Sashe 54
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kamar wacce zata bar gari "Duk mezakiyi da kayan nan haka?" "Sawa zanyi mana Yaya" tafada tana cigaba da shirya kayan hankali kwance "Har shekara nawa zakiyi a can?" Murmushi me sauti tayi "Allah da zaka barni dase nayi shekara 1 a can bakaji yadda nayi missing mummy da daddy bane ga friends dina 1 year fa kenan bamu hadu ba" girgiza Kai yayi ya yarda har yanzu kuruciya na dawainiya da Heebbah "Amma yanzu kam wata daya zanyi ko Yaya?" Murmushi kawai yayi ya shige toilet Daren ranan bacci rabi da rabi tayi tsabar farin ciki Da safe ma tea kawai tasha suka wuce air port karfe 10 flight dinsu ya tashi.............. *Toh KD tayi kira a sauka lfy, da ina gida ai danaje mun gaisa amma sis habeber zata wakilcemu* Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD AMINIYAR ANGO* *Page 52* https://chat.whatsapp.com/K2nZjsqqivQ4PcFd1p65a8 Koda suka sauka sun samu Suhail yazo daukar su Side hug ya mishi kan ya mika mai hannu suka raba hug din fuskokin su cike da fara'a Be zata ba yaji ta fada jikinshi tana dariya "Big bro wato abin 'yar son kai ne ko Yaya kawai ka sani" murmushi yayi yana rabata da jikinshi yace "Muhibbah bakisan kin girma bane" dariya me sauti tayi ta dan kalla Fu'ad ta gefen ido taga kallon dake watsamata ta dage mai gira taja akwatin tayi gaba. Booth ya bude ya zuba kayakin ya bude mazaunin driver yashiga tana kokarin shiga gaba ya harareta dole ta dawo ta bude bayan motan ta shiga Shima ya zagaya ya shiga Suhail ya tada motan suka nufi gida. Hannun ta ya gimtse cikin nashi yana matsawa a hankali ita Kuma ta kwanto kanta a kafadarshi tana murmushi, Suhail dake kallon su ta madubin gaban motan yace "Eh irin ga drivern ku ko kun koma baya kuna Shan love abinku ko" "Kaga sa idon naku ba kaida Jafar!" Yafada yana tsaki "Babu wani sa ido da ba ayi na gani ba ai da banyi magana ba" "Kai wllhi dan matsala ne" Ita ko kunya ce ta kamata kawai ta koma ta jingina bayanta jikin kujeran Janyota jikinshi ta kwanta kan kafafunshi, chakulkuli yamata sukasa dariya a tare Madubin ya dage yadda baze dinga hango su ba dan yaga Fu'ad be san wani abu kunya ba Horn yayi me gadi ya wangale musu gate ya shiga gidan a guje tun kafin ya gama parking ta balle murfin motan ta nufi cikin gidan da gudu, Suhail yaja tsaki "Kai yarinyan nan zanga randa zata girma sudai autoci duk inda suke se ka gane su" shidai Fu'ad bece komai ba suka nufi ciki me gadi ya bisu da kayan. "Mummy! Mummy!! Mummy!!!" Tashiga kwala kira Dasauri mummy ta fito tana gyara zaninta dake neman kuncewa Jikinta ta fada ta kankame ta "Kee ni cikani ace mutum baze girma ba wllhi kin bani tsoro wannan uban kira se kace makauniya" Dariya tayi "Mummy na kenan" tafada tana jan akwatin da me gadi ya shigo dashi ta nufi dakinta na dah Kallon Fu'ad tayi "Kai yayansu sannu da kokari kana fama da Muhibbah Allah yakarama hakuri" Murmushi kawai yayi ya risina ya gaisheta ta amsa cikin kulawa kan suka karasa bangaren su Bakin gado ta zauna tana karema dakin kallo komai tsaf har yanzu komai na dakin yana nan yadda yake tun dah murmushi tayi ta mike ta cire kayanta ta daura towel ta shige toilet Wanka tayi tare da dauro alwala ta zo ta gabatar da sallahn azuhur kan ta shirya cikin doguwar rigan abaya onion colour ta yafa gyalen abayan bata shafa komai a fuskanta ba ta nufi parlourn Kan kujera ta samu mummy tana Kallon Sunna tv ta zauna gefenta tareda kwantowa kan cinyar ta "Ina wuni mummy na" murmushi tayi tace "Lafiya kalau autar mummy kina lafiya?" "Lafiya kalau, nayi missing dinku over" "Eyyyaaa auren kenan Muhibbah muma haka muka baro iyayenmu muka dawo nan muka hada wani family a hankali zaki saba kuma Allah yabaku zuri'a dayyiba" murmushi tayi taja gyalenta ta rufe fuska. Wanka yayi suka fice masallaci bakinsu dauke da sallama suka shigo parlourn ya kara so ya zauna kan kujera suka kara gaisawa da mummy ta amsa cikin kulawa tana tambayarshi su Ummi ya amsa da lafiya kalau. "Muhibbah tashi ku karasa dining kiyi serving mijin ki" A kunyace ta mike Shima ya mike suka nufa dining din mummy ta bi bayan su da kallo tana murmushin farin cikin ganin 'ya'yanta sun zauna lafiya sun hada kawuna sun zama tsintsiya Kujera yaja ya zauna tayi serving dinshi kan itama ta zauna kujeran dake gefenshi a hankali yake cin abincin se yajishi duk a ta kure dan yasa ba yamata masauki akan cinyarshi suci abincin a tare yana zolayanta tana dariya Kallonshi tayi ta dage mai gira daya ganin yana tsakuran abincin kamar anmishi dole, kasa kasa yace "Feed me please" ya fada yana bude baki Dan zaro ido tayi ta mai alama dasu mummy ya make kafada irin he don't care din nan Abincinta ta cigaba da ci hankali kwance, kafarshi yasa ya dan taka nata ta saki kara mara sauti "Ash kai hearty so kake ka karya ni kaje ka auro wata ko" tayi maganan a shagwabe Mikewa Mummy tayi ta shige dakinta yana ganin haka ya riko hannun ta ya mikar da ita ya janyota yamata masauki kan jikinshi "oya feed me! Kinga ma mummy tabamu guri mu shana" dariya tayi "Wannan abubuwan da kakeyi ba dole su koreta ba" ta fada tana kai mai abincin baki, Shima Suhail tashi yayi yabar musu parlourn Soyayyarsu suka sha kan ya fice ita kuma ta nufi dakin mummy *********** Tana zaune bedroom dinta tana karatun novel din da Muhibbah ta turamata *Haihuwa da hanji* wayanta ta dau kara tsaki taja dan Bata son abinda ze katse mata karatun ta har ya kusa tsinkewa kan tayi picking ta kara a kunnenta "Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh" "Wa alaekumussalamu warahmatullah wabarakatuh" "Barka da dare Aishatul humaira" "Barka dai, dawa nake magana please?" "Mukhtar" ya fada a takaice "Mukhtar! Mukhtar!!" Ta maimaita a saman lips dinta tana kokarin tino me irin sunan. "Gaskiya malam ban gane kaba" "Haba dai Mai babban suna kidai kara zurfafa tinani" Shiru ta danyi badai mukhtar din Muhibbah ba? se Kuma ta girgiza kai aa kam bashi bane shi me zesa ya kirata kuma ma ai beda numbernta "Ya Mukhy!" "Yeah kin canka" yafada yana murmushi "Fatan dai lafiya?" "Lafiya kalau se alkhaeri" Seda yayi gyaran murya kan yace "Ina fatan zaki amshi kokon barana ki bani dama mu gina rayuwa mai cike da so da kauna" waro ido tayi ta mike a zabure har bakinta na rawa wajen furta "What? Ka gane da wanda kake magana??" "Tabbas na gane mana" Kai ta girgiza "Aa inaga wrong number ne, bani Aeshan kake so ka kira ba" Murmushi me sauti yayi "Ke Aeshan kam cousin sistern Muhibbah my wife to be Mrs Mukhtar in Sha Allah" Shiru tayi tama kasa magana "Ina fata zaki bani dama mu karashe rayuwar mu a tare my Angel" Gaba daya ta kidime maganganunshi sun zo mata a bazata "Okay zanyi tinani" kalmomin da tayi kokari ta hadasu daker kenan "Seda safe sweet dreams dear se najiki" batace komai ba tayi hanging call din ta koma ta zauna tana dafe goshinta se yanzu ta tina Muhibbah ta Karbi wayanta jiya ashe abinda take shiryawa kenan, rai a bace tashiga dialing numbern Muhibbahn. *********** Suna gama dinner suka koma parlour gaba Daya a halin gidan Muhibbah se zuba zance take suna dariya hatta Anas yayi missing abokiyar fadarshi amma duk da haka yau din ma seda suka taba rikicin "Fu'ad ya kake ganin nutsuwar yarinyan da Suhail ke nema" cewar daddy "Gaskiya daddy yarinyan batada matsala daga gidan tarbiya ta fito iyayenta nada dattaku" "Ah Masha Allah abinda muke son ji kenan muma ba tsayawa bata lokaci zamuyi ba Abbanku da abokinshi idan suka samu lokaci se suje ayi magana kawai a tsaida lokaci" Wayanta ne ya dau kara ganin sunan Aesha na yawo kan screen din wayan yasa ta mike tana murmushi ta nufi dakinta, bakin gado ta zauna "Hello 'yar kanwata" "Me kike Shirin yi haka muhibbah? Kinsan abinda kika aikata kuwa? kina tinanin zan iya soyayya da wanda kika so shi tamkar ki mutu ne? bare har a kai ga maganar aure? gara tun wuri ki janye kudurinki ki Kuma bashi hakuri kar ya kuma kirana wllhi da nasan abinda kike shiryawa kenan da ban baki wayata ba" ta Kai karshen maganan tana nishi kamar wacce tayi tseran gudu Murmushi me sauti tayi "Kai Aesha wllhi Allah yashiryeki" tafada tana dariya sosai Kara kula tayi "Wato ga banza na magana ko" "Calm down my lovely sister kinsan inda ya mukhy nada wani aibi da bazan taba miki sha'awarshi ba kinsan bazan baki abinda ze cutar dake ba, sannan maganan na so shi ai wannan yazama past tense, ina yanzu ina tare da mijina toh me kuma ya rage tsakanina da ya Mukhtar daya wuce mutumci dan Allah ki ajiye wannan maganan a gefe" seda ta numfasa kan taciga ba da magana "Ya Mukhtar yanada duk wani qualities irin na namijin da duk macen da ta sameshi ta gama dace a rayuwarta, ilimi, nasaba, kamala, nutsuwa, kyau babu Wanda bashida shi acikin abubuwan nan da na lissafa duk da be kama Koda kafar hearty ba" tafada tana dariya, itama Aesha seda ta murmusa "Dan Allah ki karbeshi hannu bibbiyu bazaki taba nadama ba kiyarda dani please" Ajiyar zuciya ta sauke "Okay zanyi tinani tnx" "Kyaji dashi dai seda safe ki gaida Ummi" tana Kai nan ta kashe wayan. Koda ta dawo parlourn tasamu kowa ya shige dakinshi dan haka itama ta juya ta koma daki tasa kayan bacci tayi kwanciyarta tanajin kewan mijinta pillow ta janyo ta rungume tana murmushi dan tasan Shima yanzu haka yana can rungume da pillow Wayarta ce ta dau kara ta janyo wayar tareda yin dariya mara sauti ta kara wayan a kunnenta "Hearty! Bakayi bacci ba?" "Uhmmmm kema me kikeyi baki kwanta ba?" "Laa na kwanta fa tun dazu" "Toh me ya hanaki bacci?" "Yanzu zanyi" "Bakiyi kewata ba ma ko" "Nayi mana irin