Sashe 68
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallo tana tinanin abinda zatayi me sauki da baze dauki lokaci ba, saboda ganin oga Fu'ad ya kusa yin late. *Smoked fish noodles ta fara kokarin hadawa* Gas ta kunna ta daura pot, ta kawo oil ta zuba, ta zuba kayan miya dasu onion, seasoning na noodles din ta zuba ciki ta kawo ruwa ta zuba dai dai yadda take bukata kana ta rufe pot din. Freezer ta bude ta dauko Kifi ta gyara tasa seasoning tasa a oven tayi smoking dinshi, pot din ta bude ganin ruwa ya tafasa ta dauko noodles din ta zuba ta rufe, seda ya dawu ta dauko smoked fish dinta ta cire kaya ta zuba cikin pot din, ta yanka lettuce ta zuba ta juya tabarshi like 5 minutes kana ta sauke, ta dafa egg. Dining din ta shirya, taja kujera ta zauna tayi serving kanta ta soma ci, ba jimawa shima ya fito ya zauna, bata ko kalleshi ba tace, "Good morning" "Morning my wife" kokarin serving dinshi take ya rikota ya zaunar da ita kan cinyarshi yace, "Bloody! Fushi kikeyi?" Kai ta gyada. Abincin da ta soma ci ya janyo ya diba ya kaimata fork din baki, ta kauda kai gefe tana tura baki. "Karba kici kona miki dure?" Kafada ta make yace, "Toh karba idan ba haka ba na duramiki, unaisah tayi miki dariya. Binne kanta tayi a kirjinshi tana make kafada, dan dagaske fushi take dashi. "Okay nagane, bed kike so mu koma ko?" Yayi maganan yana ajiye fork din yana kokarin mikewa, kai ta girgiza tayi kwal kwal da idanu tareda rike hannunshi a shagwabe tace, "Toh ai zan ci" tayi maganan tana bude baki. Murmushi gefen baki yayi, ya diba abincin ya kaimata baki ta karba, tare suka ci abincin yana rarrashinta tana zuba mai shagwaba, a haka har yasamu ta sauko. Har wajen mota ta rakashi, seda taga ya fice daga gidan kana ta Koma ciki. *After two months* Hannunsu gimtse cikin na juna suka shiga parlourn bakinsu dauke da sallama, kan kujera ya zauna, Unaisah wacce ta gane Aesha sosai, tana ganinta ta fara dariya tana zilo tana son ta dauketa, hannu ta mika ta dauketa tana daga ta sama tana dariya harda kyakyatawa, Muhibbah tace "Ummi ina wuni" "Lafiya kalau Muhibbah ya unaisah" "Lafiya kalau take" Iyyee ce ta karaso inda suke, Muhibbah tace, "Tsohuwa me ran karfe, dama kina duniya?" "Aa ina lahira, da bana duniya zaki ganni ne?" Tayi maganan tana zama kan kujera Muhibbah tace, "Allah huci zuciyarki daga tambaya, Kin dai ki mutuwa, kin rantse se kinci zamanin kinci namu" Aesha tace, "Kibari kawai sister, tun tana ban bance maggi da gishiri, seta dawo tana zuba Omo a abinci tana tinanin maggi ne saboda bakinta ya dena gane dan danon komai". "Toh naki na mutum duk se kun mutu kun barni, kijimun ja'iran yara" dariya sukasa har ummi banda Fu'ad da yake operating phone dinshi. "Hadiza! Har yanzu miskilin dan nan naki yana nan da bakin halinshi, yazo ya zauna yana faman girgiza kafa kamar wani dan sarki, babu kyau dai girman kai, ayi mutum se fadin rai" ita dai ummi bata ce komai ba. Kallonta yayi yace, "Kai tsohun nan kinada matsala, baza ki bar mutum ya huta ba" "Uban ka ne me matsala, kaji nace ubanka ne mai matsala" murmushin gefen baki yayi be kuma tankata ba dan yasan ya biye mata wuni zasuyi suna rigima Kuma ita ba gajiya takeyi ba. Dariya suka sa har Ummi, Muhibbah tace, "Wai tsohuwa kodai yamiki ne, kinga fine baby na wanke hannu ka taba duk kin wani rude, Kuma sedai kiyi hakuri saboda an rigaki daga ni ba kariii" wani dogon tsaki taja kana tace, "Eyyeeee, sannu fatsuma! Ina kiyayar? Kin manta lokacin daki bori a kan auren, kina yiiiii ni wllhi bana sonshi na tsaneshi bazan aurenshi ba" tayi maganan tana kwaikwayon yadda Muhibbah takeyi, me zasuyi ban da dariya. "Ai da ne wannan shima rashin sani ne, yanzu Kam ya zama past tense" "Ga takwararki" Aesha tafada tana doramata unaisah kan kafafunta, ta amsheta tana mata wasa ita ko se kare mata kallo take, alamun bata santa ba ta fara tabe baki tana kokarin fashewa. Muhibbah tace, "Ki kawo kayan takwara" Aesha ta tabe baki kana tace, "tafdi badai Iyye ba, tayi Wannan abin arzikin a gode mata" dakuwa Ummi tamata tace, "Aesha kinci gidanku" kuka unaisah tasa tana kallon Aesha dake tsaye, iyye tace "Ungo 'yar ku da alama mamanta ta biyo kuka, dan kukan da Muhibbah tayi ba'a magana, Idan ta bare baki duk rarrashin da za'a mata bata ji bata gani se tayi me isarta, take shiru". Baki ta tura tace, "Tsohuwa har yanzu dai bakya gajiya da surutu, hali na nan" Aesha tace, "Toh Abar hali a ci me" pillow ta wurga musu ta mike suka kwasa da gudu. Gida yayi jama'a su mummy sun iso, anata shirye shiryen biki, a ranan Saturday aka daura auren Suhail Abdullahi Muhammad BICHI da Zainab Sa'ad, Mukhtar da Aesha. Sosai akasha hidima anyi barin naira Muhibbah ko ajiye unaisah tayi ta gudu ta shige cikin 'yan mata bazaka ce tana da 'ya ba, tun babyn tana hakuri har tasa kuka mummy tayi rarrashin duniya taki shiru, se iyye ta daukota tashiga neman mamanta se daker ta ganota tashiga yi mata fada, ta turo baki ta karbeta tayi feeding dinta ta kara lallabawa ta ajiye ma mummy ita ta gudu, mummy tasa salati tana mamakin shiri rita irin na Muhibbah, ganin ba ganota zatayi ba yasa dole ta goyata, taciga ba da zirga zirga da ita a baya, su Aunty Asma'u nacewa dake yarinyan auta ce ai ta goyota tace taji. Tun magrib aka Kai ko wacce gidanta, inda dukansu aka kaisu cikin jimeta, mukhtar anan yayi gini tunda wajen aiki sunyi mai transfer yadawo nan, shima Suhail nan gidanshi yake, Suma su Abba cikin yolah suka tsan tsara gida suka koma nan da zama, sukan je KD suyi wata su dawo. Se bayan biki da kwana biyu da Fu'ad da Muhibbah suka je gidan Suhail, kana zeeee ke sanin Fu'ad ne mijin Muhibbah. Suna fita take tambayan Suhail, ya tabbatar mata da Muhibbah matar Fu'ad ce, ita duk tinaninta uwa daya uba daya suke da Fu'ad, Aesha da Muhibbah, shiru tayi tana tinin rayuwa wanda tayi nacin so ashe mijin kanwar wanda zata aura ne, Allah kenan. *After some years* Tana tsaye a kitchen taji anyi hugging dinta ta baya, kanshi ya zira tsakanin wuyanta yana murmushi yace, "Morning Angel of my life" hannu ta kai ta shafi fuskanshi ta fadada murmushin ta tace, "Morning darling" "Me kike dafa mana?" "Uhmmm tinanin da nake kenan har yanzu ban tsaida abinda zan dafa ba" "Karkiyi abi me wuya please, kar unaisah tayi late" Kai ta Jin jina, ta fara matso da duk abinda zata bukata. Pecking kumatunta yayi ya juya ya fice. Pot ta daura ta zuba ruwa seda ya tafasa, ta kawo noodles ta zuba tayi per boiling din ta tsaneshi a kwando. pan ta daura ta zuba oil da kayan miya dasu onion, ta kawo yankaken carrot dasu green pepper da nikaken nama ta zuba, tasa spices ta bar su suka soyu ta dauko bowl ta juye source din aciki, tafasa kwai a Kai tasa seasoning, ta dauko indomie din ta juye ciki ta juya kan ta daura pan ta zuba man gyada ta juye noodles din a pan din, da dayan man garen ya soyu ta juya yayi like 5 minutes ta sauke ta yankashi shape din triangle, ta zuba a food flask saura kuma ta zuba a lunch box, ta dauki food flask din ta nufo dining. Serving dinshi tayi ta ja kujera ta zauna. Dasauri ta karaso dining din tayi pecking kumatun Fu'ad tace, "Good morning Abbeey" tayi maganan tana mika mai hannu suka gaisa, kan tayi pecking goshin Muhibbah tace, "Mimi sabahul Khair" tayi maganan tana mika mata hannu, "Sabahun nur chu chu". Befi 15 minutes ba ya mike, dasauri itama unaisah ta mike tashiga kitchen ta dauki lunch box dinta ta goya jakanta tabi bayan Abbeey dinta, ta juyo tana ma Muhibbah bye bye. Har ta fita ta dawo tace "Mimi ki hadamun ice cream please" Kai ta jinjina mata ta juya dasauri ta fice. Kitchen ta shiga tafara hada ice cream din, bowl ta dauko ta zuba whipped cream 1 cup, powdered milk 1 cup, ta kawo condensed milk dai dai zakin da take so ta zuba, ta kawo ruwa me sanyi sosai shima 1 cup ta zuba ciki tasa vanilla flavor murfi daya tasa mixer tayi mixing dinsu sosai, ta kawo container ta juye tasa a fridge. Tana dawowa ko abinci bata ciba ta dauko ice cream din da mimi ta hada mata ta soma sha, tana fada mata abinda aka koyamata a school. Anyi bikin Rumaisa da jafar, Umaina da sauban, haka ma Ramlat da malam mukhtasir, duk da sun kammala school amma basu yada juna ba suna zuminci sosai. A asibitin Fu'ad (Meddy) Muhibbah da Aesha ke aiki. Aesha da Muhibbah sunje KD sun sha bikin Rufaida. Aunty zarah ta amarce da Anas, inda Ammar yayi wuff da Summy, ansha shagali ba kadan ba murna gurin su Muhibbah ba'a cewa komai saboda an dawo musu da kawayensu kusa dasu ko ince ma 'yan uwa dan sun wuce kawaye. Aesha ta haifa baby boy, yaci sunan Daddy ana kiranshi da Abbad, itama Aunty zeeee ta haihu tasamu mace taci sunan ummi ake kiranta da samha. Muhibbah ta ajiye katon cikinta a gaba, haihuwa yau ko gobe. Rumaisa ma tasamu mace taci sunan Ammi ake kiranta da Suhaima. Allah ya sauke Muhibbah lafiya ta santalo kyakkyawan babynta me kama da mahaifinshi, ranan suna yaci sunan Abba, ake kiranshi da Unais. Babu yadda batayi da Fu'ad akan ya barta tayi planning tun haihuwar unaisah ba amma yaki dole ta hakura ta bar maganan ganin yawan maganan naso ya hada su fada. *After some years* Kitchen tashiga ta hada dinner ta jera a dining, shinkafa ce da miya taji beef meat se tashin kamshi take. Kitchen ta koma ta fara kokarin hada mai fura. Nono kindirmo ta zuba a blender, ta kawo banana, coconut wanda ta bare bayanshi, sugar ta zuba, ta