← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 69

Sashe 8

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*Muhibbah*
"Jiki a sabule ta murda handle din kofar tashiga jakarta ta ajiye a hankali ta soma cire kayan jikinta tadaura towel tashige toilet tasakarma kanta ruwa"
Wanka tayi gamida dauro alwala tafito ta gabatar da sallahr zuhur da asr bayan tayi addu'a ta mike ta nade pray mat din ta ajiye gefe, wardrobe ta bude ta dauko kaya tashirya cikin doguwar rigar jallabiya baka sidik tadauki bakar hula tasa tana turo baki sabdoda duk duniya ta tsani dan kwali ko hula yanxun ma dan tasan muddin taje gurin fu'ad da Kai a bude wani Karin laifi ne shiyasa badan tasoba tasaka hulan.
Kamar munafuka tashiga lekan parlourn ganin sun tashi ne yasata yin ajiyar zuciya ta karasa shiga cikin parlourn tana gaida mummy dake zaune tana kallon Sunna tv, amsawa tayi cikin kulawa kafin tace auta yau ina kika tsaya baki dawo da wuri ba Kuma kince paper daya gareku, uhmmmm dama sumayya ce batada lafiya narakata clinic din school akayimata treatment, toh ya akayi Fu'ad yaje daukoki yace be ganki ba? takara jefo mata tambaya
"Eh mummy da aka gama mata treatment din ne naga jikinta babu kwari shine na kaita gida tayi maganan tana zama a daya daga cikin kujerun dake zagaye a dining din"
Kallo tabita dashi tadai jita ne amma bawai ta gamsu da abinda tace mata ba bata saba mata karya ba ko tayi da kanta take tona kanta shiyasa ta iya fahimtar akwai gyara a maganarta, hmmmm ajiyar zuciya tasauke tace muhibbah ki kiyaye fa kibi a hankali kar kiyi abinda bacin ran daddyn ku ze karu akanki fa naga kwanan nan kanki na rawa abinda da bakya yi shine yanzu kike tsiro dasu ko amma ai saukinta ga yayan ku nan ga Kuma Yayan ku Fu'ad betafi ba zasu gyara miki zama
Ita dai tayi shiru takasa cewa komai dan tasan wannan fadan kadan nema idan tasan mukhtar ne yakawo ta gida, tura abincin kawai take badan dadiba tinaninta kawai wane hukunci Fu'ad ze yanke mata wane hali zatashiga idan daddy yaji ze iya tunzura yakawo karshen alakarta da mukhtar duk da tana tsoron hukuncin Fu'ad amma hankalinta yafi tashi akan rabata da muradin ta bazata jure ba
Wata zuciya tace mata inaa bazema yuwu ba, wata Kuma tace miye abin tada hankali alhali kinada goyon bayan Abba se lokacin ta danji sanyi a zuciyarta
"Mikewa tayi a hankali ta nufi part din su Suhail knocking din kofar dakin ta shigayi babu abinda kirjinta yakeyi se bugawa jitake kamar ta rushe da kuka tun kafin tafara amsar hukuncin ta ixinin shigowa aka bata jiki babu kwari ta murda handle din kofar da bismillah tashiga bakinta dauke da sallama tana karanto duk addu'ar dayazo mata a zuciya kafin ta Kai karshen wannan ta ajiye takamo wani tsabar tsoron dake dawainiya da ita"
*Fu'ad*
Dagowa yayi yana watsamata rikitattun idanunshi take 'yan hanjinta suka hau kadawa gabanta yatsananta bugu, kallonta yayi kasa da sama daker ya bude baki yace kneel down yayi maganan can kasar makoshi ai kamar jira take da sauri ta zube shiru ne ya ratsa tsakani dakin ya dau shiru tsawon 10 minutes kamar daga sama taji yace wanene wanda naganki tsaye dashi? ya jefomata tambaya
Diriricewa tayi takasa ko motsin kirki seda taji ya dakamata tsawa ba tambayarki nakeyi ba? In...ina tafarayi n...ii y...a..ushe wani harara daya watsamata yaba hawayen idonta nasarar gangarowa dan Allah Yaya kayi hakuri shut up, kirike hakurinki bana bukata kuma
Karki bari nakara ganin digon hawayenki ki rike kukanki ze miki amfani gaba amsar tambayata kawai nake bukata
*Kuyi hkr da wannan please banida chaji
*Aminiyar ango ceeeeee
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*
*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*
*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*
*Page 14*
*Muhibbah*
"Sh... Shi...ne Wanda zan aura" tafada cikin in...inna wasu siraran hawaye na zubowa daga idanunta jikinta na dan rawa rawa tsabar yadda take a tsorace dashi ta kan kame jikinta kawai tana jiran saukar bulala.
*Fu'ad*
"Da sauri ya dago idanunsa yana dubanta yana mamakin furucinta "shine wanda zan aura" ya maimaita a kasan ranshi, lallai yarinyar nan soyayya ta rufemata ido shi take fadama Wanda zata aura ne"
Tun yaushe kuke tare?
Tun tsawon yaushe yafara zuwa school gurinki?
Yaushe kika fara binshi kuna fita?
Ya jefomata tambayoyin lokaci daya
Kuka ta fashe dashi tana girgiza Kai, wani uwar tsawa yadakamata "Shut up" bana son iskanci, hannuwanta tasa ta toshe bakin ta tana cigaba da girgiza Kai
Ba tambayarki nakeyi ba, Dan Allah Yaya kayi hakuri, bana son nakarajin komai daga gareki Indai ba amsar tambayoyina ba
Majinar kuka ta zuke kafin tace mun kae 3 years tare dashi tafada tana nuna yatsunta guda 3, Kuma wllhi baya zuwa school dinmu jiya ne kadai yazo takarasa maganar muryarta na rawa, tunda tafara maganar yatsareta da idanunsa ita Kuma Jin yadda idanunshi ke yawo a kanta yasa ta dukar da Kai taki bari su hada ido saboda idanunsa firgitar da ita sukeyi, cikin rawar murya tacigaba da cewa Kuma wllhi bamu taba fita dashi ba se... Se Kuma tayi shiru, yace "se yau ko" Ta girgiza Mai Kai tana zukar majinan kuka, tarbiyar gidan Nan kenan? Ta girgiza Kai yace ya ina magana kina kadamun Kai kamar kadangaruwa "Aa" tayi saurin fada wato kin take duk wata tarbiya kin shureta ko har ta girgiza Kai Kuma tayi saurin cewa "Aa" kina tsaye kina kallon kwayar idon saurayi Yana sharemiki hawaye a bakin gate tayi shiru jikinta nakara daukar rawa
"Karasowa daf da ita yayi kafin yayi magana tace Dan Allah Yaya kayi hakuri wllhi bantaba yin haka ba se yau Kuma bazan sakeba, wani gigitaccen Mari yadauketa dashi ji kake tassss yakara dauketa da wani lafiyayye seda ta kifa tareda dafe kuncinta tana sakin marayan kuka"
"Shut up" ya dakamata tsawa hadiyeshi kar kisake in kara Jin sautin kukanki ba dai bakida kunyaba rashin kunyanki har ya Kai a idon mutane kitsaya kuna musayan kalamai ba, Dan Allah Yaya kayi hakuri wllhi bazan karaba wani wulakantaccen kallo ya watsamata kafin yace "get out" kafin na tattakaki anan da gudu ta kwasa tayi cikin babban parlour tana haki
Mummy ta tarar inda tabarta da sauri tazo zata wuce tace muhibbah lafiya? Haki take kamar wacce tayi tseran gudu tama kasa magana daker ta iya cewa ya Fu'ad ta fada haka tana nufan dakinta dasauri, bayanta tabi da kallo tasauke ajiyar zuciya a ranta tace duk yadda akayi laifi tayi ma fu'ad din, tinanin yadda zasu kasance a inuwa daya takeyi muhibbah batajin magana shikuma fu'ad baya son wargi tasa zasu Sha wahala wurin zama karkashin inuwa daya
"Kan bed dinta ta fada tana sakin sabon kuka seda tayi me isarta kafin tashiga sauke ajiyar zuciya har lokacin zufa be bar kwararowa daga jikinta ba ji take kamar har lokacin a gabanshi take, daker ta saita numfashin ta tashiga bathroom tasakarma kanta ruwa".
Tunda ta tashi tayi wanka ta dafe kanta iya nema tayi tun jiya bataga time table dinta ba ita dai tasan Islamic ya rage musu Kuma final paper ce dg ita sun gama amma batasan morning bane ko afternoon, tinanin Kiran summy yazo mata amma takira yafi sau 5 switch off wurgi tayi da wayan ta mike saboda yadda cikinta ke kuka tsabar yunwan da takeji
A dining tasama a halin gidan gaba dayansu a gaishar dasu tayi a natse cikin sakin fuska daddy ya amsa yana fadin shalelen daddynta lafiya kike kuwa daga Kai tayi kafin tace lafiyata kalau daddy na tayi maganar tana Jan kujera tazauna break fast din tasoma yi cikin sanyi jiki
Mikewa yayi kana yace muhibbah kiyi sauri ki sameni a mota kin kusa makara Yana gama fadan haka ya fice
Da maamaki tabi bayanshi da kallo ya akayi yasan time din da take da paper kodai shi ya daukanmata time table, se lokacin wata zuciya tace mata idan be dauki time table din ba yaxa'ayi jiya yasan time din dakike da paper yauma gashi yasani, girgiza Kai tayi ranta na kuna wannan wane irin musiba ne miye hadinshi dani daze takurama rayuwata, muryar daddy ne yatsemata tinaninta tashi ki shiryamana kisamu yayanki ya kaiki karki makara murumushin yake tayi kafin tace tom, dah taso tace tareda daddy zata tafi amma tasan daddy baze bari ba zece taje dan uwanta ya kaita
Mikewa tayi jiki a sanyaye ta nufi bedroom dinta..........
*Aminiyar ango ceeeeee
*[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*
*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*
*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*
*Page 15*
*Muhibbah*
Bata jima ba tafito shirye cikin uniform tayima su daddy sallama kafin ta fice, mummy tabi bayanta da kallo tana sake sake iri iri.
Cikin motan ta sameshi ta bude gaba tashiga batare da tace Mai komai ba, kallonta yayi ta kaunda Kai gefe zuciyarta na tafar fasa
Murmushin gefen baki yayi yaja motar yafice daga gidan.
*Mummy*
"Ajiyar zuciya tasauke kana tace Alhaji nidai inajin tsoron zaman muhibbah da Fu'ad karkashin inuwa daya hankalina be.... Dakatar da ita yayi ta hanya daga mata hannu, tareda mikewa ya fice daga parlourn Suhail da Anas suka mara mai baya sunama mummy sallama"
Girgiza Kai tayi batareda tace musu komai ba tamike ta shige bedroom dinta.
Me aikinsu ne tazo ta tattara kayan da suka bata ta Kai kitchen tadawo ta gyara dining din
A gate din school yayi parking ta sauka ta shige ciki batareda ta juya ta Kalle inda yake ba
"Bata wuce 1 hour ba tafito daga hall din ta samu guri tazauna a compound din school din ta rasa meke mata dadi gaba daya zuciyarta a jagule take, A gefenta tazauna tareda dafamata kafada tace wai kawata meyasa kike son sama kanki damuwa akan mutum daya dan Allah kicire komae a ranki jibi duk yadda kika koma cikin 'yan kwanaki, wasu siraran hawaye ne suka shiga tsirarowa daga idanunta takasa cewa komai kwanciya tayi akan cinyar summy tana cigaba da kukanta
Ganin kukan nata bana kare bane yasa summy tashiga lallashinta tun kafin hankalin mutane yadawo kansu, daker ta lallasheta suka shiga cikin students anata murnan gama exams basu suka bar school din ba se 4
*Fu'ad*
Wajen karfe 2 yadawo daukanta Koda yatambaye me gadin school din yace mishi basu tashiba bega Wanda ya fito ba amma yaga sunata cashewa se lokacin yatina yau final paper sukayi kawai seya ja motan ya wuce
*Muhibbah*
Tana fitowa dashi taci karo tsaye jikin mota a kasan ranta tafara fadin innalillahi wa inna ilaehi raji'un wannan wace irin musiba ce mutum kamar maye, hannun summy tariko tace muje ya fu'ad yaxo daukana se ya saukeki tunda ba'a zo daukanki ba, murmushi tayi tace wow gaskiya ya fu'ad dinki kyakkyawane dama haka yake, harara ta watsamata ta karasa daf dashi tace sannu da yamma Yaya tayi maganar tareda hadiye wani abu me daci, yauwa ya fada Yana kashe mata ido tareda bude mazaunin driver yazauna itama ta bude gaba ta zauna summy Kuma tashiga baya yaja motar suna tafiya yana fira da summy yana tambayarta shagalin dasukayi yau acikin school tanata bashi amsa itakam muhibbah tacika da haushin summy ta wani bangaren Kuma tana maamakin miskilancin fu'ad idan be so maganaba zaka rantse kurma ne suna hada ido ta mudubi ta watsamata harara ita kam summy tayi kamar batasanma tanayi ba tacigaba da bashi amsaaa......
*NOT EDITED*
*Kuyi hkr da wannan jiya banyi typing ba yauma nayi busy shine nace bari nayi ko bb yawa kuyi hkr please*
*Aminiyar ango
[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA*
*FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)*
*DASHEN ALLAH WRITTERS ASSOCIATION*
*Page 16*
Chapter 8 · 0% Book details