Sashe 63
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yasa tun da kuka tashi kin bata nono" Fu'ad yace, "Ummi tun dare nayi nayi taki bata" "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, kisan kai zakuyi ne? Allah sarki baiwar Allah, gaskiya tanada hakuri. Toh mezakiyi da nonon da kike ajiyarshi? kwalliya zakiyi dashi ne?". "Ummi dan Allah kiba Aunty Suhailat tabata" iya gaskiyarta take fada harda hawaye Dariya duk sukayi, dan lamarin Muhibbah akwai ban dariya, banda Fu'ad daya hade girar sama da kasa dan ya fahimta Muhibbah da gaske take shirmen nata yayi yawa. "Ana miki magana kina cewa Suhailat tayi feeding dinta? Kin karbeta ko kuwa?" yayi maganan rai a bace Baki ta turo ta karbeta ta rungume Mikewa ummi tayi tace, "Kabita a hankali bada fada zakayi ba, bari Aesha ta kawo muku zaitun da cotton wool" ta fada tana ficewa, su Suhailat suka mara mata baya. Basu fi 2 minutes da fita ba Aesha ta miko musu zaitun din da cotton wool ta fice taja musu kofan................ AMINIYAR ANGO [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD* *AMINIYAR ANGO* *Page 58* Mikewa yayi ya koma gefenta ya zauna, ya Kai hannu ya zuge zip din rigarta yayi kasa da ita. Ya dauki cotton wool ya dangwali zaitun yafara goge saman nipple dinta, tayi saurin rike hannunshi tana girgiza kai "Yaya dan Allah kabari na goge da kaina......" Ganin kallon da yakemata yasa ta saurin sakin hannunshi taja bakinta ta tsuke. Karasa gogemata nipple din yayi, ya gyaramata babyn yasa hannunta yadda zata tallabi babyn dakyau yace, "Ki tallabeta dakyau, ki mannata sosai a kirjinki" yadda yafada tayi, ya taikamata ta seta bakin babyn yadda zata iya kama nonon. Babyn na kamawa tasaki kara tayi saurin janye bakin babyn tana fadin, "Yaya wllhi da zafi bazan iya ba, dan Allah kasiyo NAN a dinga bata kawai zefi, tunda baka son Aunty Suhailat tayi feeding dinta". Ita ko yarinya taga samu taga rashi, hakurinta ya kare, Aiko ta bude baki tasa kuka iya karfinta, bakinta har rawa yake tsabar kuka. Cikin bacin rai yace, "Fateema! Fateema!! Fateema!!!" Daga Kai tayi ta kalleshi idanunta yafada cikin nashi ta tsaya tana kallonshi na seconds kan tayi kasa da idanunta batareda tace komai ba "Kina so ajimu dake ko?" Saurin girgiza Kai tayi tace, "Aa". "Kina so sena taba lafiyarki zaki fahimta abinda nake fada ko?" Yayi maganan cikin sanyin murya Girgiza kai tayi, cikin rawar muryar dake nuna tsoronta tace, "A....aa" "Karki ga muna gidan Ummi, yanzu sena murda ma kofar nan key na zaneki, kinsan Kuma zan iya, na fahimta har yanzu bakisan inda ke miki ciwo ba, baki gane fatar baki, kiyi feeding yarinyan nan tun muna mu biyu tun tun kafin ajimu dake" idanunta ne suka ciko da kwalla ta fara kokarin feeding babyn dan tasan ba karamin aikinshi bane idan tacikashi ya zaneta, ya gwammace daga baya yayita aikin rarrashinta. Ganin tana kokarin saita bakin babyn yasashi taimaka mata, baby kamar jira take takama. Tayi saurin runtse ido hawayen dake makale a idanunta suka silalo ta saki kuka me sauti dama me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki Da mamaki yake kallonta ya Kamo hannunta, ya gimtse cikin nashi yana shafa bayan hannun ta da babban yatsanshi, yayi murmushi yace, "Wannan wace irin uwa ce haka, tana feeding babyn ta tana kuka, kina so tamiki dariya ne? Oh baby ke kam kin hadu da uwa keda ita naga me rarrashin wani". Majinar kuka taja kan tace, "Ai ba haka mukayi da kai ba, nayima alkawarin zan haifama babyn ka, daga nan na gama aikina, amma yanzu kace ba haka ba......" ta kai karshen maganan tana karama kukanta sauti Dariya sosai yayi, yakara matsawa ganganta kamar ze shige cikin ta ya sakala hannuwanshi daya ta bayanta daya ta gaba ya rungumeta ita da babyn tsam a kirjinshi. Bata zata ba taji saukar lips dinshi akan nata, tayi saurin wara fararen idanunta akan fuskarshi, idanunta ya sarkafe cikin nashi, su ka shiga kallon juna, hurt kisses yashiga aikamata dashi, ita ko se lumshe idanu tayi alamun sakonshi na kaiwa inda ake bukata, narke mishi tayi tana kokarin sakin baby shi kuwa se kara rungume su yake gudun ta sunbular da babyn. Knocking kofar da akayi yasashi saurin sakinta yana kokarin daidaita nutsuwarshi, izinin shigowa yabada Aesha ta turo kofan tashigo bakinta dauke da sallama, hannunta rike da tray tazo ta ajiye kasa kusa da kafafunsu. Kallon Muhibbah dake feeding baby tana Jan majinar kuka tayi, suka hada idanu tayi dariya mara sauti gudun Fu'ad yajita ita kuma ta watsamata harara tana kwafa. "Ummi tace ga abinci nan kici sosai bata so ki rage ko 1 spoon, kuma ki shirya yanzu zata zo ta miki wanka" ta karashe maganan tana kunshe dariyar ta Ita ko se faman aikamata da harara take tana Jan majinar kuka. Hannu ta kai zata Karbi babyn Fu'ad yace, "Kibarta tukunna bata koshi ba, kuje keda Suhailat ku hadomata kayanta dana baby, ki duba bedroom dinta akwai wayarta ki taho da ita" "Toh" abinda tace kenan ta ta fice. Kan kujera ta fada dariyar da take kunshewa ta kufcemata, Ummi tace, "Aesha menene haka? lafiyarki kuwa??" Seda ta tsagaita da dariyan tace, "Muhibbah ce ta bani dariya, Yaya yasata a gaba tana feeding baby tana kuka kamar wata karamar yarinya" "Shine abin dariya?" "Allah Ummi abin ne akwai ban dariya, kinga yadda Yaya ya tsareta ne ita ko se wani turo baki take tana shasshekar kuka, ga baby ma batasan tanayi ba se shan nonon ta takeyi hankali kwance". "Toh ke wayasan me zakiyi, ai garama Muhibbah dake" dariya tayi tace, "Haba dai Ummi nikam bazanyi shirmen Muhibbah ba, ai babyn mu ta hadu da uwa" ta Kai karshen maganan tana cigaba da dariyanta harda kwanciya. Suhailat dake gefe tana dariya tace, "kema zaki aika, zakiyi ma abinda yafi na Muhibbah, ai duk autoci ne lamarinku se addu'a" Saurin mikewa tayi ta dan zaro ido "Nashiga uku! Aunty Suhailat tashi muje kafin Yaya ya leko yaga bamu tafi ba, yace muje mu kwaso kayan baby" tana maganan tana tafiya. Bata jima ba tadawo sanye da hijjab, Suhailat ta ajiye Aadil suka fice dasauri gudun ya motsa Ummi tace dole seta tafi dashi. Hannu ya Kai ya shafi kumatunta yana murmushi yace, "'yan mata na how far" yafada yana dage mata gira Hararanshi tayi tana turo dan karamin bakinta, dariya me sauti yayi, yakama hannunta yayi pecking yace, "Ammi kawo babyn kiyi break fast" langwabar da kai tayi ta make kafada tana kare matse yarinyan ajikinta Murmushin gefen baki yayi yasa hannu ya karbeta, Muhibbah ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana gyara rigarta batare da ta kalli ko gefen da yake ba. Kallonta yayi yana murmushi me sauti ganin yadda take sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta kubuta daga wani hali "Hayateee! Da alama babyn mu batada rigima kalli daga Shan nono har tayi bacci" Dan kallan babyn tayi tace, "Uhmmmm" Kwantar da babyn yayi, ya riko hannunta ya zaunar da ita kan center carpet ya zauna kusa da ita ya ajiye tray din a tsakiyar su. Plate ya dauka yayi serving dinsu, pepper soup ne na beef head, se jallof din shinkafa dataji beef meat ga bread a gefe.cup ya dauka ya hada tea me kauri ya jeresu a gabanta ta bisu da kallo a ranta tace tafdi duk wa innan abincin ne Ummi ke cewa Karna rage ko kadan. Shinkafan ya soma bata tana karba, kadan taci tace ya isheta, kana yashiga bata pepper soup din hade da bread, taci sosai tasha tea seda yatabbatar ta koshi tana kokarin amai kana ya kyaleta Shima yaci. Tana kokarin tattare kayan dasuka ci abinci yayi saurin riketa "Blood! na huttasheki bari a turo mairo tazo ta kwashe...." kafin ya rufe baki su Aesha da Suhailat suka soma shigo da kayan baby dana Muhibbah, baki sake take kallonsu duk yadda taso ta share kasawa tayi tace, "Aesha wa innan kayan dakika dibo fa? Se kace nadawo nan kenan da zama?? Harda gadon baby, haka akwatin zuwa asibiti dakika hada kika cikashi kamar masu zuwa gidan biki harda sa pampers pack daya" tayi maganan tana dariya Itama dariyar tayi "Toh nasani ko twins ne naje nasa kaya ace se na karo" tsaki taja "Abinda yafi twins, ai ko ke zaki shirya kayan nan tunda ke kika lodosu" "Bakida matsala maman baby indai wannan ne angama" mikewa yayi, ya dauki 'yarshi ya fice daga dakin. Ita da Suhailat suka shirya kayan, suka ajiye komai a mazauninshi, Ummi ce ta turo kofan tashigo ta dubi Muhibbah tace, "Sannu Muhibbah ya karfin jikin?" Murmushi ta danyi tace, "Dasauki Alhamdulillah" Kai ta jinjina "toh taso ayi wanka" tafada tana nufar toilet din, Aesha kuma ta tattare kayan dasuka bata ta dauki tray din suka fice. Cikin sanyin jiki ta cire kayanta ta daura towel ta nufi toilet, hango ruwan zafi na tururi da tayi yasa gabanta faduwa amma ta daure ta karasa kusa da Ummin, a kunyace ta zare towel din ta tsugunna. Towel ta tsoma cikin tafasashen ruwan ta ciro ta daura a bayan Muhibbah aiko tafasa ihu ta mike a guje ta koma karshen toilet din tasaki kuka me sauti "Muhibbah lafiyarki?" "Ummi a surka ruwan please yayi zafi dayawa" "Kintaba ganin an surka ruwan wankan me jego ne? Ruwan da seda na barshi yasha iska, da iyye ce zata miki da kin gane Allah daya ne, ni dama ita tazo take miki kuyi ta dramarku ina gefe" kafada ta make tana turo baki. "Kizo muyi mu gama ayima baby, anjima kadan zakiga gidan nan ya cika da 'yan barka" tayi juyin duniya tazo ayi wankan amma fafir ta kafe ita fa se an surka, ganin bazata iya da lamarin Muhibbah ba yasa ta fice tabarta cikin toilet din. Parlour taje tasanarma Fu'ad, ya mike yabama Aunty Maiminatu babyn yabi bayan Ummi suka koma ciki, can karshen bangon toilet din ya hangota ta dauki towel ta daura tana ganinshi ta matso kusa dasu tana matsar kwalla yace, "Ummi dan Allah ki bari na zane yarinyan nan ko zata shiga hankalinta" "baza ayi haka ba, zata dena harda yarinta, abi komai a hankali" towel din ta zare ta tsugunna batareda tace komai ba. Kwafa yayi ya fice