Sashe 59
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Da sauri Cp da dan sanan daya fizge Mullin daga hanunshi harda Baba Sulaiman suka rike gam gam, Baba Sulaiman yace "Ayaan are u okay" kokarin watsa dasu yake yana ma Aaman wani irin kallo shima Aaman kallon shi yake irin kallon wanne wanan Kuma, Abba ne ya karbe kulkin daga hanun nashi ya zaunar dashi da kyar ya zauna akan kujeran amma gabaki daya baida natsuwa ahankali Abba ke tofamai addu'a Cp kuma ya kalli su Aaman da har lokacin suke tsaye ga Bilkisu dahar lokacin ke tsaye abayan shi ta rike mai riga yace "ku zauna" Baba dai har lokacin yakasa daina kallon Bilkisu mamakin yanda tarike wani namiji agabanshi ko kunyar shi da tsoron shi ma da bataji ba shiya hanashi magana, he's totally shock, dauko file dinta dake kan table Cp yayi yazo har gaban Abba dake gayama Ayaan da kanshi ke kasa yana wani irin numfarfashi magana a kunne ya mikama Abba file din yace "gashi Alhaji medical record dinta ne, sanadi yar faduwar nan datayi tasami tabin kwakwalwa banda haka tasami memory loss" da sauri Ayaan yadago kai da jajayen idanunshi ya kalli Cp da sauri ya karbi record din ya bude file din yana duddubawa yana karanatawa hanunshi har rawa yake saida yagama karance wa tass sanan yadago kai ya kalleta tana kusa kusa da Aaman kaman zata shige jikinshi tadau teddy tanata jijjigata tana wasa, wani irin zafi dayaji zuciyarshi nayi yasa yaji wasu irin zafafan hawaye naso su xubomai, Abba daya gama karantan dan nashi tsaf ya mike tsaye murmushi kwance akan fuskarshi ya karasa gaban su Aaman ya mika musu hannu yace "mungode, mungode, ubangiji Allah ya biyaku, dan Allah karku cemin a'a kuzo muje gida munsa muku girki dan Allah ya'yana karkuce bazakuba" yay maganan yana kallon su harda Dr, sosai nauyin Abba ya kamasu hakan yasa yace "to Abba" Cp ya mikama police din daya shigo plain sheet da pen ya kalli Aaman yace "zaka iya suffan tamana samari biyar dasuka fito da ita daga bakin motar" dan shiru yayi saikuma yace "yea" nan ya dinga siffanta su police din na zanasu saiko ga sketch din fuskar su Abba ya karba yana kallo babu wanda ya gane cikin su daga nan Abba yace sutafi, mikewa yayi da sauri tamike itama tana kokarin rikoshi Baba ya daka mata wani irin tsawa. "Bilkisu kewai mehaka" dago kai tayi ta kalli Baba saikuma ta murguda baki tana bobboyewa abayan Aaman tace "ni sunana Ameerah ko sweetheart" baya Ayaan yayi zai fadi sabida wani irin jiri dayake dibanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Baba yace "kasan bata hayyacin ta karka ga laifin ta" ya kalli Aaman dake faman tureta daga bayanshi yace "kumu tafi yan albarka" murmushi yayi yace "to Abba" su Abba suka rike Ayaan suka fita dashi. Da sauri Aaman ya juyo ranshi ya mugun baci yace "d next time dakika rikeni ko shigewa jikinta saina mareki naughty girl" yay gaba da sauri tsabagen haushi, Dr ya kalleta yanda take goge kwalla ahankali yace "muje" murguda mai baki tayi tana goge kwalla tabi bayan shi suka fita daga office din. Suna kaiwa waje Aaman ya nuna mata motan su Abba yace "jeki shiga motan su Abba" kallon su Abba tayi yanda duk suka tsatsaya suna kallonta barin ma Ayaan kaman zai hadiye ta, ta murguda musu baki tace "oh'oh ni namu zamu shiga" murmushi Abba yayi yace "bakomi kabarta anan muje" da sauri tabude baya ta shiga sukuma suka shiga gaba Abba ya kalli Ayaan yanda yake kallon su ahankali yace "Boy control your heart kar zuciyan ka ta buga haba dan Allah zaka halaka kanka ne jibi yanda kirjinka ke bugu, let's go" bude mota yayi ya saka shi ciki sanan ya shiga shima driver yajasu sukabar wajen motar su Aaman biye da ita har gidansu sukai horn security yabude, sukai parking suka fiffito tana makale kusa da Aaman har suka je part din Mami dayake Big Mummy taje bikin yar kawarta sai Kalle Kallen gidan take tana washe baki tana kallon fuskar Aaman murya chan tace "sweetheart nanne garin namu" ko kallonta baiyiba, babban falon Mami Abba yamusu iso suka zazzauna tana kusa da Aaman, ahankali Mami ke saukowa daga sama cikin shiga ta alfarma idanunta akan Bilkisu dake zaune kusa da wani tana wasa ta teddy Ayaan sai kallonta yake kaman ya hadiye ta, su Abba ma duk ita suke kallo har gabanta Mami tazo zata rungumeta da sauri ta matsa kusa da Aaman tana make kafada hakan yasa Mami tace "Bilkisu" murguda baki tayi tace "Ameerah sunana" tai maganan kaman zatai kuka, kasa magana Mami tayi ta tsaya tana kallonta Abba ne yay jarumtar cewa. "batada lafiya ne Firdausi, je akawo musu abinci" tadade tana kallon Bilkisu gaisuwar dasu Aaman kemata ne yasa ta farka ta amsa musu tana murmushi kafin ta juya tai kitchen nan tasaka yan aiki suka wadata su da abinci da abubuwan sha amma sun kasa ci sabida kunya drinks kawai suka sha shidai Ayaan jingina yay da kujera ya lumshe ido kaman mai bacci amma Bilkisu yake kallo bakaramin daurewa yayiba danji yake kaman ya kashe wanan mutumin datake ta manne mawa, Abba ne yay gyaran murya yace "godiya zan kara muku yarana yanda kuka taimaka mana kuka taimaki yarmu kuka sakamu acikin farin ciki ubangiji Allah ya faran ta muku haka ranan gobe kiyama" ya nuna malam yace "wanan shine mahaifin Bilkisu, ga Sulaimanu shikuma kanina ne, nikuma nine mahaifin mijin Bilkisu" wani irin bugawa kirjin Aaman yayi kafin ya farka daga hakan Abba yanuna Ayaan dake kusa dashi yace "gakuma mijin ta nan" saiya nuna Mami dake zaune gefen Baba Sulaiman yace "ga mahaifiyar shi chan" innalillahi wa innalillahi raji'un kawai Aaman ke ambata aranshi, da hikima batare dawani ya lura ba yakara matsawa daga kusa da ita yanda ta shige mai, wani irin zafi zuciyarshi keyi wasu irin hawaye masu dumi ne suka taru a idonshi ya saci kallon Dr da shiyake kallo shima, ahankali ya girgiza mai kai hakan yasa ya hadiye hawayen da kyar ya kakalo murmushi yadan kalli Ayaan aranshi yace no wonder dazu yayo kanshi baikawo komi dazu ba dan yazaci hala mutumin ya dauka sune suka saceta saisa yay haka ashe shine mijinta, ashe Ameerah matar aure ce, maganar Bilkisu ce yasa yadawo daga dogon zancen zucin dayake ta matso kusa dashi sosai tana nunamai pin din gyalen da Ummy tasaka mata takama rolling gyalen dashi ashagwbe tace "Sweetheart remove it for m..." bata karashe maganan ba sabida wani irin mugun tari daya turnike Ayaan akaro nabiyu da sauri Abba ya dau goran ruwa ya bude yabashi ture ruwan yayi azuciye yanaso ya mike tsaye Abba ya take kafarshi yasan halin danshi koba komi shiya taimaketa kuma Bilkisu bata hayyacin ta. "sweetheart plz cire" takara matso da kanta tanaso tamai kuka da sauri ya mike tsaye ya kalli su Abba yana kakalo murmushin dole yace "zamu koma yanzu karmuyi dare" kafin Abba dasu Baba da Mami dasuka Mike tsaye suma suyi magana Bilkisu tace "yeee zamu tafi, uhnn sweetheart fitsari nakeji jirani nayi" saikuma takara matsowa kusa dashi tace "where is d restroom" da kyar ya tattaro kalaman dake bakinshi dayay nauyi sosai ya nuna mata Mami yace "ga Mum nan je ta kaiki kiyi" kallon fuskarshi tayi jin yanda yay magana saikuma ta washe mai baki tace "okay wait for me" ta sakamai teddy ta ahannu tace "hold my teddy" da sauri tai wurin Mami dake kallonta ta washe mata baki tace "Mum muje" hanunta Mami takama suka hau stairs sai juyowa take tana kallon Aaman tana washe baki har sukai sama da kyar ya kakalo murmushi yace "mutafi Abba kafin tafito" rakasu su Abba sukayi har waje suka karbi number su shidai Ayaan yana zaune falo suna fita ya mike da kyar yay upstairs yay dakin Mami yabude kofa ya shiga Mami ce kadai adakin zaune tana jiranta tana ganinshi ta mike tsaye tai murmushi tace "bari naje nahado mata abinci bataci komiba" tafita daga dakin, kimono ta da gyalen ta dake kan gadon yabi da kallo ahankali ya zauna akan gadon yadau kimono ya rungume sosai yana shakan kamshin dasuke fitarwa, karan bude kofar bathroom dayaji yasa ya zame rigan daya fuskarshi bama ta lura dashi ba tafito tana kokarin jan straight skirt dinta data tattare ta barshi a cinya zuwa kasa, tundaga kai yake kallonta har yatsa, kallon black body hug din da tasa yayi ba karamin kyau yamata ba gashi ya kamata yabi jikinta hakan saiya kara bayyana cikan kirjinta dago dakai tayi bayan tagama jan skirt din yakai kasa ta kalleshi bata damu da ganinshi ba amma ganin rigan ta da gyalen ta a hanunshi yasa ta daure fuska a tsiwace ta rike kugu tana hararan shi, dan lumshe ido yayi yakara budesu ya sauke akan fuskar ta, cike da masifa tayo cikin dakin agaban shi ta tsaya ta murguda mai baki ta mikamai hannu tace "bani rigana aiba naka bane, sweetheart yasaimin" wani irin fizgota dayayi saida tafado jikinshi, gyara mata zama yayi ajikinshi tana mutsu mutsun ta sauka ya sakala hanunshi ta bayanta ya riketa gam yana numfashi da sauri da sauri yana kallon kwayar idonta, murguda mai baki take iya karfin ta tana kokarin kwace kanta ganin takasa yasa tace "leave me" tai maganan tana kokarin kwace kanta, ganin yaki sakinta sai wani irin kallo dayake yasa ta daddage takai bakinta saitin kafadar shi ta daddage ta sakinmai cizo mai shegen zafi da kanta tasaki fatar tashi ta dago kai tana kallon fuskarshi ganin ko gezau baiyiba ita yake kallon har lokacin idanunshi sunyi jajir, ahankali yadaura kanshi akan kirjinta wlh takusa suma ya kankame ta sosai muryan shi nawani irin rawa yace "am sorry wife, am sorry, I've done alot of things to you, please kiyafe min am sorr..." yakasa karashe maganan sai kuka, cusa kanshi yayi a kirjinta sosai yafashe da kuka irin wanda daga shi sai ita zasu dinga jin karan, duk hankalin ta yatashi me haka wanan mutumin yakeyi yawani daura kanshi akan nonon ta yana kuka, jikinta nema yafara rawa tasa hannu tana ture kanshi tace "leave me, let go off me" dago jajayen idanunshi yayi ya kalleta dasu, kara ware ido tayi ta bude baki tana kallonshi cike da mamaki hawayen data gani, ahankali takai karama yatsar ta ta dangwalo hawayen dake gangarawa kuncinshi ta kalla hawaye ne da gaske ware ido tayi tace "laaaa dama babba na kuka, nidai ka sakeni kai, I want to go, mehaka mtsww" tai tsaki tana ballamai harara, wani irin kuka dayaji yasake zuwan mai yasa yasake maida kanshi jikinta ya rungumota sosai kaman zai maidata ciki yace "am sorr..." sosai yafashe da kuka yakasa magana, shi kadai yasan yanda yakeji aranshi. Tureshi ta shiga yi dukta rude tafashe da kuka sosai ta kwala ihu. "wayyo Allah na Sweetheart come" dago rinannun idanunshi yayi yasa hannu ya buge bakinta, kama bakinta tayi tafashe da kuka sosai tana kokarin tashi daga jikinshi, hanunta yakama ya daura akan kirjinshi dudda kukan datake saida yanda taji kirjinshi na wani irin bugu ya bata tsoro, rungume ta yayi sosai yakai bakinshi saitin kunenta da muryan shi da bata fita sosai yace "please wife karki kara kiranshi sweetheart wlh zan iya mutuwa yanda zuciyata ke zafi" tureshi tayi da karfi cikin kuka ta make mai kafada tareda lankwashe kai tana hararan shi tace "saina kirashi din, Sweetheart dinane kuma kabani rigana naje wurin sweetheart mutafi gidan mu" wani irin tari yafara yana dafe kirjinshi yana kallonta, zaro ido tayi atsorace tana kallonshi yanda yake tari, sadaf sadaf ta tako tazo gabanshi zata zari rigarta dake kan jikinshi ya rike mata hannu ya fizgota dawani irin karfi yana tarin yafada kan gado kaman zai mutu yakeji ya matseta sosai ajikinshi bama ya iya bude ido da kyau, sama sama ma yakejin metake cewa da kyar ya daga fuskar ta ya lalubo bakinta da hannu kafin ya dago kai idanunshi a lumshe ya kamo bakin yafara kissing dinta tareda kamata ajikinshi tightly yana shafa bayanta dayan hanunshi kuma yafara yawo agaban rigarta yana neme neme dan baya gani sosai tsabagen yanda yakejin asaba a zuciyar shi.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦