← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 69

Sashe 35

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kalma daya kana tashiga aikinta. Dining din ta koma tafara breakfast dinta seda ta kammala ta dauki na mairo ta mikamata dakin data zaba, parlour ta koma ta danna Kiran umma, mukhtar na zaune gefenta suna dan fira ringing daya ta dauka "Ina kwana umma" "Lafiya kalau diyar kirki, ya gidan?" "Lafiya kalau umma" "ina fatan komai kalau" "Wllhi lafiya kalau umma "A yita hakuri kinji, shi aure dan hakuri ne" murmushi tayi kana tace "Naga sako na gode Allah yasaka da alkhaeri Allah yakara girma, Shima ya mu....." Da sauri ta hadiye maganan tana toshe bakinta "Babu komai Muhibbah Allah yabada zaman lafiya" murmushin yake tayi batare da tace komai ba sallama sukayi ta ajiye wayan. Duniyar tinani ya tafi yana dan taba saitin zuciyarshi ji yayi kirjinshi na suya umma ta fahimta sauyi a tattare dashi "Mukhtar lafiya? Me kake tinani?" Kai ya girgiza "Babu komai umma bari na dan kwanta kinsan weekend kawai muke samu mu dan huta" yana Kai nan ya bar gurin Da kallo tabishi tana sauke ajiyar zuciya tama rasa me zatace tayi tinanin zuwa yanzu ya manta da batun Muhibbah. Mairo kin zama tayi tunda tagama aikinta tayi breakfast tace wucewa zatayi tunda yau Saturday Fu'ad na gida, dole Muhibbah tasa driver ya maidata gida. Da rana sega Ammar taji dadinshi sosai iso tayi mai har parlourn ta cike Mai gabanshi da kayan ciye ciye, seda yaci abincin rana ta dauko mai babban frame din da agogo ya buga mata, har Fu'ad ya dawo daga masallacin a zuhur gaisawa kawai sukayi ya musu sallama ya fita. Da daddare bayan ta hado Mai coffee shi da Shan shi yazaman mai kamar ibada, ta dan zauna kan kujera ta mai godiyan ganin admission letter Kai kawai ya jinjina bece komai ba ta mike ta tafi ta kwanta. Da wuri ta tashi ta hada breakfast ta shirya "Aunty mairo yau zan fara zuwa school kishiga kitchen ki dauki break fast, dan Allah kiyi mana abincin rana kafin na dawo" "Toh shikenan Allah yabada sa'a me za'a dafa?" "No koma menene babu matsala" ta Kai karshen maganan tana ficewa dan tasan ba tsayawa jiranta zeyi ba gaban motar ta bude ta shiga yaja motar yafice daga gidan. A bakin gate din school ya ajiyeta yamata kwatancen office din malam mukhtasir sannan ya mikamata kudi tamai godiya ta shige ciki. Office din malam mukhtasir ta fara zuwa tayi knocking yabada izinin shigowa bakinta dauke da sallama ta shiga gaisheshi tayi cikin girmamawa, amsawa yayi yana dan murmushi, file din ta Mika mishi yana karanta sunan ya dago ya dan kalleta "kece wacce doctor Fu'ad yace nanema ma admission?" Kai ta gyada. Fadada murmushin shi yayi "Allah sarki yacemun kanwarshi ce, hakane ko?" Jim tayi can Kuma ta gyada kai tana dan murmushi "Ki dage da karatu, duk abinda ya shige miki duhu baki fahimce shi Dan gane da school din nan ba ki zo office ki sameni" Kai kawai ta Jin jina ta mai godiya tabi hanyar Daya mata kwatancen inda ze sadata da department dinsu. A class tasamu Aesha basu jima ba lecturer yashigo yashiga fasa musu physics. Karfe 12 suka fito daga class suka zauna kan kujerun dake school din suna jiran karasowar driver. Wani kyakkyawan saurayi ne yakara so inda suke "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" "Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh" Aesha ta amsa. Muhibbah ko tunda ta mai Kallo daya ta dauke Kai, kyakkyawa ne dan da ganinshi zakasan daga gidan manyan mutane ya fito sanye yake da Jan t shirt da bakin jeans gashin kanshi baki sidik se sheki yake idanunshi sanye da glass. My name is sauban Muhammad Auwal & You? Ya fada yana kallon inda Muhibbah ke zaune. Dogon tsaki taja ta mike ta riko hannun Aisha suka barshi nan tsaye Da sassarfa ya bisu har kofar gate "Dan Allah baiwar Allah ki taimaka ki fadamun Koda iya sunanki ne please" Aesha ce tayi karfin halin yin magana "Malam me kake so? Matar aure ce" murmushin rainin wayau yayi "Wannan ce keda aure? Haba dai ki gyara kalamanki" can kuma ya dan tabe baki ya dage kafada "dama ko wace mace ai matar aure ce tun da ko ba dade koba jima indai da rai da lafiya zatayi aura" "To ina nufin matar wani ce" ta dan fada a zafafe dan ranta ya soma baci. Ita ko Muhibbah ko ci kanku bata ce ba ta jingina jikin wata mota ta harde hannayenta a kirji. "Wanene wanin bayan niii?" Kallon bakada hankali ta mishi taja tsaki taja bakinta tayi shiru dan ta lura tacigaba da biye Mai ranta ne kawai ze baci. Ganin sun shiga mota driver yaja sun wuce ne yasa ya dan shafa sumarshi a zuciyarshi yace "yanzu aka fara game din, nayi alkawari sena siye zuciyarta yarinya dani kike wasa bakisan sauban bane" komawa ciki yayi yashiga motanshi yana mamakin yau shine mace take shareshi a school din nan shida 'yan mata ke binshi da sunan soyayya Amma ko kallon arziki basa samu a gurinshi. Dubanta Aesha tayi kana tace "Sister yafara saukeki a gida se ya juya ya saukeni kawai" "No ya kaimu gidan Ummi gaba daya, ina so na gaisheta" Kai ta Jin jina batareda tace komai ba. Bakinsu dauke da sallama ganin Fu'ad zaune kan kujera yasa Muhibbah daskarewa bakin kofan parlourn, Ummi tace "Aa shigo mana Muhibbah ya kika tsaya anan" tanaj ummi namata magana kallon tuhumar dake aikamata yasa ko motsi ta kasayi takasa gaba takasa baya bata taba tinanin ze zo gidan ummi a wannan lokacin ba kuma basuyi dashi zata zo gidan ummi ba cemata yayi idan sun tashi ta kira driver ya maidata gida. Ganin ya mike yasa hawayen dake makale a idanunta samun nasarar zubowa.......... *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION* *Page 40* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 "Ummi bari na koma asibiti akwae patient din da aka kawo emergency, ana bukatata urgently" "Toh Allah ya bada sa'a" Sallama yamata ya fice. A hankali ta karaso cikin parlourn ta risina ta gaida ummi ta amsa cikin kulawa tana tambayarta jiki ta amsa da dasauki. Aesha ce ta kwashe da dariya harda dafa ciki "Kai Muhibbah wannan tsoro haka karki bada mu mana" hawayen fuskanta ta share tana aikamata harara. "Gidanku ke waya kaiki tsoron" "Toh ai ummi gara ni, itafa matarshi ce amma ki dubi yadda ta tsure ita ba wani abu yace mata ba". "Kyaleta Muhibbah itama idan taga yayanku rudewa take kamar tasaki fitsari" "Toh ai yayan ne idan yana zare ido dole ka tsorata" Aesha tace "Babu ruwana zaku hadu dashi ai" labarin shi sukeyi suna dariya harda rike ciki ummi se biye musu take. "Sister muje muyi sallah se muzo muci abinci" "kije kiyi ina jiranki" Ummi ce ta dan kalleta batareda tace komai ba a ranta take raya kodai hasashenta ba gaskiya bane? Duk da wasu ko sunada ciki sukanyi period. Seda Aesha tayi sallah ta fito kana suka nufi dining sukayi lunching. Firan school suka shigayi can Aesha tace "Ummi yau muka hadu da wani mahaukaci a school" "Mahaukaci Kuma toh shi ko ya akayi ya shigo cikin school din, securities din bakin gate basu hanashi ba" "Ba mahaukacin gaske bane nice nasa mai mahaukacin" "Kinci gidanku ya mutum me hankali zaki dinga kiranshi da mahaukaci?". "Toh idan banda hauka ya za ace mai mutum nada aure yace dama ko wace mace matar aure ce kinga ai babu hankali a lamarin nan". Nan ta kwashe labarin yadda sukayi da sauban taba ummi. Salati ummi tayi kana tace "Kubi a hankali fa se kunyi taka tsantsan, kema Aesha karki Kuma yi mishi magana idan ya gaji ze kyaleku, karku yarda ku biye mai kundai San halin yayanku duk randa yaji wannan labarin kun Kade koni bazan iya kwatarku hannunshi ba". "Ni ummi ko maganama banyi mai ba shida Aesha ne sukayi magana" "Yauwa karki sake ki kulashi kinji ko?" Kai ta jinjina, aka shiga wata firan. Agogon dake manne a bangon parlourn ta kalla 15 minutes after 5 dawo da kallonta ga ummi tayi "Ummi zan tafi" "Bari ki tafin muku da dinner, Aesha kira driver ya kaita" laraba ce ta shiryo kulolin a basket takawo mata. Godiya tama ummi sukayi sallama har tsakar gidan Aesha ta rakota ita ko se korafi take mata dan me zata fadama ummi labarin sauban haka suka rabu. Bakinta dauke da sallama tashigo parlourn bataga kowa ba basket din hannunta ta ajiye ta nufa dakin mairo a zaune ta sameta murmushi ta sakarmata itama murmushin takeyi "Sannu da gida Aunty mairo" "Yauwa hajiya, ya makaranta?" "Lafiya kalau, gidan ummi na biya shiyasa na jima ban dawo ba, yanzu ma ke driver ke jira". "Hijjab dinta ta zira tamata sallama ta wuce" Tana kokarin shiga bedroom dinta yana fitowa daga dakinshi, Karan kula kofarshi yasa ta juyo karaf idanunsu ya sarke dana juna, gabanta ne ya fadi tayi saurin janye idanunta a dan tsorace tace "Sannu da dawowa" be ko kalleta ba ya wuce ya barta tsaye. Ajiyar zuciya ta sauke ta murda handle din kofar ta shige. Se datayi wanka sannan ta nufo parlourn sanye da kananan kaya karamar riga me hannun vest da pencil wando Legis, kulolin ta shiga jerawa kan dining kitchen ta koma ta dauko cups da plates ta zuba abincin tashiga ci har ta gama be shigo gidan ba. Tana Shirin mikewa kamshin turarenshi ya daki hancinta hakan ya sanar da ita shigowarshi kujera yaja ya zauna ido ta dan tsuramai can tace "sannu da dawowa" "Yauwa" abinda ya iya cewa kenan. Serving dinshi tayi ta tura mai gabanshi ta barshi gurin, bayanta yabi da Kallo har ta haura sama. Break fast kawai ta hada taci tana Shirin fitowa ya sauko serving dinshi tayi a hankali tace "Ina kwana" "kintashi lafiya?" A dan mamakance tace "lafiya kalau" tafada tana juyawa da niyyan barin gurin kamar daga sama taji yace "Wait for me outside" juyawa tayi ta wuce batareda tace mai komai ba. Drivern gidan Abba ne ya kawo mairo ta tambayeshi Aesha yace ya kaita school. Gaisawa sukayi da mairo ta fada mata break fast dinta na kitchen godiya ta mata ta shige ciki. Tana tsaye se faman tsaki
Chapter 35 · 0% Book details