Sashe 47
Soyayyar Kwana Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani kallo ya watsa musu dayasa su kara firgicewa hada kawunan su gaba daya su hudun yayi ya gwara ji kake kuuuum kuka sukasa yayi saurin daura hannun shi akan lips "Shiiiiii! Inga wata ta Kuma kula saurayi a school din nan kuga yadda zanyi da ita har kuuu" ya nuna su Ramlat Dasauri suka gyada Kai "Ba bakuda kunya ba zan gyara muku zama" yana kai nan yayi kwafa ya nufa motarshi Dasauri suka mara mai baya har suna rige rigen shiga motan, seda ya kai kowaccen su gida kana ya juya motan zuwa gidan Ummi dan sanyi sanyi sukaji a ransu dan gara ya kaisu gidan ummi da ya kai su gidanshi a rasa me ceton su. su Umaina Kam seda sukaga an sauke su kan suka sauke ajiyar zuciya sunama Allah godiya se a lokacin son Jin tabbacin Fu'ad mijin Fateema ne dagaske ko wasa ya fado musu Wani abokinshi ne ya Mika mai hannu ya kamashi ya tashi suka lallaba suka koma cikin school din cikin motarshi yasanya shi ya Mika mai goran ruwa ya kafa Kai ya shanye tass kan ya yadda goran ya jingina bayanshi a kujeran motan yana faman maida numfashi "Sauban Kai Kam me ya hadaka da mutumin nan" "Bari kawai Al'amin kome ya faru laifina ne matarshi naje ina dating Kuma sistern ta tafadamun matar aure ce amma zuciyata taki aminta da hakan saboda a idanuna yarinyan she was too young ace tanada miji" ya Kai karshen maganan yana sauke wahalallen numfashi Bubbuga kafadarshi Al'Amin yayi "gaskiya kayi kuskure tunda har an sanar da kai tanada aure Koda ba gaskiya bane seka rabu da ita ko ka bibiyeta har katabbatar da gaskiyar lamarin kuma idan banda abinka yara nawa ne ma basu kaita ba ake aurar dasu" "Wllhi tun ranan dana dora idanuna akan yarinyan na kamu da kaunarta hakan yasa idanuna suka rufe akanta, sanin kanka ne 'yan mata suke bina a school din nan ina wulakantansu dan basa gabana amma ita Allah ya jarabceni da sonta, kuskure na riga nayi sedai a tari gaba" yafada Yana kokarin tada motar "Be kamata kayi driving a condition din da kake ba" exchanging seat sukayi Al'Amin yaja motar suka fice daga school din Ganin yayi parking amma sunki fita daga motan yasa ya juyo ya kallesu, Aesha ce ta yunkura zata tashi seta rike hannunta "Get out...." Yafada a zafafe Dasauri Aesha ta fisge hannunta ta balle murfin motan ta fice amma Muhibbah ko motsawa batayi ba "Zaman me kike ko bakiji abinda nace bane ki fitarmun daga mota" Kura mishi ido tayi har lokacin bata motsa ba duk da a tsorace take amma ta dake Hada idanun da sukayi yasa tsigar jikinshi tashi yaji tausayinta ya darsun mai yayi saurin dauke kanshi daga kallonta ya balle murfin motan ya fito Hannunta ya riko ya fito da ita daga motan ya nufi parlourn dakinshi na gidan ya nufa har lokacin yana rike da hannunta, Juyowa yayi ya Kalli Aesha da ke makale jikin bango kamar kadan garuwa tunda ta shigo taji babu motsin Ummi gabanta yakara faduwa yau sun Kade Koda a idanun ummi ne seya jibgesu kafin ta kwacesu seta shirya bare Kuma yanzu da babu motsinta ihun su banza Kallon da yamata yasa ta gane abinda yake nufi a sanyaye tabi bayan su har cikin dakin, yana Kai tsakiyar dakin ya saketa be ko juyo ya kalleta ba dan kallonta rauni yake sa mishi Tun kafin yayi magana suka zube "Kuba dama abinda kuke aikatawa kenan a makarantan?Kun raina ni ko yaushe nafara wasa da ku? Kusa a ranku kuda makaranta hai hata hai hata sedai kuga anayi " Yayi maganan yana nuna su da yatsa Cikin rawar murya tace "Wllhi bama kula kowa wannan ne kawai kuma shima na fada mishi matar aure ce amma yaki yarda tun daga nan babu Wanda ya sake yi mai magana, dan Allah kayi hakuri" Lips dinshi na kasa ya ciza da karfi ranshi na kara baci yadda ya ganshi tsaye daf da ita kamar ze tabata kawai yake dawo mai se yanzu yake bakin cikin kyaleshi da yayi ji yake kamar ya koma ya kwakule mai idanun da ya ke kallon mai mata dasu Kamar bazeyi magana ba can yace "meyasa baku fadamun ba" cikin rawar murya tace "Mun fadama Ummi tace kar mu kara kulashi" kanshi ya dafe wato ummi ma tasan da zancen ba'a kyauta mishi ba da an fadamishi tun tuni ya dauki mataki da duk haka bata faru ba "Malam mukhtasir fa?" "Yaya bansan ya akayi suka hadu ba" Kallon daya watsamata yasa a dan tsorace tace "ranan dana fara zuwa school ne naje Kai mai files office dinshi shine yace na bashi number na nace banida waya" ta karashe maganan cikin rawar murya "Saboda tsabar wulakanci meyasa baki fada mishi kinada aure ba? Raini ne ko me?" "Babu komai" tafada kamar zata saki kuka "Saboda banida amfani yasa kika kasa fadamun? Baki San miye aure bane? Ko ba'a taba fada miki dokokin aure a muslumci bane? aure na kika wulakanta saboda banida daraja a gurin ki ko" Ya fada a zafafe Yana mikewa dan ba karamin hassala yasakeyi da jin labarin tun ranan da ta fara zuwa school mukhtasir ke bibiyanta amma takasa sanar dashi yama tufkar hanci tunda wuri, tsawon watanni tana gara igiyoyin aurenshi kamar kwallo yanaji idan be dake su ba baze huce ba Ganin ya nufo su suka mike a zabure, baya baya ta fara yi zata kai kasa tareda sakin kara me sauti a razane ya karasa da sauri ya tarota "Lafiya? meya sameki?" Kokawa tashigayi da numfashinta ta idanunta a rufe ta Kuma sakin wani Karan "Keee! Heebbah meyasa meki? Lafiya kike kuwa?" Ya jero tambayan a kidime Jan numfashi ta cigaba da yi tana kuka me sauti kukan da tun dazu take dannewa "Wayyo Allah kafata" "Har yanzu kafar bata dena ciwo ba?" Ya fada cikin kulawa "Wayyo Allah Yaya kirjina" hannunshi ya Dora kan kirjin "Me yasamu kirjin naki?" "Zafi yakemun wayyo Allah na Mummy na kirjina ze cire" "Dama kina da ulcer ne?" Kai ta girgiza "Nima bansaniba, Yaya mutuwa zanyi" "Kidena ambaton mutuwan nan please bazaki mutu ba" yayi maganan kamar ze zubda kwalla duk ya rude ya rasa abinyi, tinanin shi yafi bashi ko ulcer gareta ita ce me tashi farar daya idan tazo da Karan kwana daya cikin minti 5 se kaji babu mutum Shafa kirjin yake a hankali hankali tashe "Stay with me please, kidena kiran mutuwar nan dan Allah "Aesha kawomun ruwa me sanyi" a sukwane ta fita da gudu gudu kamar zata kifa itama gaba daya ta kidime ciwo yanzu yanzu kamar iska ko kuma ciwon ajali................ *A lallaba da wannan* Aminiyar ango [11/17, 09:19] Aminiyar Ango: *SOYAYYAR KWANA DAYA* *FATIMA A MUHAMMAD (Aminiyar ango)* *Page 48* Kan kujera ta zube tana maida numfashi "Umaina lafiyarki kuwa kika shigo ma mutane a birkice?" Seda ta sauke ajiyar zuciya kan tace "Wllhi umma yau ya Fu'ad din su fateema ne ya ritsamu" "Yanzu haka wani shirmen kukayi" "Umma cewa yayi duk ranan da yakama mu mun kula wani namiji a school mun shiga uku, nan ta kwashe abinda ya faru ta fadama umma" Dariya sosai tayi "Yayi mun dai dai ai banji dadi da be hada muku da bulala ba" "Ae wllhi umma harda gwara mana kai yayi bakiji yadda kaina ke mun zafi ba" "Nidai ya Fu'ad din nan ya birgeni daya muku haka kwa fi maida hankali kuyi karatu" sun dade zaune tana bata labari kan ta mike tashige dakinta. ******** Ruwan Aesha ta mika mai ya karba da hanzari ya balle murfin goran yashiga bata wani ta hadiye wani ya dilalo kasa "Innalillahi wa inna ilaehi raji'un Hayatee bude idonki ki kalleni, ki fadamun abinda ke damunki please" duk ya rude ya rasa abinyi itama Aesha hankalinta ba karamin tashi yayi ba se kuka take Cilak ya dauketa ya daura kan bed ya hau gadon ya rungumota kan kirjinshi "Fatee bude idonki nine, yayanki ne dan Allah kitashi karkiyimun haka" idonta dake a lumshe take budewa tana lumshewa Mayafinta da tuni ya fadi ya Kalla "Aesha dauko mata hijjab dinki mu tafi asibiti" da sauri ta fice bata jima ba tadawo rike da hijjab din ya karba yana kokarin zira mata ta Kai hannunta ta rike nashi "Yaya karka wahalar da kanka nasan ko mun tafi asibitin ba lallai mukai ba" cikin tashin hankali yakara rungumota hawayen dake makale a idanunshi suka silalo Jin dumin hawayenshi a fuskanta yasa ta saurin bude idanunta tana kallonshi a mamakance, Ganin sun hada ido yasa tayi saurin maida idanunta ta lumshe. "Fatee! Dan Allah ki bari muje asibiti ki taimakeni kar tafi kibarni" yayi maganan yana karasa samata hijjab din Hannunshi ta rike Kam hawaye na silalowa daga idanunta "Babu bukatar zuwa asibiti nasan ko mun tafi ba lallai ku karasa dani ba sedai gangan jikina, Yaya mutuwa zanyi a yadda nake Jin kirjina na suya bana ji zan kara 15 minutes a duniya duk da babu Wanda yasan lokacin mutuwarshi amma yakan nuna ma wasu alama yayin da suke gaf da bankwana da duniya toh nima ina kyautata zaton ina daga cikin Wanda Allah ya nunamun lokacin mutuwa na Kuma wata Rahma ne tunda har nasamu daman rokon yafiyar miina, ban dibo shekaru masu tsayi ba iya lokacin da ubangiji ya debamun kenan, ka yafemun aljannah ta na karkashin kafarka idan baka yafemun ba zan tafi gaban ubangiji na yana fushi dani" ta karashe maganan tana fashewa da kuka Kara kankameta yayi "Zahrah wllhi na daga miki kafa indai aljannah ce kin dade acikinta amma ki taimaka karki tafi kibarni, miye amfani na a duniyan nan idan babu ke? kina tinanin idan kika mutu zan cigaba da numfashi ne? Wllhi idan kika tafi kika barni nima mutuwa zanyi bazan jure rashin ki a rayuwata ba rashin ki dai dai yake da datsewar numfashina kece mahadin rayuwata kece cikar muradai na" yana maganan yana kara shigar da ita jikinshi Yama manta da wanzuwar Aesha a gurin "Yaya dan na mutu babu abinda zakaji kaifa kafadamun kanada wacce tafini komai kama daga kan ilimi kyau har zuwa class toh me ze dameka dan na