ga Allah ma dariya ta bashi yace mamana kin girma amma har yanxu dae baki dena rigima ba "Cikin bacin rae daddy yace muhibbah kifita idona a kwae abokin wasanki ne a nan idan nakaraji kin furta bakya son shi anan wllhi se jikinki ya gaya miki" Karasawa kusa dashi tayi ta tsugunna kasan kafafunshi tana kuka tace daddy ka tausayamun Kar kace na aure ya Fu'ad wllhi bana sons....... Wani zazzafan Mari ne yasata saurin hadiye maganan, daker ta janyo numfashinta tareda fashewa da wani irin kuka me tsuma rae, kuka take kamar ranta xe fita tun ana ganin abun kamar wasa har Suka soma jin tsoro ganin yadda numfashinta ke barazanar daukewa tsabar kuka. Allah sarki uwa "Mummy ce ta mike jiki a sanyaye ta nufeta ta rungumota jikinta tanajin ranta babu dadi har da laefinta acikin faruwar lamarin nan batayi domin cutar da diyar ta taba tayima lamarinsu mummunar fahimta ne, lallashinta tasoma yi daker tasamu tayi shiru se ajiyar zuciya take saukewa kamar wacce tayi tseran gudu" Shikenan mamana tunda bakya son auren nan babu Wanda ze miki dole ki nutsu kiyi karatu sosae Kar ki daga hankalinki kinga exams ne a gabanki idan kika gama exams din ki kirani a waya zandawo se muyi magana da surukin nawa kinji ko? Dasauri tadaga Mae Kae tadan yi murmushi alamun taji dadin maganarshi yace yawa mamana to tashi kije ki kwanta Kar ki makara zuwa school. Ba musu ta mike a sanyaye tamusu sallama ta nufi bedroom dinta, suma sauran Suka mike suka nufi makwancinsu mummy ma ta mara musu baya, yayi saura daddy da Abba a parlourn "Duban Abba daddy yayi yace haba Yaya ya zaka biyemata mufa muka haefeta ba ita ta haefemu ba dazata nemi juyamu saboda rashin kunya shi Fu'ad beyi magana ba se ita, murmushi yayi yace ba wae na biyemata bane