← Book details Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 69

Sashe 46

Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sauke ya cire kayanshi ya shige toilet yasakarma kanshi ruwa Itama dakinta ta shiga tayi wanka ta feshe jikinta da turaruka kan tafito ta nufa down stairs, se lokacin Kuma ta danji kunya kar Aesha ta kawo wani abu ganin tayi wanka. Zaune ta sameta kan kujera ta karasa ta dauko karamin ledan da ya Fu'ad ya kawo tadawo ta zauna kusa da ita ta Mika mata dan tasan nata ne karba tayi tai godiya ta mike "Sister bari na tafi har an fara Kiran magrib" "Ki bari yanzu Yaya ze sauko tunda an Kira magrib" Yana fitowa wanka ya tsaya gaban mirror yana shafa ya soma jin karar wayanshi karasawa yayi ya dauka ganin sunan zeeee yasa ya dan shafa kanshi shi har ga Allah yama manta da ita be kyauta mata ba yamata alkawarin ze kirata Kuma yasan duk inda take hankalinta na kanshi har ya tsinke be daga ba kan ya shiga dialing numbern ringing biyu ta daga muryarta har rawa yake "Barka da yamma my D" "Kina lafiya?" "Lafiya kalau" ta fada tana murmushi Shiru ne ya ratsa tsakani Jin beda niyan magana yasa ta aro jarumta "Uhmm da... Dama kan maganan da mukayi ne kace zaka kirani" "Oh sorry na sha'afa ne madam batajin dadi shiyasa natattara hankalina na maida kanta" Runtse ido tayi da karfi tanaji kamar zuciyarta zata faso ta fado daker ta hadiye wani abu me daci "Allah sarki Allah yabata lafiya kayi mata sannu" "Ameen! Zataji in Sha Allah, zan kiraki zuwa gobe" "Allah ya kaimu zan tinama gudun mantuwa" bece komai ba ya katse Kiran. Sauri sauri ya shirya ya sauko "Hibbah bari na Kai Aesha nadawo" "Allah yatsare" ficewa yayi Aesha ta mara mai baya Muhibbah nata mata godiya kan itama ta juya ta haura dakinta. Seda tayi isha'i ta zauna dining har tafara cin abinci se gashi kujeran dake kusa da ita ya zauna ya karba spoon din hannunta ya shiga bata abincin da kanshi tare suka cinye abincin tanata zuba shagwaba Se yanzu takejin ashe su Abba basuyi mata zaben tumun dare ba shiyasa akace duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi baze hango shi ba duk soyayyar da mukhtar ya nunamata Ashe duk wasan kwaikwayone duk da ya kan fadamata wani abun baki yayi kadan wajen furtashi sedai a aiwatar dashi a aikace yasha fadamata aure ne kawai ze basu wannan daman, shima Allah kadai yasan irin kulawan daya shirya mata Murmushi ta danyi ta yarda aure shine ribar soyayya duk wata soyayyar da za'ayi a waje shirme ce. Hannunta ya riko har dakinshi ya dauki jallabiyarshi ya zira mata dariya tayi tana kallon kanta ganin rigar tayi mugu mugun yimata yawa janta yayi kan gado ya kwanta ya janyota jikinshi yafara rudamata jiki da salonshi tana dariya taso biye mishi amma tina azabar datasha jiya yasa tafara kokarin tureshi gudun tasa kuka yasashi kyaleta yana bubbuga bayanta a hankali yana huramata iska a kunne har bacci ya dauketa Shima ya kwasheshi. Sun makara a baccin da suka koma bayan sallahn asuba sauri sauri sukayi wanka suka shirya ko break fast ba su yiba suka fice daga gidan Bakin gate din school din yayi parking ya cire kudi ya ajiye mata kan jikinta ta dauka tace "Tnx" tana kokarin bude motan ya riko hannunta "Kin tabbatar kin war ware zaki iya shiga class? Idan bazaki iya ba mu juya mu koma hospital ki tayani duba patient's" dariya tayi "Uhmmm kar kadamu naji sauki ina ni ina duba patient's wannan se ku" "Kema soon idan da rai zaki iya ai" "Toh Allah ya nunamana lokacin" "Ameen! Ya kafar taki tadena zafin gaba daya" "Abin babu kara wai kafata" tafada tana turo baki "A gafarceni ya kafarmu" Ya fada yana danne dariyarshi dariya tayi ta juya zata fita yace "ki fara siyan abinda zakiyi break fast kan kishiga class take care" "Thank you" daga haka ta fita tashige school Juyawa yayi ya dau hanyar asibitin yana shafa kanshi wato idan ka aure yarinya kaima yaron kake komawa se a zauna lafiya. Se 5 suka tash i tunda suka fito sauban ke binsu har suka fito bakin gate suna jiran karasowar driver daga ita har su Umaina babu Wanda ya tankashi Fitowarshi asibiti kenan ya dau hanyar gidan Abba yaji wayarshi ta dauki kara kamar baze daga ba ganin sunan malam mukhtasir yasa ya daga da sallama hankalinshi na kan titi "Likita bokan turai Barka da wannan lokaci" seda ya murmusa kan yace "Barka dai teacher uban karatu ya akayi ne?" "Lafiya kalau dama kokon barana na kawo" "toh ina jinka" "Dama kanwarka na gani ina so, toh namata magana akan tabani numbern wayanta tace Mun ka hanasu rike waya nace Kona ummi ta bani tace yau zata kawo tace ta manta daga karshe tace wayan Ummin ma ya lalace haka dai take tamun yawo da hankali shine nace bari na biyo ta hannun babban Yaya nakama kafa". Gabanshi ne ya dan fadi kan yace "Wacce kanwan tawa?" "Wacce kazo ka amsarma Admission letter fateema Zahra" Numfashin shi ne yaso tsayawa yaji kanshi na juya mai saura kadan ya bigi wata mota yayi saurin taka birki Jin shiru bece komai ba yasashi cewa "Hello; kana jina" "Zamuyi magana" daker ya fitar da maganan, Yana Kai nan ya yanke wayan Kwana yayi yabi hanyan school din idanunshi sun kada sunyi jajir lip dinshi na kasa ya kama ya taune da karfi gudu yake shararawa amma be mai ba ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi cikin makarantan parking din dazeyi bakin gate ya hango Umaina, Ramlat da Aesha tsaye suna kallon iKon Allah Ita Kuma Muhibbah na gefe ta harde hannayenta a kirji ta zuba ma gefe guda idanu sauban tsaye a gabanta Yana mata magana bata tankashi ba ganin ta gaji da ganin shi tsaye gabanta yasa ta dan kara matsawa Shima ya matsa daf da ita kamar ze taba ta Besan lokacin daya balle murfin motan ya fito ba ya nufesu a zafafe................[11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYA KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *Page 47* Basu ji zuwanshi ba se saukan lafiyayyen mari da yaji a kuncinshi kafin yayi wani yunkuri ya kuma Jin saukar wani marin a mamakance ya dago yana kallonshi kamar ya daga hannu ya maida mai marin amma kallon kwayar idanunshi da yayi se yaga ya mai kwarjini Kuma ya girme mishi nesa ba kusa ba shidai kallonshi kawai yake yama kasa tambayar dalilin marin dan be san abinda ya aikata ba Jikinta ne ya hau rawa tsoro da fargaba suka mamayeta tana tsaye a gurin tsoro ya daskarar da ita kamar bishiyar da aka dasa ko motsi takasa Tinanin inda zata nufa kawai take data na da dama data tsere taje ta hau mota ta nufa Kano gurin iyye anan kadai take sa ran samun sauki amma tasan ko kd ta tafi bata tsira ba dan Daddy idan yaji labarin nan ba iya fada ba kilama ya ha damata da duka gidan Abba Kuma tana tsoron zuwa gudun akara samun matsala irin na kwanaki Rike su Umaina tayi tana furta "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un ku rikeni please yau munshiga uku kwanan mu ya kare, sister tajazamana bala'i seda nace tasanar dashi tun kafin ya gano da kanshi amma taki yau kashin mu ya bushe" se sambatu take tayi can ta dawo ji take kamar ta tafi tasha ta hau mota ta nufa kaduna nan kadai take tinanin zataje ta tsira daga mutuwar da take hangowa mararan tana nufosu Riketa sukayi Ramlat tace "Ke nutsu mana se kace wacce ta zare, wancan din waye?" "Ba gara ma na zare ba dasauki akan mutuwar da nake hangowa da idanuna, ya Fu'ad nefa seda nace ta fada mai tun da wuri amma taki saurarena, wllhi Kuma se Allah ku tsira" ta karashe maganan tana fashewa da kuka Duk shiru sukayi suna kallon iKon Allah su kansu sun tsorata ainun Da yatsa yashiga nunashi hannunshi har rawa yake "Uban wa yabaka izinin tsayawa da mata ta? Wa yabaka izinin yimata magana?" Daker maganan ke fita daga makoshin shi tsabar yadda ranshi yake a bace Shidai har lokacin kallonshi yake bema fahimtar abinda yake fada gaba daya kanshi ya juye tsabar tsoro "Wllhi idan baka fadamun uban daya baka izinin tsayawa da ita ba ka Kade idan ka bari na damkeka seka dena numfashi" ganin dagaske Fu'ad yake dasauri yace "Babu kowa, nasan dai sistern ta tafada mun tana da aure amma nayi tinanin wasa ne saboda a idanunta da jikinta da shekarunta basu nuna tana da aure ba" Wani shaka ya Kai mai idanunshi suka firfito waje yana yafara kokawa da numfashinshi yashiga kiciniyar kwacewa amma ina ya kasa saboda rikon da Fu'ad ya mai bana wasa bane "Dama matar aure kamanninta daban ne? Ko ana rubutawa ne a goshin su? Kai uban wama yabaka izinin Kallan mun mata da har ka kare mata kallo, kune samarin dake hure ma yaran mutane kunne ku hana su karatu su biye muku kuyita shirme ko?" saurin girgiza kai yayi yana kiciniyar kwacewa Saurin barin gurin tayi ta koma gurin dasu Aesha ke tsaye gudun yagama dashi ya cafkota gaba daya hantar cikinta ya kada zuciyarta bugawa take da sauri sauri kamar zata faso kirjinta ta fado Ita ko Aesha tsugunne take dafe da cikinta daya murde se kara yake kuuuuu kamar zata saki Kashi a wando Ganin ya galabaita har be iya motsi yasa ya sakeshi ya tureshi ya fadi kasa yana nunashi da yatsa "ko da wasa ka Kuma yima matata magana sena ga uban daya tsayama" yana Kai nan ya juya ya barshi kwance a kasa Mutanen dake tsa tsaye suna ba idanun su abinci sukayi saurin kama gabansu Gurin su Muhibbah ya nufa gadan gadan Aesha tayi saurin mikewa tana karama kukanta sauti ita ko Muhibbah kukan ma yaki zuwa tsabar tashin hankali seda Aesha tabata shawara amma taki da tasanar dashi da duk hakan bata faru ba duk takunshi kara tafiya da numfashin su yake zuciyoyinsu nakara tsittsinkewa amma tsoro da fargaba sun kafar dasu ko motsi sun kasa bare suyi yunkurin guduwa sun San ko guduwan sukayi ma basu tsira ba sema kara ma kansu laifi da sukayi
Chapter 46 · 0% Book details