← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 89

Sashe 87

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Jijjigashi sosai ta shiga yi tana kuka. "Ya Ayaan dan Allah kabude ido, na shiga uku, dan Allah karka mutu kaji bazan karaba" tashi tayi da gudu tai wurin kofa tana bubbugawa tana kiran sunan Mami amma shiru, dawowa cikin dakin tayi tana kalle kalle ko alamun key bata ganiba, sake dawowa inda yake tayi tana wani irin kuka ta tsugunna ta daura kanta akan kirjinshi tana kuka, dago kai tayi ta kalli fuskar shi tana girgixa kai tace "dan Allah katashi bazan karaba to" ko motsi bayayi, arude tace "ruwa, eh ruwa" da sauri ta mike tsaye tai bathroom awani bowl ta debo ruwan tadawo dakin tsugunnawa tayi akanshi ta watsa mai ruwan a fuska wani irin numfashi yaja yadan bude ido, da sauri ta dukar da kanta saitin fuskarshi tafashe da kuka sosai, hada ido sukayi ahankali yafara kukkule idon zai kara sumewa dan heart dinshi baya beating da kyau da sauri tai tapping fuskar shi cikin kuka tace "Ya Ayaan no, no dan Allah, karka kulle idonka, ina key dakin ina maganin ka suke na dauko ma eh?" kara tapping fuskarshi tayi ganin yana sake kulle ido tace "ina key dakin" da kyar ya iya daga idanunshi ya kalli drawer hakan yasa ta kalli inda yake kallo da gudu tai wajen ta jawo ta dauko key data gani ta dawo ta tsugunna akanshi, sake tapping face dinshi tayi tana kuka ahankali tace "ina maganin ka yake na dauko ma" da kyar ya iya bude baki hakan yasa takai kunenta saitin bakinshi, chan kasan makoshi yay magana ahankali yace "my room drawer" da sauri ta tashi tai waje ta sauka daga kan stairs tafita daga dakin duka tai part dinshi bude kofa tayi ta shiga bedside drawer taje na bangaren daman ta jawo bataga any abu magani ba dayan ta koma tana jawo na biyun taga wani dan akwati box haka baki dan karami an rubutu cardiothoracic ajiki ga kuma sunayen abun dabazama ta iya kiraba ajikin kwalin da sauri ta dauka ta bude akwatin dan tagani wasu gajerun allurai ne ajikin form din akwatin guda hudu harda ruwan alluran wani blue dashi ajikin alluran, rufewa tayi ta tashi da sauri tana goge hawayen ta tafita daga dakin, tana shiga shashin Mami tafara kwalama Mami kira jin shiru yasa tai dakinta kawai, tana shiga ta mayar da kofan ta rufe, tsugunnawa tayi ta kira sunanshi amma ko motsi baiyiba yasake sumewa, fashewa tai dawani kukan tadau ragowan ruwan dazu ta watsamai dan nishi yayi batare daya bude ido ba da sauri tai tapping face dinshi da kyar ya bude idon ya kalleta, box din ta nunamai tace "wanan ne?" budewa tayi ta dauko allura daya ta kamo hannunshi ta sakamai da kyar ya iya kama alluran da kyau yakai shi saitin heart dinshi tana binshi da kallo tana goge kwalla, chakawa yayi akan zuciyanshi ya danne kan ruwan ya juye aciki kafin ahankali ya zamo ya ijiye gefe yana kulle ido, da sauri ta duko da fuskarta saitain nashi sosai dan har hancinsu na gogan juna cikin kuka tace "dan Allah karka sake kulle ido kaji wlh am scared, kayakuri, am sorry" fashewa tayi da kuka tanamai sheshekan kuka a fuska, kasa magana yayi ya kamo hanunta yarike ya daura akan heart dinshi, ahankali taji yanda yake wani irin bugawa ahaka ma da taimakon alluran ahankali ta daura dayan hanunta akai tana girgixa mai kai hawaye na fita daga idanunta tace "am sorry" jawota yayi ahankali ya daurata akan jikinshi ya matseta sosai yana sauke ajiyan zuciya, ahankali taji bugun zuciyan nashi na daidai ta tun tana saurara tana sauke ijiyan zuciya har wani irin bacci yay gaba da ita.
Chapter 87 · 0% Book details