Sashe 21
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
din, bata jima ba ta fito tayi sallah axuhur kafin tace Aesha tama me make up din iso, me make up din ta kure basirarta tayi musu make up me kyau kamar amare suka fito se tashin kamshi suke cikin shigar doguwar riga gown iri daya sak. Se 2 suka bar gidan suka nufa hall. Hall din ya kayatu anyi decoration dinshi da flowers ga light kala kala blue, sky, red, white, Tsayawa kwatanta kyawun gurin ma bata baki ne. Gurin da aka tanada domin su suka nufa kawayensu na biye dasu suna escorting dinsu seda suka zauna kafin kawayen suka dawo chairs din da aka tanada musu. Taro yayi taro guri yacika makil anata lashe lashe da tande tadande kowa murmushi kwance a fuskarshi banda muhibbah da tun dazu take faman duba agogon dake daure a damtsen hannunta karfe 6pm amma har yanxu Mukhtar be kirata ba bayan umma ta fadamata zatasa ya kirata tun safe take jiran kiranshi amma har yanzu shiru gashi su umman ma basu zo partyn ba Kuma har address din gurin ta turamata, kodai sun yanke alaka da ita ne?. Firgigif tayi ta dawo daga duniyar data tafi Jin MC nata Kiran sunanta, Hannu suka rike ita da Aesha, Summy da Khadija suka karaso sukayi escorting dinsu har kan step Nan Abba yatashi domin gabatar musu da gift dinsu ba karamin surprising dinsu yayi ba, kyautar sabuwar waya dal a kwali yabama ko wannesu tare da sarka da dan kunnen gold dukansu seda suka zubda kwala tsabar farin ciki Shima daddy ba'a barshi a baya ba yabasu nashi gift din kowa ya nuna tashi bajintar domin babu Wanda be bada gift dinshi a family ba hatta zarah ba'a barta a baya ba seda Aunty suhailat tamika gift din wani box me kyau an jera chocolate ciki tace na zarah ne, Shima gogan naku wato Fu'ad ya taka rawar gani be tashi ba amma ya aika an basu gift din wrist watch na zinari me hade da zobenshi sannan duk jakun kunan da aka raba a gurin shi ya dauka nauyi. Umman mukhtar da zarah ma ba'a barsu baya ba, mamaki ne yakama Muhibbah ganin su umman, dama sun jima da zuwa ita ce dai bata hangosu ba saboda taron jama'a. Muhibbah ta zubar da hawaye sosai ganin irin tarin kaunar da family ta suka nuna musu. Anci ansha an Kuma rausaya se daf magrib aka sallami kowa da jaka dasu memo. Taro ya tashi lafiya kowa ya koma gida a gajiye anayin isha'i a halin basu tsaya fira ba kowa yabi lafiyar gado, itama muhibbah baccin gajiya ne ya sureta tana jingine jikin bed ta Lula duniyar tinani bacci ya lallabo yasa ceta Jin wuyanta namata zafi ne ta silalo ta gyara kwanciyarta dakyau. Yana zaune a bed room suhail na gefenshi suna video call da abokinshi Jafar suna firan yaushe gamo Jafar yace "Wai abokina ya shirye shiryen biki ne, lokaci fa nata karatowa". Dogon tsaki yaja "Wai Kai meyasa kullum idan baka janyo munyi rabuwar rashin Dadi ba bakajin dadi ne?" "Ah daga magana daya shine har ka dau zafi haka?". Dariya Suhail yayi "kaidai bari Jafar nima kullum se nayi Mai magana akan shirye shiryen bikin nan amma yayi mun banza har nagaji". "kyale dan rainin sense so yake Muji kunya, Next week zan shigo se muga yadda za'ayi, amma idan muka biye mai baza'ayi abin arziki ba Kuma so muke ayi biki na gani na fada abinda da ba'a tabayinshi a kd ba mu kafa tarihi a Kaduna zuwa yolah". Shakiyanci suka shiga yimai amma yaki kulasu da yaga sun isheshi yayi hanging call din. A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah biki nata karatowa a halin se shirye shirye suke Mummy ma ganin batada yadda zatayi yasa ta saki jiki tanata sanar da 'yan uwanta ta bangaren ummi ma hakan ne ta saki jiki tanata shiri tana Kiran mutanenta na yolah tana fada musu bikin domin tun data kara samun Abba da maganan janye biki yayi mata tass tun daga nan ta runguma kaddara ta maida komai ba komai ba, ita ko Muhibbah a gurinta bata sauya zani ba kullum da damuwa take kwana take tashi tanata Kiran Mukhtar har lokacin be dauki wayanta ba Kuma batagaji da kira ba ko tamai message ta watsapp baya reply tun yana bude message din har yadena Kuma har lokacin bataji sonshi ya ragu daga zuciyarta ba ko kadan sema wutar sonshi da takeji yana kara ruruwa a zuciyarta. Suna zaune gaba daya gidan a parlourn daddy anata tattaunawa kan bikin kowa na tofa albarkacin bakinshi banda Fu'ad da Muhibbah cikin su babu Wanda yace kala. Har aka gan garo maganar tafiya hado kayan lefe da kayan daki, fir Muhibbah tace babu kasar da zataje su tafi su barta, da kyer da lallashi ummi da Abba suka shawo kanta ta yarda zata bisu. Bayan sun gama tattaunawan suka fita da Aesha siyo sweet da chocolate wani babban shago dake unguwar su, son yawo ya fitar dasu, suna tafiya suna fira har suka iso gida suna shigowa suka ci karo da Fu'ad batace Mai komai ba ta wuceshi se Aesha ce tayi mai sannu, har sun gotashi ya kirasu seda gabansu ya fadi dan sun San kiranshi ba alkhaeri bane a garesu, sunfi 10 minutes a tsaye kafin yace "Kneel down" da sauri suka zube. "Daga ina kuke?" Har hada baki suke gurin cewa shago suka fada suna ciro kayan dadin daga leda domin yatabbatar shagon suka je. Kallon dayasa cikinta kadawa ya watsamata yana nunata da yatsa "Keee tsabar kin rainani da kudina da ranana akanki zaki tsaya da wani Kato har ki biye mai kuna fira kina washe hakora tsabar kin rainani ko?" Runtse idonta tayi saurin yi dan bataji dadin kiran Mukhtar da Kato da yayi ba, Kai ta girgiza "Aa Yaya kawai gaisawa muk.." wani Kallon daya wurgamata ne yasata saurin hadiye maganar. Ku kama mun kunne, sunfi 20 minutes suna kama kunnen sunyi kuka harda majina sunata addu'ar Allah ya dawo da su Abba amma shiru basu dawo ba Aesha nata kunkuni a zuciyarta laifin Muhibbah ya shafeta bataji ba bata gani ba, Muhibbah ko ta tsine mai yafi cikin kwando a zuciyarta, Seda yaga sun jigata kafin yace su bace mai da gani, har rige rigen tashi suke suka kwada a guje sukayi ciki suka bar sweet din nan. Shirye shiryen tafiya suke tayi Mummy, Ummi, Suhailat, Aesha da Kuma uwar gayya Muhibbah duk da taki shirya komai se Aesha ce ta shiryamata kayanta, Ammar da Anas ma sun nace dasu za'ayi tafiyan. Bayan kwana biyu jirginsu ya daga zuwa Dubai............ *Toh mun tafi ayimana addu'ar dawowa lfy , Muhibbah tace ku fado abinda kuke so tayi muku tsaraba dg Dubai* *Muhibbah a sauka lfy* *Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: _*SOYAYYAR KWANA AYA*_ _BY_ _*FATIMA A MUHAMMAD*_ _AMINIYAR ANGONTA_ _*TEAM*_ _*ZAFAFAN DAWA*_ _*JARIRIYAR DAWA*_ _________________________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100087451774783 ________________________ *Page 28* *Shin kina neman inda xakiyi sari cikin sauki?, toh tawo 'yar uwa maxa maxa ki garxayo TEEMAH'S COLLECTION & MORE kantin sauki da rahusa suna bada sari ko siyan dae dae* *Sunada kaya kamar haka....* *Akwae atamfofi, less, abaya, veils, hijjabs shoes & bags.....* *Sannan akwae waist beads(jigida), bracelet, sarkar kafa na beads, beaded t shirt* *Ba iya Nan suka tsaya ba suna saeda candies kmr: gullisuwa, iloka, Ridi, tuwon Madara, chin chin, sunada special yaji uhmmm ba'a maganar dadinshi tested & trusted* *Sunada carrot vasiline Wanda xesa fatarki tayi laushi da sheki kinsan dae amfanin carrot, ga shampoo, room freshener, liquid soap, soap, sabulun tsarki na magarya dana miski, body spray, oil perfume, inner wears, night wears And many more......* *Teemah's collection & more* *sun shirya tsaf domin faranta ran customers dinsu siyan daya ko sari, Koda yaushe kofarmu a bude take Saturday to Friday 24/7 available, ku rikitamu da orders please we will take paracetamol *Wa/07088514846* follow this link domin ganin sample din kayanmu kae tsaye https://chat.whatsapp.com/Faz3ZelaaWpHhl30lyw6ZO?mode=ac_t A Sheraton grand hotel suka yada zango mummy da Ummi a daki daya, Suhailat Muhibbah da Aesha daki daya, Ammar da Anas ma daki daya, kowane daki room and parlour ne se toilet. Muhibbah ce tayi Mika tana fadin "innalillahi wa inna ilaehi raji'un Kai na gaji dayawa ina zamana aka sani biyoku da yanzu ina gida abuna" ta karasa maganan tana kwabe fuska kamar zatayi kuka. "Toh naga dai siyayyan nan naki ne domin ki fa muka tawo mu bamuyi complain ba seke zaki ishemu, to waye be gajin ba". Dan karamin tsaki taja "Kai wllhi Aesha kinada matsala, naga dai ban ambaci sunanki a magana na ba ko?" Ta karasa maganan da alamun tambaya. Kafin Aesha tayi magana su suhailat ta katse ta "Wai ku bakwa zama inuwa daya baku raba hali bane, daga sauka ko hutawa bakuyi ba kun fara Jan magana" tayi maganan tana nufan akwati dubo kayan da zata zira dan fitowarta wanka kenan. "Allah Aunty Suhailat yarinyar nan ne ta rainani kamar bani bace yayarta" ta Kai karshen maganan tana shigewa toilet. Seda sukayi wanka sukayi sallah kana suka nufa gurin su Ummi. Abinci sukayi order aka kawo musu parlourn dasu ummi suke sukaci bayan sun kammala suka kira aka dauke kwanukan nan suka dan taba fira kafin kowa ya koma makwancinshi saboda kowa tattare yake da gajiya. Ko washe gari dasuka tashi breakfast kawai sukayi suka ciga da baccin su, se bayan dasukayi la'asar kafin see suka fita domin su mike kafafu sun jima a waje babu laifi se gaf magrib suka dawo masauki. Yauma dai kamar jiya a parlourn dakin dasu Mummy suke suka yada zango har da su Anas anan sukayi dinner aka hau labarin irin al'adun dasuka gani Wanda suka Sha ban ban da al'adun Nigeria, Remote Muhibbah ta dauka ta canxa channel ta hau kallon cartoon. "Wai ke sister bakya gajiya da kallon cartoon ne har yanzu kina nan kamar baby bakya girma se anyi magana kice kin girmeni" "Kai Aesha kin cika sa ido, duk motsina kina nan kina kallo Kuma bakinki be iya shiru sekin tanka". Anas yace "Kudai kamar annabi da kafiri kuke da daya yama dan uwanshi maganar arziki shikuma seya maido mai dana tsiya" "Toh kaima ba haka kake ba