← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 89

Sashe 74

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yafi minti biyu kallonta yake wani irin sonta na ratsa kowani jijiya na jikinshi, dan gyaran murya yayi da sauri daga Nurse Sameera har ita suka dago kai suka kallai da gudu ta mike tana kuka tafada jikinshi ta kankame shi tsam tsam tana kuka sosai da sauri Nurse Sameera ta mike kanta akasa tana murmushi tace "tundazu ta tashi takicin abinci nazaci na dakin ne bata so na aika aka siyo mata a Mr biggs shima takici sai kuka takeyi taki cemin komi kuma, tunda kadawo bari natafi" dan murmushi yayi yace "thank you so much nurse Sameera" murmushi tayi tace "bakomi Dr" tabude kofa tafita daga dakin ta rufo musu, sai alokacin yay hugging dinta back tightly kafin yafara tapping bayanta alamun tai shiru, dago kanta tayi daga jininshi ta kafeshi da jajayen idonta dake tsiyayar da hawaye, ahankali ya bude ido shima ya kalleta, dukan kirjinshi tahauyi tana kuka sosai, da kyar ya daga hannu yakama hanunnata yahada da nashi yana girgiza mata kai yama kasa magana, shigewa jikinshi takara yi sunkai 2min ahaka sanan yaciro ta daga jikinshi yaja hanunta sukai cikin dakin akan gado ya zauna ya zaunar da ita a gefenshi, hanun yasa ya share mata hawayen dake zubowa ya girgiza mata kai ahankali yace "am sorry nabarki nafita ko, stop crying zokici abincin ki" abincin ya dauko ya daura akan jikinshi yadau spoon ya debo yakai bakinta budemai tayi tana kallon idonshi tanaci haka yadinga bata fuskarta kadai nasa shi kwanciyar hankali, saida ta koshi ta karbi spoon din daga hanunshi da sauri ta debo itama ta kaimai baki tana washe mai baki, bude mata yayi ahankali yana kallon fuskar ya karba yaci dan yasata farin ciki amma ko kadan bayajin dadin abincin abakin shi, da sauri tasake debowa tana wani irin washe baki tsabagen murna takaimai bakinshi tana kallonshi, wani irin zuciyar shi keyi, kasa bude baki yayi hakan yasa tasake matsowa tana budemai bakinta alamun yabude baki tasaka mai, wani irin rawa zuciyar shi tafara na kuka sake tunamai da Pops datayi dan dayana yaro haka yakemai in yana rashin lafiya yakicin abinci, da sauri ya ture spoon din ya jawo ta yasaka ta ajikinshi ya fashe da wani irin kuka, da sauri tafara kokarin fizge jikinta daga nashi jin yana kuka hakan yasa yasaketa ahankali, kallon fuskarshi tayi ganin yanda yake kuka yasa ta kwaye fuska zatai kuka itama cike da damuwa, da sauri ya girgiza mata kai yana goge hawayen dayake, da sauri ta zauna akan cinyarshi tasa hannu kaman yanda yamata dazu ta share mai hawayen duktai wani irin da fuska rungume fuskarshi tayi hawaye nataru wa a idonta tana shafa kanshi nakusan 1min saikuma tasake shi ta dago kanta ta kalleshi dan tabbatar daya dena kukan, murmushi yamata asanyaye, sake washe mai baki tayi tasake rungume shi saikuma tasake shi ta sauka daga kan jikinshi ta mike atsaye agabanshi tana kallon fuskarshi shima ita yake kallo a sanyaye, hannayen ta ta daura akan kafadar shi tana washemai baki ta dugo da kanta ahankali tana kallon kwayar idonshi shima ita yake kallo kaman yau yafara ganinta, daura lips dinta tayi akan nashi da sauri ya chapke tareda rungumota jikinshi sosai yana wani irin sauke ajiyar zuciya, daukar ta yayi chak ya kifata a gado yasa hannu ya zuge mata zip din doguwar rigan ya cire doguwar rigar ya yar shima cire kayan jikinshi yayi yahayo gadon, da sauri tafada jikinshi ta kankame shi sake hada bakinsu yayi yana wasanni da ita kafin ya shige ta yana yanda yaga dama da ita.

Wuraren goma ya shigo garin kano, taxi ya dauka ya bashi address din hospital din da Ayaan yatura mai, goma da kusan 15 minutes taxi yay parking a hospital din, ya shiga yana kalle kalle ahankali yaciro wayarshi yay dailing number Ayaan amma ba'a dagaba akaro na uku ya dauka murya chan kasa yace "please kabani 10min am coming" bai kawo komiba Aaman yace "okay ina reception" , dagata yayi yakaita bayi wanka yamata agurgurje yafito yana tsane gashin kanta da towel sai kallonshi take, dan murmushi yamata, yamata kiss a kumatu yace "thank you, Allah miki albarka kin sa nasami natsuwa" hanunta ya daura akan towel din ya dauko mata wani bakin doguwar rigan Abaya ya shiryata tsaf yasaka mata dogon hijabi daya kai mata guiwa pink, yasaka mata loafers sai kallonshi take sanan shikuma ya shirya cikin Jean da riga white yasaka takalmi yadau jakarta da magungunan ta yadawo yarike mata hannu yace "let's go" fita sukai daga dakin, a reception yaga Aaman zaune yana danna waya, kaman ance ya dago kai ya gansu suna tahowa hanunta cikin nashi da sauri ya kori abinda kemai yawo a ranshi ya mike tsaye yana dan murmushi.

Hannu Ayaan yamika mai suka gaisa da ido yamai alamu suje waje, wajen motar shi sukaje, ahankali Ayaan yace "duk duniyar nan a yanzu kai kadai nai trusting, koda yau na mutu nasan tana good hand, please ga wife inaso kabar garin nan da ita harsai naci nasaran kubutar da iyayena bazan tsaya jiran police ba" bai jira mezaice ba yajuyo ya kalli Bilkisu da shi taketa kallo, cupping face dinta yayi ahankali yace "Baby follow him he's going to take care of you for me kinji, be a good gurl, I love you so so much wife" lumshe ido yayi da sauri, patting kafadar shi Aaman yayi ahankali yace "I can stay with you lemme help you Bro, inada wata sister dake aure a garin nan zamu iya boyeta a gidanta" girgiza kai Ayaan yayi yace "kai nakeso ka kulanmin da ita, I want her out of kano, I don't want to risk her life in anyway tana last stage na recovery ne, please please take care of her for me" da sauri yay wurin motar shi baya ya bude yasaka jakarta ya rufe yadawo yana mata murmushi yakaita gaban mota yace "kibishi zanzo na daukeki don't cry okay" washe mai baki tayi, ahankali ya sumbaci gaban goshin ta yasaka ta aciki ya kullo yadawo inda Aaman yake a tsaye sai binshi da kallo yake hanunshi Ayaan ya kama ya saka key mota da magungunan ta yace "once kakai kabata magungunan nan twice a day ne bacci yake sata, ga key kayi parking motar a Airport leave d key with security, I will never forget dis favor" da sauri ya juya zai wuce Aaman ya kama hanunshi, ahankali ya tsaya chak batare daya juyoba zagayowa ta gabanshi Aaman yayi yay hugging nashi yana buga kafadar shi yace "all d best, I promise to take care of her, Allah yabaka sa'a, ya kubutar dasu" Ameen Ayaan yace yana kokarin hana kanshi kallon motar, ahankali Aaman ya sakeshi yajuya ya bude motar ya shiga, da sauri ya juya baya bayason ya kalleta dan kuka zaiyi, Aaman yaja motar sukabar asibitin.
♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦

Maman Abd Shakur

86 - 87

Har suka shiga titi waige waigen shi take hartazo tadena ganinshi, kuka tafara mara kara ahaka har sukakai airport yay parking motar yaciro jakanta ya zagayo ta inda take kukan ta ya bude mata kofar yana kallon ta, ahankali yace "fito" fitowa tayi tana kallen wajen tana kuka saikuma ta kalleshi tafashe da kuka sosai, girgiza mata kai yayi cikin muryan lallashi yace "stop crying gashinan zuwa, zomuje, goge hawayen" share hawayen tai da sauri, yabama security key suka shiga cikin airport din booking yay musu kafin suwuce departure hall dan, in 15minutes time jirgin su zai daga, zama sukayi yaje yasiyo mata popcorn yakawo mata karba tayi sai jujjyawa takeyi tana kalle kalle saida aka fara boarding sanan suka wuce suka shiga jirgin, jirgin yadaga sama.
Sha biyu daidai na rana jirginsu ya sauka a Abuja Ummy ne tazo da Mota daukan su tana ganin Bilkisu da gudu tazo ta rungumeta tureta tayi tanason tafara kuka ya harari Ummy yace "ke kirabu da ita batada lpy, ban key" mikamai key motar Ummy tayi bayan ta kama hanun Bilkisu dahar tafara kuka, karba yayi ya shiga gaban motar Ummy tabude musu baya suka shiga ta rufo sukai gidansu dake wuse. Hadadden gidane babba sosai koda sukakai baiwani sha wahalan shawo Kan Mum dinsu ba, bakaramin tausayi Ayaan din ya bata ma tai musu addu'a sanan ta lallaba Bilkisu da kyar taci wani abu Aaman yakawo maganin ta Mum tabata tasha Sai kuka take, sanan Ummy takaita dakinta cikin minti biyu bacci yay awon gaba da ita, fitowa Ummy tayi hakan yasa Aaman yace "where's she" zama tayi kusa da Mum tace "tai bacci" Dan ajiyan zuciya ya sauke sanan ya kalli agogon hanunshi yatashi ya kalli Mum yace "bari naje, zan kai Usaida hospital zamuje muyi blood test su genotype and d rest" murmushi Mum tayi tace "saika dawo son" ficewa yayi daga gidan bayan ya Kira Usaida yace mata ta shirya.

**************
Da saurin shi ya shiga office dinshi yana share kwalla wani irin kewanta da shaukin ta ke shigan shi sosai, gadonsu ya kurama ido dan gani yake kaman zai ganta, kayan jikinshi yacire ya shiga bayi yayo wanka yana fitowa ya shirya cikin wani bakin riga bodyhug da bakin wando bakaramin kyau yayi ba kayan sun fito da hasken fatarshi sosai, sneakers yasaka yadau wallet da waya yafice daga office din bayan ya kulle, taxi yatare ya shiga.

******************
Chapter 74 · 0% Book details