Sashe 1
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font *SOYAYYAR KWANA DAYA* *WRITING BY FATIMA A MUHAMAMMAD (AMINIYAR ANGO)* *Page 1* Dedicated to my *lovely mum* Sadaukarwa xuwa gareki wannan page din nakina mamana abin alfaharina Allah yakara miki lfy da nisan kwana me albarka *Da sunan Allah me rahma me jin kae,Godiya ta tabbata ga ubangijin talikae wanda yabani damar fara rubutamuku wannan littafin,Amincin da taslimi sukara tabbata ga annabin mu annabin rahma annabi muhamammad salallahu alaehi wasallam* https://chat.whatsapp.com/IVMTZRVmci41jq3pTyzdZs Wata 'yar madaedaeciyar budurwa me matsakaecin shekaru na hango kwance akan bed tana waya se faman sheka dariya take,da alama wayan nasata farin ciki. Mummy ce tanufo bedroom din knocking tafara yi taji ba'ayi maganaba,shiru tayi jin dariyar dake tashi a dakin kara kunnenta jikin kofar tayi ta fahimta waya takeyi tana jin wasu maganganun wasu kuma bata fahimta . Ganin wayan nata bame karewa bane hakan yasa mummy karayin knocking din kofar amma ina tayi nisa batasanma anayi ba,cikin mamaki mummy ta murda kofan tayi sa'a kofar bude take. Shiga tayi da sallama kafin tace Muhibbah lafiyanki kuwa kedawa kike waya tun daxu inata knocking amma shiru kmr bakya dakin. Xabura tayi ta xauna ganin mummy tsaye a kanta cikin borin kunya tace mummy nemana kike ne,wani kallo ta wurgamata kafin tace Muhibbah dawa kike waya,mikewa tsaye tayi gabanta na faduwa amma seta sakarma mummy murmushi tace wata kawata ce munjima bamu haduba kuma nayi missing contact dinta shine yau takirani tanayi tana boye wayan a bayanta. Kallonta mummy tayi tana mamakin karyan da tamata me take son boyemata saboda wayan da take ya nuna da namiji take waya, Muhibbah ce ta katse mata tinaninta ta hanyar fadin mummy yau ni xan hadamana dinner nakoya wani jallof rice a wayata natabbatar idan kikaci girkin nan se kunnenki ya kusa tsinkewa. Daddy ko idan yaci seyamun kyauta,bata tsaya jiran amsan da mummy xata bataba ta fice daga bedroom din, murmushi mummy tayi tanafadin Allah yashiryamun wannan yarinyan. Bayanta itama tabi a parlour ta taddata xaune tana kallon mbc 3 gefenta ta xauna tana fadin kedae Muhibbah har yanxu bakida banbanci da yara aekin ki kenan kallon cartoon Murmushi tayi tace mummy dama ni na girma ne 17 years fa nake kinga ko dasaurana saboda Kinga bakida kanwa shiyasa kike fadan haka amma bari kwanan nan xan haefo baby. Hada fuska tayi a dan shagwabe tace haba mummy na wane irin baby kidena fada Kar yaxama gaske,dan sedae kikaeshi gidan marayu dariya mummy tayi tanafadin sedae ke na kaeki gidan marayu saboda kece maraji dariya sukayi gaba dayansu. Haka suka dinga firarsu cikin farin ciki,A gogon dake manne a bangon parlourn Muhibbah ta kalla karfe 1:30pm dasauri ta mike tace mummy time din school yakusa bari naje nayi shiri batajira amsan mummy ba ta shige bedroom dinta. Tana shiga Kae tsaye toilet tashiga tayi wanka tareda dauro alwala tana fitowa pray mat ta shinfida sallahn axuhur tayi kafin ta mike tanufa wardrobe dinta budewa tayi ta dauko uniform bata wuce 5 minutes ba tashirya wando ne blue black se riga white hijjab ma blue black, nikab ta daura tareda dauko school bag ta fito bata same mummy a parlour ba bedroom dinta ta nufa knocking tayi akabata ixinin shiga. A xaune ta taddata kan pray mat tana karatun alqur'an me girma,mummy xantafi nakusa makara harta juya xata tafi sekuma ta dawo tace yauwa mummy na karki manta nace yau ni xan hadamana dinner kafin mummy tayi magana harta fice daga bedroom din murmushi tayi kafin tacigaba da karatunta Tana fitowa ta shige mota driver yaja suka fice daga gidan,a daedae wata katuwar makaranta yayi parking, bude motar tayi tafito har xata shiga makarantan se kuma ta juyo wajen driver tace please kadawo da wuri saboda yau Ina so nakoma gida da wuri inada aeki tom madam in Sha Allah xa'ayi hakan Anan tabarshi ta shige cikin makarantan shikuma yaja motarshi yayi gida,tana shiga class suka fara fira dasu Rufaeda gyaran muryan malam sudaes sukaji dasauri kowacce ta koma wajenta ta xauna. Awa 1 da rabi suka kwashe a cikin class malamae 3 suka shiga ko wanne ya musu karatun 30 minutes Sallahn la'asar suka yi kafin suka koma class subject biyu sukayi karfe 5 daedae a katashe su tana fitowa driver na jiranta yau bata tsaya bata lokaciba tashiga mota suka nufi gida,ko gama parking beyiba dasauri ta fito tana shigewa parlourn bakinta dauke da sallama bata tada kowa a parlourn ba Kae tsaye bedroom ta wuce ta canxa kaya. Dawowa parlourn tayi har lokacin babu kowa hakan yasa ta nufa kitchen tafara girki per boiling din shinkafa tafarayi kafin tafara blending din kayan miya ji tayi kamar mutum a bayanta dasauri ta juya ganin mummy ce yasa tasakarmata murmushi itama murmushin tasakarmata tana fadin Muhibbah yaushe Kika dawo,tun daxu nadawo mummy inata sallama naji gidan shiru babu kowa a parlourn nikuma ina sauri na daura girki Kar daddy na yadawo yasama ba'a agama ba. Gaskiya kin kyauta Shalelen daddynta murmushi tasake wanda har seda hakoranta suka bayyana saboda a rayuwarta tana so a kirata da Shalelen daddynta,toh yanxu mexan Kama miki,aa mummy kije ki huta yau ni xanyi komae.Karfe 7:00pm takammala komae ta jerasu akan dining kafin ta wuce dakinta domin gabatar da sallahn magrib. Wanka tayi saboda taji dadin jikinta kafin tagabatar da sallan magrib tana xaune akan pray mat har akayi Isha'i kafin ta bude wardrobe dinta tadauko kaya,gaban mirror takarasa tashafa body lotion cikin 'yan mintina tashirya vest ce tasa se skirt iya gwiwa takama gashinta amma duk da haka jelarshi nareto a bayanta kayan sun amsheta sosae se xuba kamshi take tamkar me me shirin tarban ango. A dining ta tarar da a halin gidan suna jiran fitowarta karasawa gurinsu tayi cikin sakin fuska tace daddy Sannu da dawowa yauwa Shalelen daddynta ya fada yana mata murmushi,food flask tabude tafara serving dinsu jallof rice ne da naman rago se xobon data hada har sun fara cin abincin kafin tace mummy ina ya Anas ne ko har yanxu bedawoba kafin ta karashe maganarta yashigo tareda sallama amsawa sukayi kafin yaja kujera ya xauna kamshin abincin ne ya daki hancin shi yace kae yau daji abincin nan xeyi dadi shima serving dinshi tayi yana Kae cokali 1 yace wow gaskiya yau girkin nan yayi dadi,dariya Muhibbah ta kwashe dashi tana fadin ashe na iya girki irin wannan santi haka. Allah ya kiyaye naci abincinki yaushe Kika iya irin wannan girkin,sedae Kar a Kuma ci na nawa kuma hade fuska yayi shi a dole babban yaya yace ke ina wasa dake ko daddy ne yace mekuma yafaru kuda bakwa xama inuwa daya bakuyi fadaba. A shagwabe tace wae dan nace yana santin girkina shine nayi laefi toh ae gaskiya tafada saboda girkin yayi dadi sosae shalelen daddynta cewar daddy,dama dagaske ita tayi girkin cewar anas mummy ce tabashi amsa da Eh haba shiyasa naji girkin wani kala ko Maggi beji ba hade fuska tayi tace mummy kinajin abinda ya anas yake cewa ko wae abincin beyi dadiba aa tsokanarki yakeyi shima yasan yayi dadi haka suka dinga tsokanar junansu su daddy na biyemusu suna dariya. Wayarta ce ta hau Ringing sunan ya Fu'ad mummy tagani yana yawo akan screen din wayan tana mamakin lafiya fu'ad yake Kiran muhibbah da dadaren nan daxuma fa yakirata suda bawani jituwa suke da junaba mikama Muhibbah wayan tayi ganin sunan dake yawo akan screen din wayan yasata xaro ido tana kallon mummy hada ido sukayi kalkalo murmushi tayi tace seda safenku sallama sukayi tanufi bedroom dinta. Kwanciya tayi tafara tinanin anya mummy bata fahimta wani abu tsakaninta da ya Fu'ad ba tana haka wayanta ta hau Ringing Kara wayan tayi a kunnenta tana fadin Amincin Allah sutabbata ga yayana amsawa yayi da Ameen tareda kyakkyawar kanwata,fuska ta rufe kamar yana ganinta tace Kae dae ba'a rabaka da xolaya. Ina Kika shiga ne daxu nakira sedae mummy tayi picking gabantane ya fadi tace da yaushe kenan wajen karfe 7 murmushi me kama da kuka tayi tace namanceta a kitchen ne nikuma Ina bedroom ina sallah,yayi kyakkyawar kanwata me aka rokamana ajiyar xuciya ta sauke kafin tace abubuwa dayawa sun dau kusan 1 hour suna waya kafin sukayi sallama, toilet tashiga tayi brush ta dauro alwala addu'ar kwanciya bacci tayi kafin ta kashe bulb din dakin ta kwanta.................*SOYAYYAR KWANA DAYA* *It based on true life story* *WRITING BY FATIMA A MUHAMAMMAD (AMINIYAR ANGO)* *Page 2* Dedicated to my *lovely dad* Wannan page din naka ne Abbana da baxarka nake taka rawa Allah yakarama lfy da nisan kwana me amfani *Da sunan Allah mae rahma mae jin kai,Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai,Aminci da rahma sukara tabbata ga annabin mu annabin rahma annabi muhamammad salallahu alaehi wasallam* https://chat.whatsapp.com/IVMTZRVmci41jq3pTyzdZs Bude idonta tayi tasaukeshi akan agogon dake gefen bed dinta tareda fadin * Karfe 7:00am dasauri ta fada toilet domin yin wanka bata dauki lokaci ba tafito,shiryawa tayi cikin uniform dinta rigace iya gwiwa se socks doguwa wacce tarufemata har gwiwa se hijab dae dae kafada. A dining ta tarar da ahalin gidan suna break fast cikin sakin fuska tanufa dining din tana fadin good morning my family tafadi haka tana xama a kujerar dake gefen Anas amsawa sukayi cikin sakin fuska,kallon ya Anas tayi tace ya anas yau Kae xaka kaeni school ko,wani harara ya watsamata tareda fadin Ni drivern kine? Yafada cikin sigar tambaya. Fuska a shagwabe tace please dan Allah ya anasa ka taemaka ka saukeni a school seka wuce wajen aeki,rankwashi ya kaemata yace baxan sauke ba idan baxaki je driver ya kaeki ba kibar xuwa school din. Kukan shagwaba tasaki tareda fadin daddy kana ganin ya anas ko, kyaleshi shalelen daddynta yi sauri kigama breakfast din na saukeki da kaina . Murmushi mai sauti tasaka yauwa daddy na abin alfaharina tafada haka tana kallon ya Anas,ku dai bakwa xama inuwa daya baku raba haliba cewar mummy. Wannan yarinyar ta raina ni idan banda neman magana dama ni nasaba kaita school din ya fada haka fuska a hade. A haka suka kammala breakfast din tabi bayan daddy suka fice. A daidai wata katuwar makaranta yayi parking *KA'AB BN MALIK ACADEMY* Kae da ganin makarantan kasan bata kananun mutane bace,1 thousand yamikamata godiya tama daddy