Sashe 58
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
be rufeta ba saboda magungunan datasha. Be tsaya breakfast ba yana shirin fita, tace "Hearty! Dan Allah nazo mu tafi naga babyn Aunty Suhailat?" Ta fada a dan tsorace, dan ganin har yanzu a Fu'ad dinshi yake. "No! Zan turo Aesha ta tayaki zama". Langwabar da kai tayi, a shagwabe tace "Nidai dan Allah muje tare idan naga babyn semu tawo da Aesha nasan yanzu hakama maybe tana asibitin". Bece komai ba ya fice, tasan tunda yayi shiru ya amince ne miskilancin ne ya motsa, kuma koya za'ayi bazata haihu yanzu ba. Duk yadda zata kwatanta mai azaban data ke sha baze fahimta ba tunda ba'a jikinshi bane. Mayafi tadauko ta yafa, da sauri tamara mai baya ta bude motan ta shiga yaja suka fice daga gidan. Yana driving yana kallonta ta gefen ido, fuskanta yayi fayau idanunta sun zurma, gaba daya tausayinta ya kamashi, tayi yarinya dayawa 18 years ga cikin yazomata da laulayi me wahala, amma hakuri zatayi, dole ze zauna ya lallasheta gudun tayima kanta illa takuma yi mai asarar cikinshi. Parking yayi suka fito, a tare suka jera har cikin asibitin. Doctor fareeda suka ci karo da ita ta gaisheshi cikin girmamawa, ya amsa. Kan Muhibbah ta gaisheta, ta amsa tana tambayarta ya tsoron allura, sukayi dariya. Dakin da Suhailat take ta fada musu suka karasa. Bakinta dauke da sallama tashiga dakin banda Fu'ad da yayi tashi akan lips, tana zaune tana feeding baby suka sameta, Aunty Maiminatu na zaune gefenta. Fuskarta dauke da fara'a ta karasa "Ina kwana Aunty Maiminatu" "lafiya kalau Muhibbah". "Maman baby Ina kwana". "Lafiya kalau" "Ya baby?" "Lafiyanshi kalau". Cikin girmamawa suka shiga gaishar da Fu'ad, ya amsa cikin sakin fuska yana tambayar Suhailat karfin jiki, ta amsa da Alhamdulillah, tana mika mai babyn. Karba yayi yamai addu'a, Muhibbah ta mika hannu ya daura mata yaron ta kalleshi tana murmushi, tareda manna mai kiss a kumata. "Tubarkallah Masha Allah! Aunty Maiminatu kin Kalli yaron nan kam, kinganshi kyakkyawa". "Na gani Muhibbah". "Dan Allah Aunty Suhailat ki barmun yaron nan" "Yanzu kuma kin fasa zarahn kenan? Haka zakiyima daughtern naki?". Dariya tayi "jariri ne akwai sha'awa, bare wannan tubarkallah dan lukuti, dan Allah ki barmun shi sena hada duka harda zarahn". Dariya sukayi har Aunty Maiminatu "Toh Muhibbah na bar miki, amma ki barmun zarah bana zauna ni kadai ba" "Eh na yarda". Hada idanu sukayi da Fu'ad ya harareta ta dauke kai tana turo baki. Fita yayi ya dawo da wasu allurai yazo yama Suhailat, ya juya ya fice. "Yunwa nakeji" tafada tana shafa cikinta. "Bakiyi breakfast bane kika fito?" Cewar Maiminatu. "Eh Aunty! Naga Yaya ze tawo yabarni ne shiyasa". "Toh ga flask nan akwai ruwan zafi ki hada tea" "Aunty! Bazan iya Shan tea ba". Suhailat tace "Toh ga soyayiyar doya da miyan source da Aunty Maiminatu tazo dashi". Yatsina fuska tayi "Kai bar doyan nan Aunty". "Farfesun fa?" Ta fada tana bude kula, saurin toshe hanci tayi tana ja baya tareda girgiza kai. Da mamaki suke kallonta, Aunty Maiminatu ta bude baki zatayi magana Aesha tashigo. Ta zauna tana gaishe su, suka amsa ta Karbi babyn itama se santinshi take. Food flask din da Aesha tashigo dashi tashiga budewa, tayi murmushi ta dauki plate ta zuba ta koma ta zauna. Tanajin Aesha na tsokanarta tayi banza da ita dan yunwa takeji jikinta har rawa rawa yake. Sosai taci ta ajiye plate din, aka cigaba da fira. Zare gyalen tayi ta jefar kasa ta kwasa bayi a guje ta shiga Kwara amai. Da sauri Maiminatu ta bita tana mata sannu, seda tagama ta taimaka mata ta kuskure baki ta rikota tazo ta kwantar da ita kan hadadden gadon asibitin da zaka dauka gida kake tsabar haduwar dakin da suke ciki komai akwai, fridge, tv dasauransu, Aesha ta karaso itama tanata jeramata sannu. "Gaskiya babyn nan yana wahalar mana dake". Ita dai bata kulata ba se numfashin azaba take saukewa "Jeki ki kira Yaya" da sauri Aesha ta fice, ba jimawa se gashi sun dawo tare da Fu'ad. "Heebbah! Jikin ne?" Kamar jira take yashigo tasa kuka. "Wayyo Allah mummy na, nashiga uku na zan mutu, wllhi Yaya bazan iya ba na gaji....". "Kinyimun shiru ko sena bige bakin ki". Bakin ta taja tayi shiru bata iya kara cewa komai ba se kuka kawai take Kayan aiki ya dauko yazo yasamata drip yasa allurai a ciki ya hada dana bacci, ya zauna gefenta ya riko hannunta yana kallonta. Su Kuma su Aesha suka juya suka cigaba da firansu kasa kasa. Seda yaji tayi shiru alamun bacci ya dauketa, kan ya zare hannunshi daga nata, ya gyaramata kwanciya ya fice. "Wllhi natausayama Muhibbah laulayi me wahala takeyi, cikin zarah na sameshi a bonus amma wannan karon kam naci kwakwa, ko ruwa nasha seya dawo, seda ya girma nasamu sassauci amma duk da haka yau lafiya gobe ba kalau ba. Sedai banyi tsayin na kuda ba dan da tasowar na kuda da isowarmu asibiti befi 40 minutes ba, kuma Ina zuwa banjima ba na haihu". "Kinsan cikin Khalil wahalar da naci, ni ko abincinma bana iya ci, ruwa wannan sena wuni ban kaishi bakina ba, ciki tun be kai sati 2 ba kowa seda yasani daga karshe gidan Ummi na dawo, har na haihu bazan ce miki gashi yau naji ni normal ba, Kuma ana cewa idan kayi laulayi me wahala kana samun nakuda me sauki, toh nikam har na kudan babu sauki seda na wuni cirr ina abu daya. Allah dai ya raba lafiya, amma haihuwa is not easy". "Ameen" suka amsa dashi. Ita dai Aesha na jinsu tayi ta gumi tana tausayin yayarta, kawarta, kuma aminiyar ta. Koda ta tashi taji karfin jikinta, sallah tayi taci abinci amma still seda tadawo dashi, ta gumi ta zabga tana hawayen tausayin kanta tana tinanin mafita, Aesha se faman lallashi take. Se yamma ya daukesu gaba dayan su, duk ya dire ko waccen su gida. Suhailat tasamu uwar mijinta ta turo mata dattijuwar dazata dinga kula da ita da babyn ta. Restaurant ya biya, ya siya musu abinda zasu ci, kana suka dauki hanyar gida, a masallacin unguwar su yatsaya yayi sallah kan suka karasa gida. Wanka tayi, tayi sallah ta nufo parlourn Har yasoma cin abincin ta karaso taja kujera ta zauna, tasa spoon suka cigaba daci tare, tana ci tana tsoron abinda ze biyo baya, Tayi sa'a har ta kwanta bacci bataji aman ba. Shiryawa yayi cikin kayan bacci wando iya guiwa ko riga besa ba ya nufa dakinta, gefenta ya kwanta ya daurata kan kirjinshi yanajin yadda feeling dinta ke taso mai Mutsu mutsu ta fara, yayi saurin tashi zaune ta dirka da sauri tayi toilet. Abinda taci ta fitar, ya taimakamata ta kuskure baki suka fito, kukanma nemanshi tayi ta rasa tsabar azaba, bakin gadon ya zauna yamata masauki kan kafafunshi. Mannota yayi da jikinshi, yana shinshinan wuyanta tareda shafa gashin ta, ita Kuma ta sakalo wuyanshi tana kara lafewa a jikinshi. "Sorry bloody! Babyn nan yana wahalar mun dake, duk randa yazo sena rankwashe shi" Hawaye ta fara "Yaya kanajin azabar dana keji kuwa? komai naci seya dawo. Kona so naki ci bana iyawa yunwa bata barina, katausayamun mu zubar da cikin nan zuwa gaba, kaga nayi karama.....". Tayi maganan jiki a sanyaye Bakinsu ya hade yashiga aikamata da hurt kisses, seda ya kashe mata jiki kan ya raba bakinsu. "Bakya so ki haifamana irin yaron Suhailat ne?, kefa naji kina cewa tabaki yaron". Kai ta gyada kan tace "Ina so mana, yaron kyakkyawa tubarkallah gashi dan lukuti nafi son irin yaran, wllhi dazata bani shi karba zanyi". "Toh meyasa ke bazaki haifa mana ba?" "Toh aini nayi karama" "Injiwa? Waya fadamiki? 'yan 15 years ma suka haihu bare ke, ki daure please, gaba kadan aman ma ze tsaya ba kinga yanzu kindena zazzabin ba?" Kai ta jinjina. "Kuma fa haihuwa babu wani wahala, kinga ni doctor ne nasha karbar haihuwan yaran da basu kaiki ba, sannan bamusan ko iya shikenan kwanmu a duniya ba, idan muka zubar Allah ze kamamu da laifin kisa, sannan ya jarabcemu a lokacin da muke nema ya hanamu saboda ya bamu a farko, munyi butulci bamu gode ba, zaki so mu kashe rai? Ran ma na danmu". Saurin girgiza Kai tayi kana tace, "Toh na yarda zan haifoma baby, amma kai zaka karbanmun haihuwan da kanka ba doctor fareeda ba, dan ita Kam barina zatayi nasha wahala" murmushi yayi tareda gyada mata kai "Naji na yarda". "Toh ai ni kunyan su Abba da daddy nake, idan suka sani fa" Dariya sosai yayi "Toh menene dan sun sani? Ina su suka mana auren? ai murna ma zasuyi, barima na kira na sanar musu, su ma babyn mu addu'a tun kafin ya iso". Ya fada yana dauko wayanshi Saurin rike mai hannu tayi tana kukan shagwaba, "Nidai kar ka kirasu, ai se suce bamuda kunya". Dariya maganan ta bashi ya ajiye wayan ya shiga yawo da hannunshi a jikinta, ganin zaman baze mai ba yayi baya baya suka kwanta. Se korafin batada lafiya take tana tureshi, ya birkitata tadawo kasa yamata runfa ya hade bakinsu. Tun tana nokewa har ta biye mai suka sha bidirin su dan ba karamin missing dinta yayi ba itama tayi missing dinshi. Aesha na shiga ko zama batayi ba ta hau sanarma ummi Muhibbah nada ciki, murna gurin ummi kamar me se washe baki take, Abba nadawowa tayi mai albishir, shima yayi murna ba kadan ba Gidan ummi ya sauketa ya juya ya nufa asibiti, Ta karasa cikin parlourn kanta kasa. "Ina kwana Ummi" "lafiya kalau Muhibbah! Ya karfin jiki" "da sauki" ta amsa a kunyace. Gaba daya kunyan ummin take ji har ummi seda ta ganota. Har dare tana gidan, tausayinta ne ya kama ummi ganin yadda take amai, batada daman cin wani abu ta zauna lafiya. Aunty Asma'u tazo saboda gobe sunan Suhailat, nan ta kira Mummy ta sanarmata autan ta nada ciki, nan tashiga murna kan kace me har su Anas duk sun sani. Washe gari sukayi ma gidan Suhailat tsinke, Fu'ad yaso hanata zuwa tasa mai kuka dole yabarta. Wuni tayi daki dan bata so mutane suyita cewa tayi haske ta kara kyau, amma idanunta sun zurma. Har Zeeee da Rumaisa ma sun zo, sunata