Sashe 11
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallon Fu'ad tace "ya Fu'ad ga ya mukhtar" ta fada tana sakin murmushi. Cije lips dinshi na kasa yayi ya furzar da wata iska me zafi daga bakinshi, lallai muhibbah wuyarta ta isa yanka ko darr batajiba ta tsaya tana introducing dinshi ga wani a gabanshi, batareda taji ko shakkanshi ba hmmm! Yasauke ajiyar zuciya. Mukhtar yakara bashi hannu suka gaisa sosai, Fu'ad ya tafi yabarsu nan a tsaye. Ai Aisha tuni tashige ciki gudun taji an kwadamata Mari. Seda fu'ad ya wuce kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, dan duk abinda takeyi a tsorace take duk da tana da goyon bayan Abba tunda shi yace ta turomai mukhtar din su tattauna. "Uhmmmm! Wae ni banma tambayeka ba wayama kwatancen gidan nan". Girgiza Kai yayi yace "zuciyata mana" dariya tayi sosai tace "uhmmm! Aa fa banyarda ba Kai dai fada gaskiya ga goma". Murmushi yayi har hakoranshi suka bayyana kafin yace "namiki karya kenan" "wace niii na isaaa?" Tafada tana zaro ido. Seda suka gama shirmensu tace "muje ko" babu musu tayi gaba yabi bayanta har parlourn baki, Fu'ad na kallansu aiko suna hada ido dashi ta sakarmai murmushi tana kanne mai ido Daya. Murmushin gefen baki yayi ya girgiza Kai alaman zaki sani. Gurin zama ta nuna Mai ya samu guri a Daya daga cikin kujerun parlourn yazauna, takawo Mai ruwa da abinci amma fir yaki ci yace ya koshi dole ta hakura tace "toh bari na kawoma snacks" snacks ta kawo mai da drink Shima daker ya dan tsakura. "Yanzu fa saura watanni kadan kizama mallakina ko my Zahra". Hannu tasa ta rufe fuska wai ita kunya tace "in Sha Allah ya mukhy". Sun dade suna fira kafin yace mata yana zuwa, aiko yana fita ta dauki wayarshi daya ajiye kan kujera tadanyi danne danne ta maidata idan tadauketa kana ta Koma tazauna, tana nan zaune yadawo hannunshi rike da wata 'yar karamar bag me bala'in kyau. Yace "close your eyes" rufe idon tayi gam, ya ciro wani box dan dai dai anyi decoration dinshi, bude box din yayi kafin yace open your eyes. A hankali take bude idon har ta budeshi gaba Daya ai ko idanunta suka sauka akan wata hadadiyar sarkar gold dake cikin box din, hannunta har rawa yake ta ciro sarkar tana kare mata kallo, sarkar tasha ado se walkiya take. Hannu ta Kai taciro dan kunne ta kara a kunnenta suka saki murmushi gaba dayansu, takara Kai hannu taciro abin hannu tako zira tana jujjuya hannunta yace "wow kinga yadda kika has Kashi you look so beautiful". "Lallaima shalele bama shi ya haskani ba ni na haskashi ko?". "Ai bashida kyawun daze haskaki sedai ke ki haskashi" "dariya kawai tayi tanajin kaunarshi nakara mamaye zuciyarta dama gangan jikinta baki daya ba tace Mai komai ba idan da sabo tasaba da Jin abinda yafi hakama a bakin ya mukhy. Wani box yakara cirowa ya mika mata tana budewa taga sabuwar waya dal i phone 13 pro, tsallan murna tayi tace "Thank you Hayateee" shiiii ya Dora yatsanshi a lips dinshi yace "it's my pleasure, you deserve more". "I luv you with all my heart Hayateee". "Luvs you too my one". "Fadin irin son da nake miki ma bata lokaci ne, Baki yayi kadan wajen zayyana miki irin tarin kaunar da nake miki habeebtee". Gyaran murya Abba yayi, tayi saurin mikewa tana kasa da Kai tace "sannu da fitowa Abba". "Yauwa maamana". Fakan idon Abba tayi ta dubi mukhtar tayi tamai alama da hannu se sunyi waya, ta fice tayi cikin babban parlour inda take jiyo hayaniyar mutane. Shi kanshi Abba yadda yagansu seda yaji jikinshi yayi sanyi. Bata tsaya a parlourn ba sannu kawai tamusu tayi bedroom Aisha tabita. "Muhibbah kinga yadda jikina yake rawa kuwa gaba daya nayi tinanin kashin mu ya bushe a hannun ya Fu'ad, nayi mamaki da naga be mana komai ba". Dariya tayi sosai tace "Matsoraciya kawai toh ai Abba ne yasa nakirashi Nima da wani ganganci zesa in kirashi, nacema Abba ya Fu'ad dukana zeyi idan yaganshi yace kar nadamu baze mun komai ba, ina kyautata zaton Abba ya Mai magana, Amma ai da yanzu jikinmu ya dau dumi". Ta karashe maganan tana sakin dariya, itama Aisha dariyar tasa. Kasa ya zamo ya gaishar da Abba cikin girmamawa, amsawa yayi cikin kulawa kafin yace yatashi yakoma kan kujerar, daker ya koma ya zauna. Abba ya dubeshi cikin kulawa yafara magana "Wai ke muhibbah yanzu aure zakiyi? School dinfa?". Harara ta watsamata tace "toh uwata shakeni in fada miki kike jeromun tambayoyi". "Dan Allah mu bar batun wasa ki amsamun". "Hmmm! Aisha kenan, kinfi kowa sani a tsarina babu batun aure yanzu, bantaba tinanin soyayya zata iya canzamun tinani cikin sauki haka ba har na amince zanyi aure ba tareda nagama school dina ba, Amma ina son mukhtar fiye da yadda nake son kaina babu abinda bazan iya yi saboda Shiba, duk abinda ya tambayeni zanyi Mai shi indai be sabama shari'a ba". "Eyyeeee muhibbah gaskiya kin fada da yawa, irin wannan zazzafar kauna, amma fa babu karya kun dace da juna babu laifi gayen ya hadu Kuma ya iya daukar wanka, Allah ya kaimu musha biki". Murmushin ta tafadada tace "Amiin esherty, thank you". Box din farko ta bude mata tafara nuna mata sarka da abin hannu, sannan ta bude dayan box din ta ciro wayan. Kara mata sarkar tayi a wuyanta tace "Wow kinganki kuwa muhibbah kin hadu, saura haduwarki da Allah". Suka sa dariya, suna fira amma rabin hankalinta na waje tana lekar compound din ta window, tana jira taga fitowar mukhtar, shiru shiru be fito ba ta koma ta zauna kamar an tsunguleta takara mikewa leka window din dazatayi ta hango fitowarshi a alamunshi babu walwala ya shiga motarshi yayimata key ya fice daga gidan a guje. Wayanshi tashiga kira ba'ayi picking ba tayi mai missed call yafi 10 ba'ayi picking ba tana kara dialing numbern taji switch off. Take jikinta yabata ba lafiya ba, duk yadda akayi wani Abu mara kyau yana faruwa tun data baroshi a parlour shida Abba gabanta ke faduwa har lokacin dataga ya fito take taji zuciyarta to tsananta bugawa da sauri sauri. Gudu yake a kan titi Yana addu'ar Allah ya kaishi gida lafiya, tun yana iya kallon hanya har yasoma gani dishi dishi aiko seji kake kiiiiii karar hadduwar motoci.......... *Ya ilahi meke Shirin faruwa da masoyan nan biyu? Allah yasa Muji alkhaeri* *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION* *Page 20* Allah ne ya kare daba karamin accident zasuyi ba, gangarawa gefen titi yayi ya kifa kanshi a stiring motan yana kokarin daidaita nutsuwarshi, ajiyar zuciya yake ta saukewa ajere ajere. A hankali yakoma kan titin yacigaba da driving dinshi yana karanto duk wasu addu'o'i da suka zo bakinshi, da taimakon Allah ya isa gidan, daker yayi parking ko key din be cire ba yabarshi jikin motan ya nufa cikin parlour da sassarfa. A kan Daya daga cikin kujerun parlourn ya fada, ya dafe goshinshi yana jujjuya Kai, a razane umma ta mike ta nufeshi tana tambayarshi abinda ke damunshi, tun shigowarshi yanayinshi ya nuna ba lafiya ba, dan da alama ma besan tana zaune a parlourn ba. Yakasa magana saitin zuciyarshi yashiga nunamata yana cigaba da jujjuya Kai. Cikin tashin hankali tace "bangane ba mukhtar me yake damunka? meyasamu zuciyar taka? Dan Allah kayimun magana" daker ya iya cemata Muhibbah ce.. kafin yakarasa se aman jini, rungumoshi jikinta tayi tasa kuka tana furta innalillahi wa inna ilaehi raji'un, meyasamu muhibbahn? Shiru babu amsa, ji tayi jikinshi ya saki baya iya kwakkwaran motsi kuma har lokacin jini be dena fita ta daga bakinshi ba Aiko hankalinta yayi mugun tashi. Wayarta ta dauko daker ta duba numbern Abbansu ringing Daya ya daga tace "Mukhtar babu lafiya aman jini yakeyi" dasauri ya mike daga zaunen da yake a office yace "what? Meya sameshi kuna wane asibitin?". "Bamu tafi ba da wai ko za'a kira family doctor" "wane magana kike" yayi magana cikin daga murya. "Maza Maza a kaishi al_muneef specialist hospital, ganinan zuwa". Be jira amsarta ba ya katse Kiran yana tattare files din dake Saman desk din. Da sauri ta fita takira me gadi da driver suka taimaka akasa shi a mota itama ta zagaya tashiga ta rungumoshi ta fashe da kuka. Ko kafin su isa asibitin Abba yakira family doctor dinsu ya sanar mishi da zuwansu, tun kafin su isa an tanada komai, ai ko suna isa aka daukeshi a keken marasa lafiya akayi emergency room dashi, umma tabisu, wani doctor yace "please maa ba'a shiga ki dan jiramu daga waje". Safa da Marwa take takasa zaune takasa tsaye a haka Abba yazo ya sameta "ina mukhtar din yake?" Cikin muryan kuka tace "anshiga da emergency room". "Meyasa meshi haka? Meke damunshi" ya jero mata tambaya. "Nima bansaniba Alhaji natambayeshi se zuciyarshi kawai yake nunamun daker ya buda baki yacemun muhibbah ce, daga nan be Kuma cewa komai ba se aman jini". Jinjjina Kai yayi batare da yakara furta komai ba. Seda doctors suka kwashe 3 hours suna abu Daya, da taimakon Allah suka ceto rayuwarshi. Gunguroshi akayi a keken marasa lafiya, su Abba suka bi bayan doctors din zuwa special room, har aka kwantar dashi kan bed be ko motsa yatsanshi ba yana kwance kamar matacce, umma tashiga rera sabon kuka tana ambaton ubangiji, Abba na faman lallashinta yana karfafa mata gwiwa Shima din dauriya kawai yakeyi. Umma ta dumi doctorn daketa dura allurai cikin ruwa tace "doctor kaga fa baya motsi kafadamana idan ya mutu ne" tafada tana cigaba da kukanta Yace "be mutu ba hajiya idan kika taba hannunshi jijjiya na motsi, haka zalika idan kika taba zuciyarshi zakiji tana bugawa, yanzu bacci yake saboda alluran da akayi Mai masu karfi ne amma in Sha Allah yana farkawa ze tashi normal". "Allah yasa haka likita" suka amsa da "Ameen" har Abba. Likitane yace Abba yasa meshi a office, ya dube umma yace karki fadama kowa ki daga musu hankali kinga dare yasoma yi kibarsu har zuwa safiya idan Allah ya kaimu, jinjina Kai tayi tana sharar kwalla, shikuma ya nufa office din doctor. Zaune yake gaban doctor yana Mai bayani, yace "Alhaji gaskiya