← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 69

Sashe 26

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta Mika mata wayan. Numbern Fu'ad ta lalubo ta danna mai kira, Seda ya kusa yankewa ya daga "Hello" kamar bazeyi magana can yace Aesha ya akayi yayi maganar can kasan makoshi kamar wanda akayi mai dole "ba Aesha bace maimunatu ce dama Muhibbah ce batada lafiya" "toh yanzu me kike so nayi mata? Kibata paracetamol ko Diclofenac mana" "toh Yaya bafata ko motsi" be ce komai ba kit ya kashe wayan. Ranta yakai kololuwa gurin baci Muhibbah sam batajin shawara da tanajin abinda ake fadamata da duk haka be faruba indai tace a hk zata tafi toh ba karamar wahala zata sha gidan Fu'ad ba dan baze dauki iskancin nan ba, su kansu dasuke yayyinta bakyalesu yayi ba sedai idan basuyi laifi ba se sunsha fada. Tanajin Asma'u na tambayarta abinda Fu'ad yace amma ta kyaleta kitchen taje ta dauko ruwan sanyi ta dawo bedroom din. Balle murfin goran tayi tashiga antayamata ruwan a jiki da sambatu ta farka "Wllhi bana son shi dan Allah Abba kuyimun rai kar kuce na zauna da ya Fu'ad wllhi mutuwa zanyi kace ya sakeni dan Allah, Wllhi ya Mukhtar a shirye yake ya bani duk wani farin ciki na rayuwa rabani dashi tamkar katsemun numfashi n.....". Saukar zazzafan Mari a kuncinta yasata saurin hadiye maganar, tayi saurin dawowa hayyancinta tareda mikewa zaune tasaki kuka me sauti. "Dan Allah kucemun mafarki nakeyi ba gaskiya bane cewa an daura aurena da ya Fu'ad" ta karasa maganan tana kuka me cin rai. "Kinyima mutane shiru kose na miki dukan da bakiyi tinaniba" Mummy tayi maganan tana huci kamar wacce tayi tseran gudu. "Aa mummy ba haka zaki mata ba lallashinta zakiyi harda yarinta ke damunta kibita a hankali" "Kyaleni da ita Ummi wllhi ta Kuma magana anan sena fasa bakinta dama kyaleta nayi ta farfado na nunamata mune muka haifeta ba ita ta haifemu ba munada iKon yanke hukuncin da mukaga dama akanta, wane irin rarrashi ne ba amata ba babu wanda be bata baki ba hatta mahaifinta seda ya sauko ya lallasheta amma a banza sekace me zuciyar dutse ina amfanin taurin Kai, 17 years ace yarinya ce ai tana iya bambance tsakanin fari da baki tasan me kyau tasan mara kyau maganan yarinyata ya kare tsabar rashin Jin magana ne Kuma mu xuba nida ita kafin tabar gidan nan zatasha mamakina" tana Kai nan tabarsu nan. Jikin Ummi ta fada tasaki sabon kuka. Aunty Asma'u tace "Gara dai ayi a tattarata a kaita gida ya Fu'ad shine dai da ita ze gyaramata zama". "Ya isa kiyi shiru, Maiminatu kiramun yayanku a waya jikinta zafi rau" "Ummi nafa kirashi yace wai nabata paracetamol" "inji yayan naku? Kirashi ki hadani dashi seya maimaita abinda ya fada naji da kunnena yaga yadda zamu kwashe dashi". Da wayar Aesha ta kirashi amma har yagama ringing ya tsinke be daga ba, Ummi ta mikamata wayanta tace takirashi da ita ringing biyu ya daga tun kafin yayi sallama ta haushi da fada "A kiraka yarinya batada lafiya amma kace a bata paracetamol, kafita idona fa Maza Maza ina jiranka yanzun nan" tana Kai nan kashe wayan. "Sannu kinji Muhibbah kwanta kafin yayanku yazo ya miki allura". Runtse ido tayi dan ko sunanshi bata son taji an anbata. Befi 10 minutes ba se gashi ya iso har bedroom din, fada ummi tashiga yi mai shi kuma yana bata hakuri juyawa tayi ta fice ta bar dakin. A hankali ya kai hannunshi wuyanta kamar me jin tsoron jikin nata, tabe baki yayi Jin jikin nata rau kamar wuta a ranshi yace iska na wahalar da me kayan kara nima kakabamun akayi ba son auren nake ba amma idan zabina za'abi me zanyi dake yarinya. Anas ya kira yace ya duba ya mai message yaje pharmacy yasiya mai abubuwan daya rubuto Mai. Be jima sosai ba ya shigo da ledan magungunan yana ajiyewa ya fice suma su Aunty Asma'u suka bi bayanshi, Aesha na kokarin fita yace ta kawo mai ruwan sanyi a bucket da towel. A wani roba me fadi ta dibo ruwan ta kawo mai ta ajiye ta fice tare da jan kofan ta datse, taje ta sake wanka ta shiga cikin kawaye anata hotuna. Zip din rigarta ya zage tayi saurin mikewa zaune tana kankame jikin ta tana zazzare ido, shi dariya ma tabashi amma ya fuske ya daure fuska zazzabin jikinki nake so ya sauka, Kai tashiga girgiza mai "Bana so karbani" tsaki yaja ya dauki ruwan da towel ya haura gadon yayi kasa da rigar ya rage daga ita se bra yashiga dibo ruwan a towel yana daddanamata jiki tana turjewa amma yaki kulata Kuma be fasa abinda yayi niya ba, seda ya gama ya kira Aesha ta kawomata riga mara nauyi knocking tayi yaje ya bude ya karbo rigan ya maida kofar ya rufe. Yazo samata rigar ta rike "kabari bana so zansa da kaina" be kulataba seda ya zira mata rigar aiko ta cigaba da rera kukanta, A ranshi yace me zan kalla anan. Drip ya daura mata ya dura allurai a ciki, ciki harda alluran cin abinci, Jin kukan ya isheshi yasa shi dakamata tsawa, "Kin isheni fa bana son iskanci wani abu namiki ne kike wannan kukan, kinsan Allah yanzu zan zaneki kiyi kukan da hujja, nima banda bin umarnin iyaye me zanyi dake, budurwata tafiki komai da komai kyau, ilimi class duk tafiki" "Toh ai ni bance ka aure ni ba ko yanzu ka sakeni ya Mukhtar ze aureni" tayi maganan tana turo dan tsukakken bakinta. Bata an karaba taji ya murda bakin yabita da kallon gargadi. Kukanta takarama volume "Toh kayi zuciya mana ka sakeni kaje ka aure budurwar taka nima na aure ya mukhtar kowa yaje ya zauna da abinda yafi kauna". Yatsunshi biyu yasa ya dane bakin "Kika kara Kiran sunan wani anan sena fasa bakina, daga ke har wawan can sena hadaku na bibbigeku". Ya ja tsaki ya fice daga dakin. Lips dinta ta rike tana rero kukanta har bacci ya kwasheta saboda alluran da yasa acikin ruwan. Ansha hidima mutane duk sun watse se wa inda zasu kwana ne kadai suka rage. Karfe 9 na dare ta farka tanajin cikinta kamar anyimata yasa Koda Aesha ta kawomata abinci taci sosai, ummi nata jera mata sannu banda mummy dako kofar dakin bata kara zuwa ba seda tagama cin abincin Aesha ta kira Fu'ad ta fadamishi ta farka saboda dama yafada mata idan ta farka ta kirashi. Allura yazo yamata da dambe akayi alluran saboda dama bata son allura ko magani se Mummy tamata dagaske take sha idan ba haka ba duk ciwon da zatayi bazata taba shaba wani lokacin ko bare maganin akayi aka bata data faki idon mummy seta wurgar dashi. Kwana biyu da biki dangin ummi dana mummy suka tafi gida se yayar Ummi Daya da kanwar mummy suka zauna saboda Kai amarya, Ummi da Abba da Ammar suka koma gida saboda baki 'yan kawo amarya. Kafin kwana biyu ta dan murmure saboda tana dan cin abinci babu laifi. Kwana na uku da daurin aure aka shirya zuwa dinner me make up aka kira ta cancarama amarya kwalliya tayi kyau ainun a hankali take takunta cikin sanyin jiki tun daga nesa ya hangota kasa dauke kanshi yayi daga kallonta har seda suka kusa karasowa inda suke ya waske yaci gaba da wayanshi. Mota daya suka shiga shida ita, satar kallanshi tayi yayimata kyau ba laifi sanye yake cikin shadda gezna ash colour tasha aiki hularshima Ash hatta takalmin karfshima ash colour. Ita Kuma tana sanye cikin doguwar rigan shadda ash colour itama gyalenta takalminta da poser dake rike a hannunta duk ash colour ne, har suka isa babu wanda yacema wani uffan fuskarta yau ba yabo ba fallasa hakama ango, Koda aka nemi babban abokin ango yabada tarihin ango suhail ne ya fita ya bada tarihin saboda yasan Fu'ad gaba da baya tare suka taso yayi mishi farin sani hakama da aka kira babbar kawar amarya Aesha ce taje tabada tarihin amarya Summy takarma ta daura daga inda Aesha ta tsaya. Se wajen 11pm taro ya tashi. Koda suka dawo kasa bacci tayi se juye juye take, wayarta ta janyo ta nufa toilet hannunta na rawa ta danna numbern Mukhtar tayi mai kira yakai biyar amma yakiyin picking, message ta turamishi "Dan Allah ya mukhtar ka dauki wayata ko sallama ne muyi" Karar shigowar message yasa shi tashi zaune dama ba bacci yake ba tun bayan da yaje daurin aure daker ya kawo kanshi gida dauriya kawae yake kar ciwo ya kwantar dashi dan yana lure da umma hankalinta na kanshi, wayan ya dauka ya duba sakon ya maida wayan ya ajiye wayar shi ce ta hau kara sunan Muhibbah ya bayyana akan screen din wayan dan tun kwanaki ya canza sunanta daga My life zuwa Muhibbah saboda yasan ta tashi daga ruyuwarshi. Kara wayar yayi a kunnenshi batare da yace komai ba cikin shasshekar kuka ta fara magana "Ya Mukhtar nasan kanaji na, me nayi maka da na can canci irin wannan hukuncin daga gareka na soka tun ban san menene so ba Kaine mutum na farko da zuciyata ta fara aminta dashi har ta bashi daki na musamman daga cikin dakunanta, kasani bazan taba dena sonka ba, kaunarka itace ajalina" ta karasa maganan tana sakin kuka me cin rai. "Muhibbah bakiyimun komai ba, hukuncin dana yanke shine dai dai ko a musulumci haramun ne nema akan nema, kiyi hakuri jarrabawace kitayamu addu'a Allah yabamu iKon cinye jarabawarmu Kuma ki sani wannan yana daga cikin zanen kaddararmu dan haka ki runguma kaddara kar ki kara furta kina Sona ko kina so ubangiji yayi fushi damu ne? Yayi maganar cikin sigar tambaya, kaita girgiza kamar yana kallonta kafin can tace "Aa" "Toh kiyi hakuri kiyima mijinki biyayya, Allah ya albarkaci auranku yabaku xuri'a dayyiba" yana Kai nan kit yayi hanging call din. Zamewa kasa tayi ta saki kuka me tsuma zuciyar me karatu tana fadin "innalillahi wa inna ilaehi raji'un". Tun sassafe shida Suhail da abokinshi Jafar suka nufi air port flight din karfe 8 suka bi zuwa yola. Karfe 10:30 na safe su Aunty Maiminatu suka rikota zuwa parlourn daddy sanye cikin lafaya, a kusa da kafafunshi suka zaunar da ita yafara nasiha cikin sanyin
Chapter 26 · 0% Book details