Sashe 56
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daya karayi a kirjinshi kamar za'a kwace mai ita, a haka bacci ya dauketa. Shikuma ya tsuramata idanu yana kare mata kallo har bacci yayi gaba dashi. wajen 5 na asuba cikin baccinshi yaji nishinta. A hankali ya bude idanunshi ya sauke su a kanta, bacci takeyi amma se nishin zazzabi take ga jikinta yayi zafi rau kamar wuta. Cikin kidima ya sauka daga gadon ya dauko allura iya kan paracetamol da atimeter yaja a siringe. ya haura gadon ya janyota jikinshi yana shafa fuskanta hade da huramata iskan bakinshi. A hankali ta fara bude ido har ta sauke shi cikin nashi. Yasakar mata murmushi batareda yayi magana ba, ya juyata yamata alluran. da mamakinshi batayi korafi ba yadda tasaba idan zemata allura se ranshi ya baci kana take tsayawa amma yau ko tari batayi ba. Seda ya rungumeta kan yaga hawaye na silalowa daga idanunta. Yasa hannu yana share mata, Hade da bubbuga bayanta. yana nan zaune manne da ita har ta koma bacci kan ya kwantar da ita yaja blanket ya rufeta shikuma ya sauka ya nufi toilet. Alwala ya dauro ko masallaci be iya fita ba ya shinfida pray mat yayi sallah yadawo ya zauna gefenta. Se 8 yaje kitchen yasama musu breakfast, Koda ya dawo dakin yasamu har tayo wanka tazo ta tada sallah. Shima wankan yaje yayi kan ya fito har ta fice daga dakin. Shiryawa yayi cikin white shirt da bakin jeans, ya feshe jikinshi da turare ya nufi dakinta. Shirye take cikin doguwar rigan material tasa hula ta dan jata baya kwantacen gashinta ya bayyana, suna hada ido yasakar mata murmushi itama murmushin tayi kana tace "Good morning my heart". "Morning Angel of my life" yafada yana karasawa ya riko hannunta. "Ya Jikin ki?". "Na war ware" "uhmm nima sheda ne, dan gashinan kinsha kyau abinki" yayi maganan yana pecking goshinta. Murmushi tayi tana rufe fuska. "Dagaske fa kinyi kyau" Yafada yana kureta da ido ganin yadda takara haske har tana kashe ido. Murmushi ta danyi kan tace, "Dan saurayi! Ya akayi ne? Karka hadiye ni mana" tayi maganan da zolaya. Murmushi me sauti yayi "Wankan naki ne ya tafi dani". Dariya tayi har hakwaranta na bayyana, tace, "Kai kam baka rabo da zolaya". Kamo ta yayi ya tsayar da ita gaban mirror, ya manne bayanta da kirjinshi "ke kyakkyawa ce ajin farko, ki Kalli kanki da kyau a madubin nan zaki tabbatar da abinda nake fada miki. Ko dawisu bazata nunamiki ado ba, duk wata mace idan baki ne take amsa sunanta mace amma dakin doso dole su ja da baya". Juyowa tayi ta rungumeshi tana dariya tace, "Hearty muje please yunwa nakeji" tafada tana shafa cikinta da takeji kamar an yashemata 'yan hanji. Lakace hancinta yayi, "Ba dole kiji yunwa ba, jiyafa da yunwa kika kwana blood". Yana kai nan yayi sama da ita ya fice. Kan rough center carpet din dake parlourn ya ajiyeta ya nufi kitchen ya dauko tray, yadawo dining yashirya breakfast din kan tray din ya nufo parlourn. Zama yayi ya dauki plate yayi serving dinsu tareda janyota jikinshi yamata masauki akan kafafunshi. Abincin yashiga bata tanaci, shima yana ci, babu laifi kam taci sosai. Kan kujera ya dorata ya tattare kayan ya kai kitchen, gefenta ya zauna ya kwanto da kanta kan cinyar shi yashiga shafa gashin ta. "Bloody! Ya kike Jin jikin ki yanzu?" "Naji sauki". "Zazzabin fa?" Yayi maganan yana kallon kwayar idanunta yana so yatabbatar da abinda yake zargi. "Dama na fadama dadare ne zazzabin ke rufeni amma da safiya tayi seka nemeshi ka rasa" tayi maganan tana kai hannunta tana shafo sajenshi zuwa gemun shi. "Jeki ki dauko hijjab mu tafi asibiti" make kafada tayi tace, "Yaya kabarshi kawai base munje ba nasan malaria ce ma, bakina gaba daya babu taste. Hancinta yaja "toh doctor Fatee". Dariya tayi tana kokarin yin magana taji amai na taso mata, ta mike da gudu ta shiga wani daki a down stairs, tafada toilet tashiga Kwara amai. Da hanzari ya mara mata baya ya riketa har tagama aman, ya wanke mata baki da fuska kan ya dubeta, "Sorry dear, ki jirani Ina zuwa". Kai kawai ta gyada, ya fice. Be jima ba yadawo toilet din ya mikamata PT, tsayawa tayi tana kallonshi dan batasan amfaninshi ba. "Yimun fitsari akai". Ba musu ta tsugunna tayi fitsarin, tayi tsarki ta mike yana tsaye yana kallonta. Mikamishi tayi yasa hannu ya karba, befi 30 seconds ba yaga 2 lines sun fito rada rada jajir, ya dan zaro idanu yayi murmushi har fararen hakoranshi na bayyana. "Yaya meyafaru? Me kagani a fitsarin nawa? Malaria ce ko? Dama nafadamaka ba wani abu bane malaria ce, lokacin ina KD na taba irin ciwon kullum da dare zazzabi kamar zan mutu, amma gari na wayewa ze sauka kamar aljani sedai mummy take kwana dani Kuma doctor yace ba wani abu bane malaria ne". Murmushi mara sauti yayi, bece mata komai ba ya dauko Dettol ya wanke musu hannuwa, ya daukota suka dawo parlour. Ajiyeta yayi tanata maida numfashi tanajin Jiri na dibanta. Hijjab yaje ya daukomata ya ziramata suka fice rike da hannunta, ya bude mata mota ta shiga ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja motan suka fice daga gidan. Cikin asibitin yayi parking ya fito, ya bude mata ya rikota tareda mannota da jikinshi suka nufo ciki anata miko gaisuwa sedai ya gyada musu Kai. Lab ya nufa da ita, yasamu doctor fareeda na zaman jiran su dan tun kan su tawo ya kirata. Gaisheshi tayi ya amsa cikin kulawa dan babu wacce yake kulawa tun daga kan doctors din har zuwa nurses kamar ita, saboda tasan aikinta kuma tasu tazo daya kowa shakkar yi mai magana yake, ita kadai ke iya fuskantarshi su tattauna kan abinda taga ya dace a gyara kuma ya saurareta. Zama yayi yamata masauki kan kafafunshi, ta karaso taja kujera tazauna kusa da su ta riko hannun Muhibbah. Ina kwana doctor "Lafiya kalau madam, ya jiki?" "Alhamdulillah". "Fatan dai kin dena tsoron allura?" tayi maganan tana murmushi dan sarai ta gane itace wacce tasama drip kwanaki. wajen yin allura suka dinga drama, kwanaki kuma taji anata cewa matar boss ce gashi kam ta tabbatar tunda gata kan cinyar shi dare dare, duk da dah tayi tinanin ko kanwarshi ce saboda kaman data ga suna yi. Murmushi tayi, shi Kuma hankalinshi na kan waya yana duba abu. Jin tsinin allurar a fatan ta tun bata shige ba tayi saurin janye hannunta tana hawaye. "Madam haka zamuyi dake?, doctor inaga seka dan rike mun hannun ta" tayi maganan cikin kulawa. Wayarshi ya ajiye a gefe, ya rike hannunta ta binne kanta a kirjinshi tana kuka har aka gama diban jinin. Mikewa yayi ya rike hannunta yace "Doctor ina jiran results din office" "in Sha Allah sir". Office dinshi suka nufa ya kwantar da ita kan kujera. "Yaya! na baro wayata gida nasan Aesha zata zo yimun sannu da dawowa ka kirata please karta je bana nan. Bece komai ba ya zaro wayan yashiga dialing numbern Aeshan. "Assalamualaikum! Ina kwana Yaya" tafada a hankali dan ji take kamar yana gabanta. "Kina ina yanzu?" "Ina gida yanzu dai zan tafi gurin Muhibbah". "Okay ki biyo asibiti ku tafi tare" yana kai nan ya ajiye wayan. Karasa shiryawa tayi ta fito, a parlour tasamu ummi "Ummi bari naje, Yaya ya kirani yace nabiya ta asibiti mu tafi da Muhibbah gidanta" "Asibiti kuma? Lafiya dai ko?". "Nima Ummi bansaniba, abinda yace mun kena n ya kashe wayan". "Toh A dawo lafiya". Asibitin ta biya ta nufi office dinshi tayi knocking, ita ko duk an santa tunda ko ciwo suke asibitin suke zuwa. Izinin shigowa ya bata ta murda handle din ta kutsa kai. Gaishe shi ta kumayi ya amsa. "Riketa da kyau ku karasa mota, ina driver ya kawoki?" "Eh Yaya tare muke dashi". "Okay ki sama mata abunda zataci idan kunje, yau ma kijata kushiga kitchen tare idan kinga dama kiga yadda zamuyi dake". Kai kawai ta gyada, gaba daya ta kosa su fice daga office din. Taimakamata tayi ta tashi zaune "Hearty?" "bloody" yafada yana kallonta. Hannunta biyu ta hada ta sumbata ta hura alamun kiss din iya isa gurinshi. Murmushi yayi shima yamata yadda tayi tasa dariya, ta rike hannun Aesha suka fice ta juyo tana mishi bye bye. Suna isa ta zube kan kujera Jiri take ji yana diban ta ga yunwan dake kwakular ta. "Maman un born baby! Me zakici ne?" Harararta tayi, "Kya gama abunki ki kyaleni malaria ce ba wani abu ba, in sha Allah bazan ga ciki yanzu ba kidena mun fata Idan ba haka ba ajimu dake". "An dade ba'a jimu ba, dama yau aka fara jinmu ne? Nidai fadamun abinda zakici dan yanzu zakiji Kiran yaya, na shiga uku". "Fate" waro ido tayi "Fate Kuma? Gaskiya ki canza wani abun". "Toh shi nake so" Zatayi magana taji ana danna door bell, mikewa tayi taje ta bude, ganin mairo yasa tayi murmushi "Allah ya taimake ki, ga Aunty mairo nan dan bazan iya wani fate ba". "Wa ke son fate?" Ta fada tana shigowa parlourn. "Muhibbah ce bata da lafiya shine tarasa abinda zataci se fate" Murmushi tayi "Kibarta idan bashi ta samu ba bazata iya cin komai ba". Hijjab ta zare ta nufa kitchen, Bata samu tsaki ba ta diba shinkafa tasa a blender ta nika. Batafi 30 minutes ba ta kammala faten ta zubo a kula ta kawo musu parlour ta ajiye. Plate Aesha ta dauko ta zuba mata se taga ya birgeta itama ta dauki plate ta zuba ta fara Sha. Lumshe ido tayi "kai gaskiya faten nan yayi dadi". Har ta shanye amma Muhibbah na zaune ta tasa shi gaba tana kallo. "Sister kisha mana kinga harma yayi sanyi" Daker ta Kai chokali daya baki, ta yatsina fuska tana ture plate din gefe "Sister bazan iya Sha ba, idan nasha zan i amai zanyi. Ki dafamun indomie please kisa yaji sosai". Da mamaki take kallonta "kisa a dafa abu yanzu Kuma kice bazaki sha ba tsakani da Allah" Mairo dake gyaran parlourn tace "Aesha kimata uzuri mana ko kinga dah tanayin haka ne?" Girgiza kai tayi, ta mike tashiga kitchen. Hannunta rike da plate din indomie ta fito tazo