Sashe 18
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t Nan mutanen gidan suka shiga gaishe da umma cikin ladabi da sakin fuska, kana kowa ya kama gabanshi itama Zahra tabi su Muhibbah. Nan fira ya barke tsakanin umma da Mummy, daga baya ummi ta haura sama tabarsu su tattauna, ita dai mummy gaba daya jikinta babu kwari kunyar umma takeji, tun suna firan business har suka gangaro labarin duniya da abinda ke wakana a cikinta. Muskutawa umma tayi tace "hajiya hafsat! Ashe Mukhtar 'yarki yake nema, bantaba saniba". Nannauyar ajiyar zuciya tasauke kana tace "hakane hajiya Sa'adatu nima bantaba sani ba se yau". Daga haka Bata kara cewa komai ba ta kama bakinta. Seda taja fasali tace "haki kanin gaskiya na yaba da tarbiyan da kika ba Muhibbah, Yarinyar akwai nutsuwa ga fara'a da son mutane ta kwantamun a rai, Nayi burin ta kasance Daya daga cikin a halina amma dazu Mukhtar ya fadamun cewa anyi mata baiko da yayanta". "Tabbas abinda Mukhtar yafada miki gaskiya ne, Mahaifinta ya yanke hukunci banida jaa akan haka, Amma danasan kece mahaifiyar mukhtar kunyarki ta kamani wannan abu yazo duk na gida". Ta karasa maganan cikin jimami. Hannun mummy ta rike "karki damu hajiya kaddara tariga fata, haka Allah ya tsara al'amarin shi muyi addu'a Allah yasa haka shine mafi alkhaeri. Dan mukhtar be aure Muhibbah ba hakan baya nufin alakarmu zata sauya, na dauki Muhibbah matsayin diyata Kuma har yanxu bata sauya zani ba duk sanda take ra'ayin zuwa gurina dan Allah karkiyi kokarin hanata, mun riga mun zama daya". "Naji dadi sosai daki ka fahimce ni, Allah yakara dankwan xuminci". "Ameen! Ameen!!". Nan suka shiga wata firan. "Aunty zahrah ina ya mukhtar ne?, ko bashi ya kawo ku ba?". "Tare muka zo yana waje yana jiranm.....". Karar wayanta ya katseta Tana daga wayan yace "Zahra zanje gurin Friend dina idan kun gama just call me". Dasauri Muhibbah ta mike ta zari gyale ta nufa Kofa, Aesha ta rikota "Ina zuwa kike sauri haka?". "Gurin mijina". Tafada a hasale Dan taji haushin dakatar da ita da Aesha tayi. Dariya tasa "Toh me miji, muma Allah yabamu". "Ameen!" Ta fada tana kwace hannunta tayi waje. "Muhibbah ina zaki haka" cewar Mummy. "Uhmmm d...m.... dama zamu dan gaisa da ya Mukhtar ne". "Toh sekin daw" tun kafin mummy ta karasa ta fice. Kunyan idon mahaifiyarshi yasa ta barta dan tana tsoron daddy ya sameta tsaye da Mukhtar tasan fadan ba iya kan Muhibbah ze tsaya ba, har ita seya shafa. Tana fita daga gidan ta hango shi yana kokarin shiga mota, da sassarfa ta karasa tana Kiran sunan shi "Ya Mukhtar" tsayawa yayi cak tareda juyowa yana kallonta karaf idanunsu suka sarkafe dana juna, sun dauki lokaci a haka zuciyoyinsu na bugawa da sauri, murmushi tayi ta karasa gaf dashi "Barka da war haka mijin fateema xahrah". Murmushin yake yayi Wanda yafi kuka ciwo tareda hadiye wani abu me daci a makoshin shi, amma still idanunshi na kanta be ko kyafta ba. Iska ta hura mai a fuska "hey! Yada Kalo haka, ni karka cinye ni". Ta karasa maganan tana dariya. Turo bakinta tayi "Tukunna ma laifin me nayi da har ka zo kofar gidanmu baka neme niba? koda baka nemeni Dan komai ba ai ka nemeni domin kaji lafiyata" ta karasa maganan tana sakin kukan shagwaba. "Sorry autan mummy, ni na isaaa har na tafi ban nema princess dina ba, kema kinsan hakan baze taba kasancewa ba" yayi maganan yana ciro handkerchief daga aljihunshi ya mika mata. Karba tayi ta goge hawayenta, tana sakin murmushi tace "Nayi tinanin ko kamanta dani ne ai" "uhmmm wane niii ai har yanzu kina makale a kirjina" ya nuna saitin zuciyarshi. Tasa dariya. Hannu ya Mika mata "bani handkerchief dina". "Naci xarra, ban badawa, naji hausawa sunce kayan Allah na annabi ne, da Kai da kaya duk ba mallakar wuya bane, dan haka n.....". Maganar ce ta tsaya saboda hango Fu'ad da tayi ya nufo inda suke, tasan yanzu ze zo ya casta ta gaban mukhtar. Karasowa kusa dasu yayi yana mata kallon uku saura kwata ta dauke Kai kamar batasan yanayi ba, Mukhtar ne yayi kokarin Mika mishi hannu suka gaisa, a Kai kace yake kallonshi kana yace "Malam kasan hukunci abinda ka aikata kuwa?". Bece Mai uffan ba se ido daya bishi dashi dan ya fahimce raina mai wayau yake sonyi saboda kallan tun fitowarshi ya lura da kallon rainin hankalin Daya ke mishi. Ganin bashi da niyyan magana, ya dora dacewa "Bakasan cewa mata ta bace?" Ya karashe maganan cikin sigar tambaya. Dariyar rainin wayau mukhtar yayi "Au dan Allah? Ai banida labari saboda baka kawomun IV ba bare na sheda, kaga ko ubangiji baya kama bawa akan laifin dabe saniba". "Toh idan baka saniba ka sani akwai kudina akanta sannan kasan haramun ne nema kan nema, kuma kasani bana so nakara ganin kafarka a kofar gidan nan, idan Kuma ba haka ba ba za kaji dadina ba". Seda ya kalleshi kasa da sama ya nuna Muhibbah da yatsa yace "Muhibbah allurar cikin ruwa ce, Wllhi kaci darajar princess dakaji maganan dabaka taba tinaninta daga gareniba, maganar banza kake tunda ba ariga an daura ba kaga ko a Koda yaushe Allah kan canza al'amuranshi, ba abin mamaki bane a fasa auren da kai a Kuma daurashi da niiii kana kallo babu yadda ka iya daga baya ka koma kanajin kunya". Ya Kai karshen maganan yana dariyar rainin hankali. Wani iska me zafi ya furzar daga bakinshi ya dunkule hannu ya kaima iska naushi ya tako gaban mukhtar yana nunashi da yatsa can kuma ya dun kule hannu kamar ze Kai mai naushi, me ya tina ya fasa yace "malam ka iya bakinka idan ba haka ba wllhi yanzunan bakinka zeyi jini, ka tattare dattin kafarka kabar gurin nan bana so nakara ganin me kama da Kai a kofar gidan nan idan Kuma ba haka ba wllhi kotu ce zata rabani da Kai". Ya karasa maganan yana huci kamar zaki, saboda duk a maganar babu abinda yafi bashi haushi kamar inda mukhtar yace abin Allah ne a fasa auren dashi, shidae yasan ba son muhibbah yake ba umarnin iyaye yabi, amma baze so mukhtar yazama winner ba shikuma yazama looser, ina hakan ma bazata taba yuwuwa ba. Ganin fada na neman barkewa tsakanin su ta shiga tsakiyarsu tasa kuka "Dan Allah Yaya kudena, da girmanku kuke musayar yawu wannan ai abin kunya ne". Suna haka su mummy da umma suka fito saboda umma tasa zarah ta kira mukhtar ta sanar mishi sun shirya amma ba'ayi picking ba shine suka fito tunda yana tare da muhibbah tasan be tafi ko ina ba. Ganin fitowar su Mummy da irin kallan da ummi take Mai yasa shi yima muhibbah wani kallo alamun zan kamaki ya wuce ciki fuuuuu kamar ze tashi sama, Shima mukhtar na ganin haka ya shige mota ya rufo, Gaba daya Muhibbah a tsorace take jikinta har rawa yake tsoro take daddy ya fito tasan yau har su mummy bazasu tsira ba ga tsoron haduwarta da Fu'ad dan tasan ba kyaleta zeyi ba seta karba hukunci, kowa yatsaya cirko cirko se ummi ce tayi kokarin magana "Muhibbah lafiya? Me yake faruwa" cikin shassheka tace "Ummi muna tsaye da ya Mukhtar ya Fu'ad yazo ya samemu shine yace karya kara ganin kafan ya mukhtar a kofar gidan nan daga nan suka fara musayan yawu". "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un, wannan wane irin abin kunya ne Aiko zan saba mishi, dan Allah hajiya Sa'adatu kiyi hakuri, wllhi wannan lamari bemun dadi ba". "Babu komai lamarin yara se addu'a, Shima mukhtar din da laifinshi, Allah dai yakara shiryamana". Kowa ya amsa da Ameen". Nan mummy ta kara bata hakuri sukayi sallama. Ko a hanya fada umma kema mukhtar sosai cikin bacin rai "Da girmanka zaka jamun magana kome zema be kamata ka tankashi ba tunda kofar gidan su kazo sannan katsaya da matar da ze aura kowaye dole ya jama layi". Lip dinshi na kasa ya tauna ya buga stiring motan dan maganan ta na karshe ba karamin taba zuciyarshi tayi ba. Ta daura da cewa "Mukhtar dole ka hakura da Muhibbah ka rungume kaddara sannan ka nesanta kanka da ita itama ka taimakamata kadena kiranta Koda ita takiraka ka rage dauka domin zuciyarta ta samu salama ta dauki dangana". Ranshi a da gule har suka isa gida yayi parking suka nufa ciki har yayi hanya stairs umma ta kirashi "Mukhtar" juyowa yayi "Na'am" "dawo ka zauna ina son magana da Kai". Jiki babu kwari ya zauna kusa da ita, yana sauraron abinda zata fada. Cikin kulawa tafara magana "Mukhtar kacire komai a zuciyarka ka dauki dangana ka runguma kaddararka sannan kayi kokari ka cinye jarabawar da Allah ya jarabceka dashi, mahaifiyar Muhibbah kawar business dina ce mun dauki shekaru Muna business har mun zama kamar 'yan uwa". Dasauri ya dago idanunsa dasuka fara canza kala yana kallonta. "Kayi mamaki ko, Nima bantaba sanin gidan taba online business mukeyi, sedai mukan hadu duk karshen month idan angama meeting muke tattauna abinda ya shafi rayuwar mu Kuma mu bama juna shawara, dan haka bazaka jamun abin kunya ba ka rabu da Muhibbah kayi mata addu'ar Allah yasanya alkhaeri a auran dazatayi sannan ka tayata rarrashin zuciyarta, kasani babu Wanda ya isa ya aure matar wani haka zalika babu Wacce ta isa ta aure mijin wata". Nan tayi mai fada fada sannan tayi mai nasiha me ratsa jiki. Jiki babu kwari ya tashi ya haura sama, Zahra tace "Allah sarki ya mukhtar wllhi yabani tausayi, umma kinga yadda Muhibbah ke rawar jiki taje gurin ya Mukhtar ni tama fi bani tausayi" Ajiyar zuciya umma tasauke "haka Allah ya tsara, Allah yasa haka shine mafi alkhaeri" "Ameen ya rabbi". Har ummi tashiga parlour tana fada mummy na bata hakuri, bayan ta zauna ta duba Suhailat "Ke kiramun yayanku". A sanyaye ta tafi kiranta saboda tasan kuskure kadan zatayi ta karba hukuncin ta dan aurenta be hana idan tayi laifi ya