Sashe 25
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai bayan sallan la'asar dan lokacin hartai sallan la'asar har an chanza mata kaya wanan karan amtapa ne ajikin ta milk colour anmai kwalliyan black ajiki, wayyo Allah bakaramin kyau Bilkisu tayi ba tasa takalmin dazu baki da gyalen da jakan tana zaune cikin su Walawa daketa mata tsiya Baaba da wata kawarta sukazo gidan, gyalenta suka saka mata sukai mata lullube sanan suka kalli kawayen Baaba tace "kudan bamu aronta" suka fice tana biye dasu abaya har gidan Baaba da babu mutane saidai su Mama, Umma, da bakin dazu na kano datake iya hangosu ta huji hujin gyalen dake jikinta, sallama ababban falon Baaba taji Baaba tayi ta shiga da ita ta zaunar da ita kusa da mutum dabata san kowaye ba, saikuma taji Baaba ta cire gyalen daga kanta ta maida mata dashi kafada kafin tajuya tafita daga dakin, tasami su Mama dasu Mami da ita suke jira duk suka fita daga gidan dan komawa gidan su, kana ganin fuskar Mami kaga farin ciki lullube akan fuskarta, Baba dashi kadaine zaune adakin da Ayaan da aka ijiye Bilkisu kusa dashi dan su Abba basu dade da fita daga gidanba sunje dauko wasu abokan shi daya kira ya fadi musu zancen auren Ayaan, ajiyar zuciya Baba yayi yana tausayin yanda ma zai fadama yar tashi abinda Isyaka yayi hakanan dai ya tatataro jarumtar shi ya fuskanceta yakira sunanta "Bilkisu" dago kai tayi ta kalli Baban nata tace "na'am Baba" yace "inaso ki zama jaruma mai karban kaddara aduk yanda tazo mata, karki sa komi aranka ki dauka komi yafaru ne ayanda Allah yakeso, ahaka Allah ya tsara tun kafin ma a hallice mu" yadanyi shiru kafin ya nisa yace "yau awurin daurin aure Isyaka ya tashi agaban kowa" saikuma yay shiru kafin yay murmushi me ciwo yace "yace yafasa auren ki baya sonki yajuya yama fita daga masallacin abinshi" tunda yafara maganan ta dago kai take kallon mahaifin nata badadan shi bane ke gayamata maganan nanba da wlh zata iya cewa karyane Isyakan ta bazai taba yimata hakaba, yace "bazai aure kiba, shine dama mahaifin Ayaan yataba zuba nemama danshi auren ki lokacin ankusa bikin ki da Isyaka, shine yau bayan abin yafaru Ayaan yace shi abashi yana sonki shine nasa aka daura auren ki da Ayaan ga sadakin ki nan" ya daura mata kudin ajiki, kaman ma bata duniyar nan haka takejin ta Isyaka yace bazai aureta ba, andaura mata aure da Ayaan din dabama tasan wayeshi ba, dan bilhakki takara manta wani Ayaan, Isyaka na ne yace "bazai aureni ba?" da sauri ta kalli Baba da rinannun idanunta dasuka cicciko da hawaye dan shima ita yake kallo tace "Baba Isyaku nane yace bazai aureni ba? Menamai Baba, wlh banmai komiba dan Allah kace yayakuri Baba" tafashe da kuka sosai kaman zata mutu, Baba ya girgiza mata kai yace "i shiru ki manta da zancen isyaka danke matar wani ce yanzu, nasan ban kyauta miki ba dan banji ta bakinki ba, amma a matsayina na uba zan iya zaba miki miji nagari daga ganin Ayaan yaron ne dan gidan arziki, ga mahaifin shi da kirki da daraja musulmai, nariga na musu bayanin jarabawan da zaki zana sun amince daki zauna agida bayan gama jarabawan saiki tare, yanzu dai bari na barku tare kudan tattauna ni natafi wajen su mahaifin ka" yay maganan yana kallon Ayaan da kanshi ke kasa tun dazu, dago kai yayi ya kakalo murmushi yace "to Abba" Baba yafita yana kallon Bilkisu dake wani irin kuka dake tabamai zuciya gidan yarage daga shi sai ita.
Baba nafita tamike tsaye zata fita dan bama tason ganin koma waye mijin da Abba yace yamata, hanyar fita daga dakin tayi cikin kuka fuuu taji an wani irin fincikota danhar saida gyalenta yafadi kasa saura kiris tafada kanshi amma ganin wanda take shirin fadawa jikinshi yasa ta dage ta tare kanta tafadi agabanshi tana kuka, wanan mugun Baba ya aura mata dama, wutsiyar hanunta daya kama tabi da kallo, hawaye masu dumi suka zubomata tafara kokarin fizge hanun nata amma yaki sakinta saima wani irin matsiyacin kallo dayay yace "Ke! bazaki natsu ba" ko kallon shi bataiba saima daddagewa data keyi zata fizge hannun, hannun yabi da kallo ba karamin kyau lallen yayiba barinma yatsunan ta da dogayen kumbunan ta da aka zagaye su da ja, yasake mata wani irin kallon yadanyi murmushin gefen baki yace "bakiji dadi bama na taimaka miki? Wanan kazamin yaron yace baya sonki shine nace ni bari indan rufamiki asiri sabida tausayin mahaifin ki danaga hawan jini yana neman kamashi za'ai abun kunya, shine na taimaki rayuwan ki inda bahaka ba mezanyi dake jibeki fa dan Allah" wani irin bakin ciki da maganganun shi yasa taji yasa ta daddage taja wata shegiyar tsaki. "mtswwww" fizgota yay wanan karan saida tafado a kirjinshi, gabaki daya hanunta daya rike yamaida shi ta baya ya lankwasa hakan yasa tai wani irin ihu. "wayyo Allah Mama zai kasheni" tafashe da kuka mara sauti jikinta ko ina rawa yake, dan lumshe ido yayi jin yanda numfashin ta na kuka ke sauka akan fuskarshi kafin ya budesu ya sauke akan hawayen dakebin kuncinta ba kakkautawa ya daure fuska tamau tareda sake matse hannun tabaya ihu tayi sosai har saida ta bankare ta daura dayan hanunta akan kafadarshi duk cikin azaba, hanun yabi dawani irin kallo da sauri ta janye tana kuka sosai tana yarfe hannun harda shesheka, sakinta yayi tareda tureta harsaida ta fadi akasan wajen ta tashi ta zauna da sauri ta kamo hanun daya kama tana kallon yanda yay ja takara fashewa da kuka tana hurama hanun iskan bakinta dan zafi yake mata, tsaki yay yafita daga dakin, akofar gidan yaga su Abba da abokanen shi dasuka zo tareda Malam ya gaidasu sanan yaja Abban shi gefe kaman zaiyi kuka yace "Pops am going to the hotel nidai nagaji wlh i need to sleep" da sauri Pops yataba kanshi yace "shikenan Mah Boy jeka huta muma dasu maman ka Anjima bayan Isha zamu dawo hotel din, gobe da safe zamu dawo akara gaishe gaishe da sanin juna kafin mu wuce kano ko" gyada kai kawai yayi yawuce ya shiga mota yaja yabar wajen.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
31 - 32
Anan falon Baaba taci kukan ta ta koshi, ji take kaman tahadi yi zuciya ta mutu maisa Baba yamata haka tunda Isyaka yace bayayi basai abarta ba anwani hadata da wanan basamuden mugun, ahaka bacci yay awon gaba da ita a wurin.
Hayaniyan dataji yatada ita daga baccin daya dauketa Baaba tagani zaune da wasu bakin gidansu dasuka zo daga kauye anata hiran rabon kudin da Abba yay tayi, fashewa tai da kuka hakan yasa suka lura ma tatashi Baaba tace "hakuri zakiyi ai Isyaku duniya ce tanada girma yama kanshi, ki yakuri ba gashi Allah ya musanya miki ba mai sonki wanda kika taimaka, ni wlh inxakiji ta tawama kinfi dacewa dashi, tashi kije kiyo salla kici abincin ki karfe sha biyu fa" tashi tayi ta karbi toculan da Baaba ke mikamata ta karba tafita daga dakin ta wuce yo alwala.