← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 69

Sashe 61

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga kaji wani labarin, zamuyi waya" tana Kai nan ta juya tana daga mai hannu ta shige ciki. *********** "Ammi! Ashe Muhibbah matar aure ce, duk zuwan da suke bamu taba sani ba" "Nima ban kawo tanada auren ba se yau da idanuna ya kai kan cikin, fatan mu dai Allah ya sauketa lafiya" "Ameen ya rabbi" ita dai zeeee na kwance tana chatting da farin cikin ranta, tanajinsu bata ce musu komai ba. *********** "Miye alakarki da wanda na ganku tare yazu?" Yayi mata tambayan kamar be taba sanin wanda ya ganta dashi ba. Ummi ta kala, ita ko ta dauke kai, dan tunda ta fito da mayafi ta tambayeta ina zata tace wani course mate dinta ne yazo zata bashi book dinshi, tace babu ruwanta idan Abba ko Fu'ad suka zo suka sameta Murya na rawa tace, "B...a..bu komai" "Toh kar inkara ganinki dashi". Saurin gyada kai tayi kana tace "Tom" Muhibbah tace, "Kaima Yaya tunda kaganshi a gurinta ai kasan da dalili ko" "toh gaban kanta takeyi? Izinin wa ya nema? Saboda haka kar na kara ganinta tsaye da shi". "Kayi hakuri, ze nema in Sha Allah" be kuma cewa komai ba, ya janyo wayarshi yashiga operating. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin Muhibbah ya shiga wata tara a Koda yaushe zata iya haihuwa, duk yadda yaso ta dena zuwa school taki tace babu amfanin zaman gidan zuwa makarantanma exercise ne. Zuwa yanzu duk course mates dinsu sun san matan aure ce saboda yadda cikinta yayi Kato a gaba kamar kwallo duk da babyn yayi kasa alamun yana gab da fitowa. Kullum hankalinshi na kanta se yazo school din sau biyu kafin su tashi, kawai dan ya dubata. Ko ya tafi baya 1 hour be kirata ba, ko tace kalau take, seya kira Aesha yakara tabbatarwa. idan suka tashi school ma gidan Ummi take tafiya se yamma yazo ya dauketa. Rigunan da aka dinkamata take zunbulawa taita yawo a ciki, sunyimata yawa sosai amma tafi jinta comfortable aciki, su Aesha dasu Umaina idan suka Kalli fadin rigunan suyita mata dariya, tun tana tankasu harta dena bi ta kansu. Su ummi ma hankalinsu na kanta kullum addu'arsu Allah ya sauketa lafiya, haka mummy hankalinta na kan autan ta kullum seta kirata sau 3 sau 4. Ita kam Muhibbah tafisu shiga damuwa, A tsorace take kullum gabanta cikin faduwa yake kawai daurewa takeyi. Wata ranan Sunday da dadare labour ya tashi mata, tana sanye da vest da mini skirt suna zaune suna fira, ta soma jin changes a jikinta amma seta daure saboda bata so ya daga hankalinshi tasan idan ya fahimta yanzu duk ze damu kuma ba wani sosai bane ciwon. Jin ana Kiran isha'i ya mike yayi pecking goshinta ya fice, tayi murmushin yake tana mai bye bye Kokarin mikewa ta fara taje tayi sallah, taji mararta ta murde, da sauri ta zamo kasa ta tsugunna, tun tana Jin ciwon kamar wasa wasa, a hankali ta soma jin bayanta na rikewa, mararta na tsananta ciwo. Bakinshi dauke da sallama ya shigo parlourn nishin ta yasoma jiyowa, da sauri ya Kalli inda ya barta ai ko ya hangota durkushe tana murkususu A guje ya karasa ya rukota "Heebbah! Lafiya? Meke miki ciwo?" Takasa magana se jujjuya Kai take tana nuna mai bayanta. Cikin tashin hankali ya dauketa cilak ya fice daga parlourn, ko tinawa da wani hijjab beyi ba yasata gaban motan Shima ya zagaya yashiga ya fige motan a guje ya fice daga gidan, yana driving yana shafa fuskanta cikie da tausayawa, gani yake driver baze mai gudun da yake so ba shiyasa ko takanshi be biba. Tun daga nesa yake horn me gadi ya wangale mai gate ya danna motan ciki, ya fito ya dauketa yayi labour room da ita doctor fareeda ta mara mai baya..................... AMINIYAR ANGO * * Aminiyar ango *[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD* *AMINIYAR ANGO* *Page 57* Kan gadon ya daurata ta rikeshi gam tana hawaye tana cije lips "Hearty marata wayyo Allah bayana, kuguna ze cire nashiga uku na" Fuskanta kawai yake shafawa yasa hannunshi biyu yana gogemata hawayen, yama kasa magana dan ji yake shima kamar ze zubda kwalla. "Sir please bari na dubata" doctor fareeda tafada tana karasowa inda suke, shi gaba daya ma ya rasa ta ina ze fara se da doctor tayi magana kana yafara kokarin zare hannunshi daga nata, takara rikeshi. Kanta ya shafa yasa hannu ya tallabo habarta, idanunshi yasauke cikin nata cike da tsananin tausayawa yace, "Sorry dear, ki bari doctor ta dubaki, ko bakya so mararki tadena ciwo?" Saurin gyada mai kai tayi. Yayi pecking goshinta cikin dubara ya zare hannunshi daga nata, ya matsa baya yana kallonta zuciyarshi gaba daya ta karye, duk da shi ba mace bane amma ya karba haihuwan dubannin mata yasan irin wahalar da suke Sha Hand gloves tasa ta karasa ganganta "Sorry madam, dan kwanta mu gani" tafada tana taimaka mata ta kwanta. Skirt din jikinta ta janye sama, ta kai hannunta tana kokarin zame pant din, tayi saurin mikewa tana ja baya ta jingina da bed din tana zare ido kamar mara gaskiya. Girgiza kai tayi, tayi murmushi, idan da sabo tasaba ganin irinsu Muhibbah, se aita fama dasu su kafe. amma idan labour yayi labour har riga suke cirewa tsabar azaba. Tasan yanzu duk wasan kwaikwayo ne shiyasa har tasamu daman abubuwan nan amma kuka na gaba. "Doctor ina ga sena nemo wata ta tayani ni kadai bazan iya da madam ba" beyi magana ba yakaraso ya rike hannayenta yana mata dubara hade da kalamai masu kwantar da hankali, a haka har doctor ta samu ta rabata da wandon ta dubata, tako saki kara. Hand gloves din ta zare ta zuba a sharp box tace, "doctor ta kusa, yanzu 8cm remain 2" jinjina kai yayi, ta juya ta fice. Bata jima ba tadawo hannunta rike da kayan aiki, tazo ta rike hannunta tafara neman vein da mamakinta batayi darun data saba ba se hawaye kawai ke bin kuncinta. Shikuma yana zaune kan stood dake gefen bed din, ya gimtse dayan hannunta cikin nashi, dayan hannunshi kuma yanata aikin share mata hawaye hade da rarrashinta da karfafa mata guiwa. Drip ta dauramata ta kawo wata allura (Oxytocin) ta zuba cikin drip din. Tana kwance lamo kamar me bacci, ciwon maran ya lafamata. Ruwan natafiya da dan sauri dan har yayi rabi, kamar an tsikareta ta tashi zaune tasa hannu ta fisge canularn tasaka ihu. Cikin kidima ya rike hannunta da jini ke faman zuba yace, "Heebbah! Ya akayi? Meyasa kika cire drip din gashi kinsa jini nabin hannunki" yafada hankali tashe. Ita bama ta hannunta takeyi ba dan bata fahimtar abinda yake fada, kuka me sauti ta fashe dashi "Yaya marata, innalillahi wa inna ilaehi raji'un........" Yana rike da ita a jikinshi duk ya kidime, se doctor fareeda ce ta karaso ta kwantar da ita ta duba taga ta kai 10cm "madam push, ga babynki nan na neman hanyan fita" nishi tashigayi iya karfinta, kuka take amma hawayen sun kafe tsabar azaba. "Yauwa madam push, ga kan babyn nan" "doctor kibarni na gaji" "Sorry madam ki daure, kin kusa" tafada cikin kulawa. Nishi tacigaba da yi, baby ya doso a lokaci daya kuma mararta ta wani murde, A zabure ta zira kafarta kasa tana kokarin sauka daga gadon. Da hanzari suka rikota tasaki kuka me sauti, "bayana, kuguna Wayyo Allah marata. Mummyna ki haifemun Allah yabiyaki da gidan aljannahtul firdaus, kai innalillahi wa inna ilaehi raji'un........." Shiko baby burinshi kawai ya ganshi a waje dan ya gaji da rayuwar duniyar su, se neman hanyan fitowa yake "Yaya mutuwa zanyi, ka kiramun mummyna, wayyo Allah na dan Allah ka kiramun Ummi da sister, Ko munada rabon sake ganawa kafin na mutu, bazan iya ba" "Heebbah zaki iya" Kai kawai ta girgiza dan tagama sarewa da lamarin duniya Be ankaraba yaji hawaye na silalowa daga idanunshi yakasa magana se girgiza kai kawai yakeyi zuciyarshi ta karye idan yace zeyi magana kuka ne ze kufce mai, bata kula ba ya zame hannunshi daga nata ya juya dasauri ya fice, dan baze iya jure tsayuwa a gabanta cikin wannan halin ba, Mota ya dauka ya fice, gudu yake kan titi kamar ze tashi sama. Horn ya danna aka bude mai gate ya kutsa ciki, yanayin parking ya nufa ciki dasauri, wani karamin akwati da Aesha ta hada kayan baby dana maman babyn aciki ya dauko ya shige mota ya fice daga gidan. Koda ya koma asibitin kasa shiga labor room din yayi sai wata nurse yaba akwatin ta mika cikin room din shikuma ya koma office dinshi. Waya ta daga takira wata nurse, ba jimawa se gata ta shigo labour room din Ita ko ta kasa magana se binshi da ido da tayi har ya fice daga room din, gaba daya hawayenta sun kafe tazama kalar tausayi se jujjuya idanu take, takasa fahimtar a duniya take ko akasin haka. Wani nishi me karfi tayi dabata san yaushe yazo mata ba, se ga kan baby ya leko. lokaci daya kuma wani azaba ya ziyarce ta tayi ihu tareda hada kafafunta tana kokarin matse kan babyn. "Madam haka zamuyi dake Kuma? zaki matse kan babynki, ki daure kin kusa saura kadan" "Ni ki kyaleni nace miki bazan iya ba, ko dan bakisan azaban da nakeji ba, tun dazu se cewa kike na kusa amma har yanzu shiru" tafada da karfi cike da masifa. Murmushi kawai doctor tayi bata ba maganarta muhimmanci ba ta rike kafafun Wani nishin taji yana zuwanmata ta takura ta saki nishi me karfi tareda furta "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un......." Cikin taimakon Allah Sega babynta ta sunbulo. Nurse din tayi sauri ta tare ta fada hannunta Wani nannauyar ajiyar zuciya tasauke ta kwanta lamo ta rufe idanunta tana furta Alhamdulillah a kasan zuciyarta, wani sanyi takeji kamar ancire mata kaya, tanajin kukan babyn amma ko magana takasa bare ta tambaye me ta haifa. Zama yayi ya kunna CC TV camera yana kallon abinda ke faruwa a labour room din, duk ya rude se karanta duk wata addu'a data zo bakinshi yake, zuciyarshi tayi rauni baya so kuma ya kira su ummi ya daga musu hankali. yana ganin fitowar baby ya mike da
Chapter 61 · 0% Book details