← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 69

Sashe 44

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ya canza wani ya nufi wardrobe ya dauki jallabiya ya zira Daker take motsawa har lokacin idanunta a rufe se hawaye take a daddafe tayi wankan tana kokarin fita daga bath tube din taji anyi sama da ita dama karfin hali ne tasan ba iya tashi zatayi ba bare tafiya Kan bed ya direta yaja blanket ya rufeta kan ya nufi wardrobe ya dauko mata jallabiyarshi yazo yasamata yanaji tana tureshi be ko tanka ta ba sema haurawa da yayi gadon ya rungumota, kuka me sauti ta cigaba da rerowa, bayanta yashiga bubbuga alaman rarrashi "Ki dena kukan nan haka kar kiyi zazzabi please, yayanki ne ko? Natuba bazan sake ba" banza ta mai ya Kai bakinshi saitin kunnenta "Allah yamiki albarka Heebbah kin shayar dani ruwan zuma kin daukemun kishin da koda teku zan shanye ko makoshina baze jika ba kin dauke mun cutar data taru a mara na shekara da shekaru, Allah ya biyaki da gidan aljannahtul firdaus Allah ya faranta miki kamar yadda kika farantamun, Allah ya azurtamu da 'ya 'ya na gari *I LOVE YOU*" Yana maganan yana kara kankameta kamar ze maidata ciki. taji dadin kalamanshi sosai ba kadan ba amma Kalmar daya fada a karshe ne tajishi un expected se take kokonton gaske ne ko mafarki, take kuma tinanin lokacin da yanemi suyi soyayyar kwana daya ya fadomata batasan lokacin da tasaki boyayyen murmushi ba, dg haka bacci ya dauketa. a ranshi yake raya lallai dan hakin daka raina shi ze tsole maka ido ji fa 'yar yarinyan amma tasa shi ya tafi wata duniya ya Dade yana tina ne tina ne a haka har bacci ya daukeshi. Se 5:40 ya farka da sauri ya zira kafarshi ya sauka daga gadon yana fadin "Ya Salam" alwala yayi yadawo ya tada sallah seda ya shafa addu'a kan ya mike ya karasa kusa da ita blanket din ya janye yaji hucin zafi ya siraro mai a hankali ya kai hannunshi wuyanta yaji zafi rau dan zaro ido yayi "Ya ilahi" ya fada a zuciyarshi, bacci yaci karfinshi be ko ji dumin jikin nata ba se yanzu. Dukawa yayi ya huramata iska a kunne yana shafa gashin kanta, motsi ta farayi gashin idonta na rawa amma taki bude idanun Murmushi yayi "bude idonki mana ko bakya son kallon yayanki ne?" Saurin daga mai kai tayi tana kara runtse ido. Murmushin gefen baki yayi yafara kokarin daukanta ta ture hannunshi "Na kyaleki zaki iya tafiya?" Kai ta gyada "Toh jeki kiyi alwala kizo kiyi sallah Kisha magani" kokarin mikewa tafara ta sauke kafarta kasa tana takawa tasa kuka me sauti ta koma ta zauna "Wayyo Allah na Mummy na mutuwa zanyi, kafata ta cire shikenan nazama gurguwa nasan sedai a cire kafar nan batada wani amfani yanzu" da iya gaskiyarta take maganan tana kuka wiwi. Tsayawa yayi kawai yana kallonta yana murmushi shi wllhi dariya ma take bashi be cemata komai ba ya dauketa zuwa toilet da kanshi yamata alwalan ya dawo ya ajiyeta kan darduman ya zira mata hijjab ya koma ya zauna bakin gado yana kallonta A zaune tayi sallahn tayi addu'a ganin ta shafa addu'an ya karasa ya dauketa ya kwantar kan bed din ya koma ya nade sallayan. Jikinta ne yakara daukar zafi hakoranta har hadewa suke da juna jikinta se rawa yake Da sauri ya fice be jima ba yadawo hannunshi rike da magunguna Kokarin cire mata hijjab ya fara ta rike hannunshi "Dan Allah kabarni sanyi nakeji" "miye haka, wayace miki idan ana zazzabi ana lulluba?" Jin yayi maganan da dan fada tayi saurin sakinshi, yakai hannu ya zare hijjab din ya jefar kasa ya kare hade fuska yasan idan ba haka ba kan yasamata drip din nan se an jisu. Canular yafara samata tafara kuka ya girgiza kai ya cigaba da aikinshi drip yasamata ya dura allurai a ciki ya hada dana bacci Ya kunna AC yakoma ya zauna a gefenta ya gimtse hannunta cikin nashi tun yanajin sautin kukanta can yajita shiru alamun tayi bacci kallonta yayi yasaki murmushin gefen baki ya mike yabata peck a goshi ya fice. Kitchen ya shiga ya hada breakfast yayi wanka ya shirya ya tsaya gaban mirror yashafa body lotion ya bude wardrobe ya dauki kayanshi ya sa ya feshe jikinshi da turare ya fito rass a angonshi ya karasa kusa da ita ya zauna yana kare mata Fara ce tass ga dan dogon hancinta dai dai fuskarta yadda ta turo dan karamin bakinta tana faman yatsina fuska yasa murmushi kufce mai kai da gani kasan baccin wahala take. Hannu ya kai yataba wuyanta yaji zazzabin ya sauka yaja blanket ya lullubeta ya rage gudun AC ya dauko wayanshi ya hado da nata ya fice. Door bell aka danna yakarasa ya bude mairo ya gani tsaye ya juya tashigo tace "Ina kwana" "lafiya" yafada yana karasawa dining ya zauna ya zuba abincin farfesun kan rago ne da bread se tea befi 20 minutes ba ya mike ya haura daki mairo ta fito tafara gyaran parlourn. Wayanta ne ya dau kara yayi picking call din yakara wayan a kunnenshi ba tare da yayi magana ba "Hello!" Jin shiru yasa tace "Banson wulakanci wllhi, ana miki magana kinyi ma mutane banza se kace ke kesamun credit" "Aesha ya akayi?" Jin muryarshi yasa duk ta dabur ce tama rasa me zatace daker ta bude baki cikin rawar murya "Dan Allah Yaya kayi hakuri bansan kai bane" "tambayr da na miki kenan?" Yayi maganan a kausashe "Da.... da....ma naga Muhibbah bata shigo school bane har yanxu shine nace bari na kirata naji ko lafiya" tayi maganan a rarrabe. "Bata da lafiya bazata samu shigowa ba" kit ya yanke kiran. Wayan tabi da kallo tana ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseran gudu, masifar ya Fu'ad se shi tafada tana toshe baki kamar tana gabanshi juyawa tayi ta koma class. Ganin drip din ya kare yasa ya cire mata ya koma ya zauna Yana zaune bakin gado kanshi kasa yana operating wayanshi yasoma jiyo kukanta Juyowa yayi ya kalleta yana dafe goshinshi a hankali ya furta "ya Salam, yarinya se kuka kamar 'yar baby tayi kuka hakanan ma bare yau da dalili" Karasawa yayi ya yaye blanket din ya zauna ya dagota ya dorata kan cinyar shi "Kinyi bacci da kuka ba dole ki farka da kuka ba, ya jikin? Me ke miki ciwo?" Kala bata ce mai ba "Kanki ke ciwo? Ko kafar ce har yanzu ke zafi?" Saurin daga kai tayi, takara ma kukanta sauti "Yaya shikenan ka lalatamun kafa nazama gurguwa" hancinta ya dan ja "Injiwa muje nakara gasa miki ita zata warke" mikewa yayi da ita ajikinshi ya nufa toilet ruwan zafi ya hada ya tsomata hade dayi mata wanka ya na dota a towel ya fito dakinta ya nufa da ita ya ajiyeta bakin bed ya dauko kayan shafan ya zauna kusa da ita yafara shafa mata body lotion batasan lokacin da ta waro ido ba suna hada idanu a kunyace tayi kasa da kanta wani mugun nauyinshi take ji ji take kamar kasa ta tsage ta shige "Wai kunyata kike ji matar Yaya?, zama ki gama gulmanki ki bude idon ne" Har powder shi ya shafamata ya dauko mata abaya orange colour ya zira mata yanaji tana shagwabar ya kyaleta tasa da kanta yaki kulata. Sama yayi da ita "Muje ki yi break fast" "Ni ka saukeni na tafi da kafata" "Na hutasshe ki bari na cika ladana" se zilo take amma yaki sauketa, kan kujera ya ajiyeta ya juya ya nufa kitchen bayanshi tabi da kallo yamata kyau ainun sanye yake cikin tsadadden yadin shi me taushi Blue Black yakawo hula ya daura, batasan lokacin da tasaki murmushi ba. Be jima ba ya dawo rike da tray ya ajiye kan carpet ya daukota yamata masauki akan cinyarshi ya shiga bata farfesun Lecture daya gare su basu jima ba suka fito daga class suka Kamo hanya driver yazo ya dauketa tayi masu Umaina sallama "Ki gaishar da Fateema Allah yakara sauki idan gobe bata shigo ba in Sha Allah zamu zo mu gaisheta" cewar Ramlat "Ameen zataji". Gidan Muhibbah tace driver ya kaita bakin gate ya ajiyeta tayi knocking me gadi ya bude mata tashigo Door bell din ta danna Jin shiru yasa ta murda handle din kofar takoyi sa'a a bude yake kutsawa ciki tayi da sallama "Kai matar Yaya kina ina ne ciwon nan ya isheni se ance ciki gareki se kice aa toh yau nida kaina zan miki tes......." Maganan ce ta yanke ganin Muhibbah zaune kan cinyar Fu'ad hada idanun da sukayi yasa da sauri ta juya tana furta innalillahi wa inna ilaehi raji'un..............
Chapter 44 · 0% Book details