Sashe 5
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kaga munyi ma abun mummunar fahimta a yanayinsu munyi tinanin akwae alakar soyayya Kuma danazo mummyn su itama tace ta fahimta hakan a tsakaninsu ashe duk bamu fahimce su bane shiyasa muka yanke hukunci batareda munji ta bakinsu ba, Amma yanxun ma bazamu janye ba a kyaleta tagama exams dinta karta daga hankalinta tasamu matsala idan yaso bayan ta kammala se ayi abinda yadace Dan dama ni ko ba'a fahimce wani Abu game dasuba inada burin mu hadasu aure domin Karin dankwan zumincinmu" Se lokacin yaji sanyi yace toh shikenan ae Yaya hakanma yayi dama Kar yazamana an biye Mata ace anfasa ne Amma shawarar nan ma tayi, se a fadama iyayensu Mata su su sanar da makusanta se a soma shirye shirye, hakanma babu damuwa se da Suka gama tattaunawarsu kafin suka tafi makwanci. [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Dedicated to my lovely brother* *Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare* *Page 8* "Jiki a sanyaye ta isa bedroom dinta ta fada toilet tasakarma kanta ruwa tajima a toilet din kafin ta dauro alwala ta fito daure da towel, wardrobe tanufa ta dauko nighties ta shirya Riga ce me sirirrin hannu se wando iya gwiwa" Kwanciya tayi luf akan gadon tana sauke ajiyar xuciya ta na tino abubuwan da Suka faru a parlourn daddy, da hk har bacci yayi awan gaba da ita "Shima bangarenshi hakan ne ta kasance yana kwance idonshi a rufe amma ba bacci yakeba ya tafi tinani gabanshi babu abinda yakeyi se faduwa yana ganin fuskarta yadda ya hango tsanarshi karara a cikin kwayar idonta babu abinda yake bakanta Mae rae kamar yadda take na nata bata sonshi Kuma kalmar daga kasan zuciyarta yake firowa iya gaskiyarta take fada Amma ta wani bangaren yaji tunda sanadiyyar boren datayi anfasa auren dan koda anyi auren yasan xaman baxe musu dadi ba tunda shima baya sonta Kuma dama tun farko basa jituwa tabashi mamaki ma data yarda da soyayyar kwana dayan dasuka shirya Amma yayi mamakin yadda Abba ya janye maganar auren Nan cikin sauki da haka bacci ya daukeshi Fitowa tayi sanye da uniform, a dining tasamu a halin gidan karasawa tayi ta risina tace "Abba Ina kwana? Lfy qlau mamana an fito Kae ta gyada tace Eh" Daya bayan daya ta gaedasu tana zuwa kan Fu'ad ta dauke Kae taja kujera kusa da Abba ta zauna, Tea ta hada ta soma sipping dinshi a hankali kamar an Mata dole, muryar Suhael ta jiyo kamar daga sama yana cemata muhibbah ashe baki da kunya banida labari? Fu'ad din sa'an kine ki gaeda kowa amma ki kalleshi ki watsar, shi sa'an ki ne Ina tambayarki kinyi mun shiru da sauri ta girgiza kae tace aa big bro yace to gaesheshi Kasa da Kae tayi tana Wasa da yatsunta belt dinshi ya xare ya nufeta yace gaeshar dashi nace, da sauri ta mike ta Isa gareshi tace Ina kwana Dan tasan ba karamin aekin suhael bane ya xaxxabgamata belt din ta tafi makaranta da kuka yanada saukin Kae amma baya son raeni ko kadan Kuma baya so a gabanshi yaga mutum na raena na gaba dashi to anan ne zakuyi fada dashi Ko kallon inda take beyi ba bare tasa ran ze amsa gaba daya ranshi a bace yake ya rasa ya akayi ya bari yarinyar ta raenashi ko tamanta wayeshi ne oho, wani murmushin mugunta yayi a ranshi yace nasan mexanyi zan gyara miki zama "Hawaye ne suka Fara bin kuncinta bakin cikinta yanxu daddy saboda Fu'ad ya juyamata baya yadena supporting dinta, wayarta ta dauka ta nufi hanyar fita tajiyo muryan Abba kiranta cak ta tsaya ya karaso kusa da ita yace yau zamu tafi baki bari munyi sallama ba ko ni ma fushin kikeyi dani, murmushi tayi a xuciyarta tanama Allah godiya yau Fu'ad xe tafi tace aa Abba ae ko zanyi fushi da kowa baxanyi da Abbana ba kawae na sha'afa ne yace toh muje na kaeki school din cikin jin dadi ta jin jina Mai Kae, hannunta ya rike Suka fice har suka isa school din suna fira yana jaddada mata cewa data gama exams dinta ta sanar dashi xexo har nan yaga sirikin nashi murmushin jin dadi kawae take yi kafin ta fito daga motar tana Mae godiya da addu'ar Allah yatsare tana daga mishi hannu har ya bace ma ganinta lumshe idonta tayi ta bude tare da sauke ajiyar zuciya kafin ta nufi cikin school din" Karfe 12:00 Suka fito daga exam hall din ita da summayya rike da hannun juna suka nufi cafeteria suka siyo snacks kafin suka nufi main class dinsu suka zauna, kallonta summy tayi tace muhibbah Lafiya naga idonki duk sun kun bura alamar kinyi kuka, ajiyar zuciya tasauke kamar zatayi kuka tace kedae bari summy jiya saura kadan na mutum saboda bakin ciki wae ya Fu'ad za'a auramun *soyayyar kwana daya* naso tajawomun masifa nan ta kwashe duk abinda ya faru daren jiya ta Bata labari dariya ta dingamata tana tsokanarta meyasa kikace bakya son shi da munje land of beauty munsha fura da nono, hade rae tayi tace to ae ko yanxu ma zaki iya zuwa dariya tayi sosae kafin tace Allah ya huci zuciyar Amaryar Mukhtar murmushi me sauti tayi tace yauwa ko kefa yanxu naji magana, wayarta ce ta hau ringing wani kayataccen murmushi ta saki ganin sunan dake yawo akan screen din wayan *My king* "Kara wayan tayi a kunnenta cikin sanyin murya tace Amincin Allah su tabbata ga Angon Fateema xahrah, Ameen tareda matar Mukhtar Kara fadada murmushinta tayi tace Ina fatan kana Lafiya sororo summy tayi tana kallon yadda take waya cikin nutsuwa tana sakin murmushi alamun kalaman da yake mata suna shigarta, seda tagama wayar kafin sukayi sallah Suka Dan duba kadan kafin suka shiga hall din" Se karfe 5:00pm ta koma gida a gajiye likis bakinta dauke da sallama ta shiga parlourn turus tayi ganinshi zaune kan kujera suna fira da mummy, hade rae tayi takarasa shiga ciki kamar zatayi kuka............[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Dedicated to my lovely brother* *Nasadaukar da ragowar pages din nan xuwa ga my yaya Abban Fateema Kuma angon Fateema har gaban gobe ana kyawun tare* *Page 9* Xaunawa tayi gaf da Mummy kafin tace Mummy Abba fa ya fasa tafiyan ne? Murmushi tayi saboda ta fahimce abinda yasata hada rae kamar Wanda aka aeko ma mutuwa batace Mata komae, ba munyi sallama dashi ba daxu ko fasa tafiyar yayi tayi maganar cikin xakuwa da jin amsar da mummy xata bata "Ya tafi" tafada Kae tsaye "Toh shi wannan fa baxe tafi bane? Tafada tana nunashi da yatsa wani kallo dayamata ne yasata saurin sauke hannunta tana kauda kanta daga kallonshi, bata ankaraba taji mummy ta bige mata baki dafa bakinta tayi da sauri hawaye na bin kuncinta" Yaushe Kika koma haka shi sa'an kine? Wllhi xan Saba miki ki fita idona Da gudu ta nufi bedroom dinta tafada kan bed ta fashe da kuka Seda tayi me isanta kafin ta tashi ta shige toilet tasakarma kanta ruwa tajima a toilet din kafin ta fito ta shirya cikin bakar Abaya taji stones masu walwali kamar wuta, pray mat ta shinfida ta gabatar da sallahn magrib tana xaune tana axkar har aka kira isha'i seda tayi sallah kafin ta nade pray mat din ta xare hijjab din jikinta ta xaune gefen bed tayi ta gumi seda taji yunwa ta dameta kafin ta nufi parlourn Suna xaune a parlour ta karasa ta gaeda daddy tana Mae Sannu da dawowa amsawa yayi sama sama saboda har yanxu ranshi a bace yake a kanta yaga idan ba haka yamata ba baxata fahimce kuskurentaba dining ta wuce ta xauna ta xuba abincin jallof din taliya ce data sha naman rago tasa fork ta soma ci Anas ne ya karaso yaja kujera kusa da ita ya xauna seda ya kalleta kamar baxe ce komae ba kafin Kuma yace wae waya tabamana ke ne naga idonki ya kumbura alaman kinyi kuka kedae kuka baya Miki wuya, rau rau tayi da Ido xatayi kuka yace sorry dear sister fadamun waya tabamun ke hawayen daya xubo Mata ta goge tace ba mummy bace ta buge min baki yanxu gaba daya saboda ya Fu'ad su daddy sun dena Sona girgixamata Kae yayi yace ba haka bane kiyi hakuri uhmmm? lallashinta yashiga yi seda yatabbatar ta hakura kafin ya nufi friedge ya dauko Mata ruwan sanyi ya xuba mata a cup ya mikamata duk abinda sukeyi mummy na kalansu girgixa Kae kawae tayi a xuciyarta tana mamakin halinsu su abin fada baya musu wuya indae xasu xauna inuwa daya se anjisu amma kuma indae daya yashiga damuwa hankalin daya baya taba kwanciya Kuma indae sukayi sirri xasu binne abinsu babu me ji Bayan ta kammala cin abincin ta tattare dining tayi musu sallama ta wuce bedroom dinta ta shiga toilet ta dauro alwala tayi duk wani dabi'a da takeyi kafin ta kwanta tareda karanto addu'ar bacci taja blanket ta rufe har kanta bacci ya dauketa "Bangaren Fu'ad kuwa Abba da yayi Mae maganan komawa gida yace yatafi kawae xe Kara 1 week xasu dinga su company suna ragema daddy aeki shida Suhael be hanashi ba yatafi abinshi" Bata fito ba se 9:13am kasancewar yau Saturday babu school gaesheda mutanen gidan tayi babu Wanda ya fita suna enjoying weekend dinsu a gida ganin Bata ga mummy parlourn ba yasata nufar kitchen can ta isketa tana hada breakfast gaesheta tayi kafin ta taemakamata suka cigaba da girkin, mummy wae yaushe mama jumae xata dawo ne aekin Nan yanamiki yawa ke kadae ko xa'a samo wata house made din ne? Tayi maganar cikin sigar tambaya, Aa muhibbah bansan wacce xan dauko ba gara jummae nasan halinta tunda mun dade tare nakirata tacemun in Sha Allah nanda 2 weeks xata dawo ajiyar zuciya tayi tace Tom shikenan Allah yadawo da ita Lafiya, amsawa tayi da Ameeen Yauwa mummy Dan Allah Ina so xanje gidan su Rufaeda anjima mamanta batada Lafiya, Tom shikenan Allah ya kaemu Kafin 10 sungama shirya dining din ita ta tattare