Sashe 41
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *Page 44* Tana ajiye wayan tayi wani uban tsalle ta rungume Rumaisa "Sister yau rana daya Dr Fu'ad ya saurareni, shekara nawa ina binshi babu irin rokon da banyi mai ba ko sau daya yazo inda nake amma yaki gashi yau shi yake cewa na turami address dina nakasa yarda mafarki ne ko gaske" takarasa maganan tana fadawa gadon cike da farin ciki "Dama Aunty zee bana fadamiki ba don't give up, addu'a babu abinda ta bari gashi yanzu kin fara ganin haske" "Wllhi nayarda Allah maji rokon bayinsa ne, haka nake faman tsayuwan dare akan bawan Allahn nan amma sena mishi 20 missed calls beyi picking ba sena jera 1 month ina Kiran wayanshi befi yayi picking sau daya ba, har asibiti nakan je a hanani shiga office dinshi se an sanar mai da nice wani lokacin yace kar abarni shiga wani lokacin Kuma yace nashiga amma Kona shiga daga amsa gaisuwata baya kara cewa uffan har nagama surutuna na karaci zamana na tashi, addu'ar nake amma kullum jiya I yau har na soma gajiya ashe ubangiji na sane dani" "Sedai abinda yaso ya kashemun guiwa wai yanada aure, Kuma ni bantaba Jin labarin aurenshi ba ko a social media ban taba ganin ya dora ba" takarashe maganan kamar zata saki kuka. "Dama haka Allah ke lamarinshi addu'a bata fadi kasa banza wani lokacin Allah yana jinkirtamana kafin ya amsa wani lokacin Kuma da munyi a take ze amsa mana wani lokacin ma se ya hanamu abinda muke roka ya canzamana da mafi alkhaeri, Toh Aunty zee ma banda abinki menene dan yanada mata kedai ba burinki ki mallakeshi ba gashi kuma kin fara dauko hanyan samun matsuguni a zuciyarshi ki maida hankali wajen ganin yazama mallakin ki, bare ma nafi tinanin kawai yafada ne yaji abinda zakice amma bashida wata matar". "Rumaisa kenan bakisan yadda nake kaunar gayen nan bane, ina mugun kishin shi fiye da tinaninki ni kaina ina mamakin kaina, fatana dai Allah yasa abinda ya fadamun ba gaskiya bane" "Kema Aunty ki bar maganan wata matarshi kiyi focusing akan yadda zaki sace zuciyarshi koda yana da matar kisan yadda za'ayi yaji kece on top azuciyarshi, kawo kunnenki kiji" Kasa kasa tayi mata magana, hannu tabata suka tafa "Kai kanwata kanki naja, Gobe akwai cire wanka" "Toh idan Abba ya ganshi fa ya zakiyi?" "Ni ai zanso ma suyi 4 eyes da Abba ayita ta kare" "Kai Aunty zeeee ke Kam bakida dama" tafawa sukayi suna kwashewa da dariya. *************** Runtse idanunta tayi tana jira kawai tajita a kasa, Jin tafada kirjinshi yasa ta saurin bude idanu karaf suka fada cikin kwayan idanunshi, kallonshi tayi na seconds kan ta kawar da kanta zuciyarta na tsalle a tsorace tace "I'm sorry wllhi bansaniba ne cup din ya fadi ya fashe, Allah yasama ruwan zafin be zubanma a jiki ba" Murmushi ya danyi "Duk kishin ne haka matar Yaya?" Dasauri ta juyo ta kalleshi gabanta na faduwa Jin yakira ta da matar Yaya, kar dai dama yanajin sunan da su Aesha ke kiranta dashi. "Kishi Kuma mezanyi ma kishi?" "Ga kishi nan ya bayyana karara a kwayar idanunki, budurwata kike kishi?" Kuka me sauti ta saki tana kokarin raba jikinta danashi, kara kamkameta yayi yadda bazata iya kwacewa ba "Wayyo Allah mummy na kafata zata cire na shiga ukuna innalillahi wa inna ilaehi raji'un......" Kuka take sosai kamar wacce aka cire ma kafar gaba daya. Dariya taso bashi ya waske shidai yasan wannan kukan ba iya na jin zafin ciwo bane. Kacho Kam ya dagata ya nufa bedroom dinshi da ita, a bakin bed ya ajiyeta ya juya ya fice Fasashen glass din ya tattare ya zuba a dust bin ya goge jinin gurin kana ya dauki first aid box ya haura dakinshi. Har lokacin kuka take ya karasa ganganta yasa guiwowinshi a kasa ya Kamo kafan ya dora akan cinyarshi yafara yimata dressing Jin ya dangwali spirit a jikin cotton yafara gogemata ciwon takwallara kara tanayin baya baya ta kwanta kan gadon Rike kafar yayi Kam tana kuka amma yaki sakinta har seda ya gama yimata dressing din. A hankali ya sauke kafara kasa "Raguwa kawai" ya fada yana daukar box din ya fice. Kitchen ya maida box din ya dawo, gefenta ya kwanta yasa hannu ya dan ja hancinta "Wai duk wannan kishin na miye daga Jin ina waya da matar da zan aura kika rude kika saki cup ya fashe gashi har kinjima kanki ciwo" saurin bude idanunta da suke a lumshe tayi Jin yace tana kishi, Rai a bace tafara magana "Toh ni meze sa nayi kishi, ina ruwana da budurwarka" iya gaskiyarta take fadan ita ba kishin da takeyi akan mema zatayi kishin shi. Janyota jikinshi yayi ya rungumeta tsam ya Kai bakinshi saitin kunnenta "Nidai nafada miki ki rage wannan kishin naki dan soon zan kawo miki abokiyar zama, stress namiki yawa ga school ga girki ga kula dani ai seki rame kisa Ummin ki tace bana kula dake yadda yakamata, kinga idan na kawo miki abokiyar zama zaki dinga hutawa na kwana biyu, ko ya kika ce" ya Kai karshen maganan yana dage mata gira daya. Kokarin mikewa ta fara yakara matseta sosai a jikinshi. "Ina zaki haka kike Shirin mikewa?" "Ni kasakeni na tafi daki bacci nakeji" Tafada kwalar dake kwance a idanunta na silalowa. "Nan a daji kike?" "Ni dakina nake so ka maidani" "Uhmmm uhmmm nikuma a dakina nake so ki kwana" yayi maganan yana kwaikwayonta. Kuka ta shiga rera mai ya birkitata tadawo tana kallan ceiling yamata runfa da faffadan kirjinshi, tsoranta ne ya ninku zuciyarta na tsittsinkewa tashiga girgiza mai kai ta bude baki zata fara rokonshi ya hade bakinsu a zafafe ya fara kissing dinta yana yawo da hannunshi a jikinta ya mutsa gashin kanta yashigayi ita ko se kokarin kwacewa take. Dayan hannunshi yasa yarike kugunta ya fara shafa daga wuyanta zuwa hannayenta lumshe idonta tayi hawaye na gangarowa Jin canjin feeling ajikinta yasa tasa hannayenta ta rungumeshi. Seda ya kashe mata jiki kan ya mirgina ya kwanta gefenta tareda janyota yayi tighting dinta a Kan kirjinshi yana maida numfashi a hankali basu motsa daga gurin ba har bacci yayi awan gaba dasu. Shi ya fara farkawa ya kai hannu ya janyo wayarshi yaga 5:00am a hankali ya janyeta daga jikinshi ya kwantar da ita kan pillow ya nufa toilet yayi wanka tare da dauro alwala ya fito ya shinfida pray mat ya zauna yayi karatun alqur'an na 15 minutes kan ya mike yayi raka'atanil fajr. Kusa da ita ya karasa ya duka ya hura mata iska a fuska a hankali ta fara bude ido tasauke su kan fuskarshi kallonta yayi na seconds kan ya fice Jin an fara Kiran sallah Mikewa tayi dasauri ta koma ta zauna tana cije lip saboda azabar data ratsata. Har yadawo masallaci tana zaune dafe da kanta "kinyi sallahn?" Kamar jira take yayi magana tasaki kuka "Wayyo Allah kafana zata cire na shiga ukuna" "Wai ke bakya gaji da kuka ne" Bata tankashi ba se tashiga uku take maimaitawa. Daukarta yayi ya direta cikin toilet din yafito yaja mata kofa, lallabawa tayi ta dauro alwala "Ya...ya..." Ta kirashi a dan tsorace gudun yayi fada Jikin kofar toilet din ya tsaya "Meyafaru" "Nagama alwalan" tura kofan yayi ya shiga ya daukota akan sallaya ya ajiyeta ya nufa dakinta ya dauko mata hijjab A zaune tayi sallahn tana idarwa ko azkar bata gama ba ta bingire kan sallayan tafara bacci. Karasawa yayi ya dauketa ya dorata kan gado ya kwanta kusa da ita yana kare mata kallo girgiza Kai yayi ganin hawaye duk sun bushe a fuskanta, ita dai bata gajiya da kuka Shima a haka bacci ya daukeshi. Se 10 minutes to 8 ya farka ya ziro kafafunshi kasa ya zira slippers ya fice daga dakin Kitchen ya nufa yafara hada breakfast jinshi yake wani kala se faman jan tsaki yake baze tina when last yashiga kitchen da sunan kirki ba Jin ana danna door bell ya je ya bude kofan mairo ya gani tsaye tana murmushi ganinshi yasa tayi saurin yin kasa da kai duk a tinaninta Muhibbah ce. Matsawa yayi ta shigo "Ina kwana" "lafiya" yafada yana cigaba da shirya dining din. Yana gamawa ya haura dakinshi, har lokacin bacci take ya wuce toilet kai tsaye. Mairo na ganin haurawarshi tasoma gyaran parlourn bata wani jima ba ta kammala gyaran gidan tasa turaren wuta. Fitowa yayi daure da towel ya tsaya gaban mirror Cikin bacci taji wayanta na ringing ta Kai hannu ta janyo wayan ganin dearest sister na yawo kan screen din wayan yasa tayi picking call din tareda manna wayan a kunnenta "Hello Aesha, ya akayi?" "Naji kamar ma bacci kikeyi gaskiya ne duniya ta lafa miki, kin manta munada lecture karfe 9 ne gashi yanzu 8:45" "Banida lafiya bazan iya zuwa school ba". "Eyyyaaa sorry, sannu Allah yabaki lafiya" tayi maganan kamar zata zubda kwalla. "Ameen tnx" "Kiyi baccinki idan muntashi school zan shigo" tana Kai nan ta katse kiran. Yana jinsu bece musu uffan ba ya juyo ze nufa wardrobe yaga ta kafeshi da ido tana kare mai kallo suna hada ido ya dage mata gira tayi saurin lumshe ido tana mamakin shi kwana biyu ya dan sake kamar ba shi ba. Shiryawa yayi cikin red t shirt da bakin wando ya feshe jikinshi da turare se tashin kamshi yake. Yunkurawa tayi ta zauna ta langwabar da wuya "Ina so zanyi wanka" tayi magana muryarta a shagwabe "To muje in kaiki toilet" Make kafada tayi "Aa dakina nake son zuwa" hannu ya mika mata ta kara make kafada "Nidai ka goyeni" tayi magana tana turo baki Dan kallonta yayi kamar zeyi magana Kuma ya fasa. Dukawa yayi Aiko ta haye ya nufa dakinta a toilet ya direta ya dawo bakin gado ya zauna wanka tayi sharp sharp ta daura towel ta ziro hijjab dinta kan tayi knocking kofar bayin bude kofan yayi ya shiga ya daukota yazo ya ajiyeta bakin gado Kaya tasa ya miko mata duk Wanda ya dauko tace bashi take so ba se daker ta zaba wata abaya purple. Kayan shafa ya Mika mata tashafa body