Sashe 53
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dan juyo dakai yayi ya kalleta nayan sakanni yana nazarin abinda Dr yafada, gashi tawani labe abayan shi tana wani zazzaro ido, yujawa yayi ya kalli Dr Aminu yace "Man come and examine her please" ya matsa gefe da sauri tasake binshi kaman zata shige jikinshi hakan yasa ya juyo da niyar mata masifa ganin yanda take kallonshi yasa yakasa ya nuna mata bed yace "sit" make mai kafada tayi kaman zatai kuka tana shafa cikinta tana kallonshi da sauri ya dauke kai yace "menene?" da kyar tace "yunwa" juyo dakai yayi ya kalleta yace "sit lemme get food for you" zama tayi ya juya zaiyi wajen Dr Aminu daketa kallonsu da gudu ta mike ta bishi hakan yasa ya tsaya chak tareda juyowa, shagwabe mai fuska tayi Dr Aminu yace "u know something, sata ta zauna na dubata tukun" baice mata komiba yay wurin gado ya zauna abakin gadon da sauri itama tabiyo shi ta zauna abakin gadon tana haki, Dr Aminu yadau stethoscope daya ijiye akan fridge din dakin ya maida wuyan shi yana zuwa wurin su, ihu tayi ta koma kusa dashi sosai ta rikemai riga da hannu daya tana nuna Dr da hannu daya, ahankali yasa hannu ya fizge rigarshi data rike da kyar yace "hey calm down" ya mika hannu ya riko Dr Aminu yace "he's my friend, babu abinda zai miki, Dr kine so don't be afraid okay" gyadamai kai tayi tana kwalalo ido tana kara mamatso wa kusa dashi, saida ta rike hanun rigarshi gam gam sanan tabari Dr Aminu ya dudduba tareda cire mata bandejin kanta ya chanza zuwa plasta yasa adaidai wurin ciwon sanan yay mata murmushi ganin yanda take yatsine fuska alamun zafi yace "wai Barrister zaka sha aiki anan wlh" yadau byro yana rubuce rubuce sanan ya mikama Aaman, fizge hanunshi yayi ya mike tsaye da sauri itama ta mike ya karbi takardan, Dr Aminu yace "zaku iya tafiya da ita na sallame ku, memory loss dinne dai banda haka brain dinta yabugu dan haka zakaga tana abubuwa sai ahankali, yanzu dai ran Wednesday zaku dawo ranan ne likitan brain din asibitin nan ke zuwa zai dubata nasan zai mata memory loss test sabida ya gane if long term memory loss ko short term ne, tasamu daganan saiya daurata akan medications in sha Allah she will be fine, but u need take extra care of her gaskiya" shiru Aaman yayi yana kallonshi ko motsin kirki yakasa, ahankali Dr Aminu ya dafashi turo baki tayi tasa hannu ta ture hanun Dr Ameenu daya daura akan kafadar shi dukansu atare suka kalleta, turo baki tayi tana kallon Dr saikuma ta kalli Aaman ta washe mai hakora da sauri ya dauke kai ya kalli Dr, Dr Aminu yace "i know wat u are thinking amma karka damu duk mai taimako baya tabewa, dazaran ta warke saika kaita wajen iyayen ta kaga yanzu idan ka barta wat if mutanen dasuka so kasheta sukazo suka karasa ta? Gwara ka tafi da ita chan farm house din for now inyaso ai zaka iya kiran gida chan Abuja Ummy tazo hutu, nasan kuma Abba zai barta tazo, in yaso saita tayaka kula da ita idan zakaje site, u can go now buy this drugs for her kabata abinci taci kuma she need it" dan ajiyan zuciya ya sauke saikuma ya kalleta yanda dogayen kitso guda biyun da wata nurse tamata sabida ciwon dake kanta ke lilo tana kusa dashi takara washemai baki da sauri ya dauke kai ya kalli Dr yace "ina zamu samu hijabi" shiru Dr yayi kaman mai tunani sai chan yace "i think inada hijabin Maryam a office dina bari na dubo na kawo muku" da sauri yafita hakan yasa tawani irin juyar dakai ta harari kofar tana turo baki ta gefen ido ya kalleta abinma mamaki ya bashi, zama yayi akan gadon yaciro wayarshi yana daddana wa, da sauri ta zauna tana kallon wayar, hannu tasa ta fizge wayar da sauri ya dago kai ya kalleta nunamai wayar tayi saita boye abaya tana makemai kafada, abinma dariya yadan so bashi hakan yasa yay mata murmushi 4 d first time, ware ido tayi saikuma ta ijiye wayan akan gado ta mike tsaye tana tafa hannu sosai tace "yeeeeee" dan girgiza kai yayi kawai yace "funny" yadau wayar ya maida aljihu, ana bude kofa ta dawo kusa dashi ta zauna da gudu, Dr ne ya shigo dakin rike da maroon hijab ya mikama Aaman ganin yanda taketa murguda mai baki, karban hijabin yayi yace "thank u" ya mika mata hijabin da sauri ta karba tana jijjiga hijabin tana dariya kaman taga kayan wasa, ganin batama san meba yasa ya fizge ya warware ya saka mata kallon kanta ta dingayi tana jajjjan hijabin tana kokarin cirewa hakan yasa ya girgiza mata kai yace "No karki cire" da sauri takara tambayar shi "karna cire?" gyada mata kai yayi itama da sauri ta gyadamai kai, slippers yabata tasaka sanan yay hanyar fita Dr nagaba, da sauri tabishi suka fita a pharmacy ya tsaya ya saimata maganin duk tana kusa dashi tana kallon fuskarshi sanan suka wuce har wurin mota ya bude mata ya nuna mata ta shiga, ta shiga ya rufe ya zagaya duk tana binshi da ido sanan ya ahigo ya tada motar sukabar asibitin.
Cikinta ta rike ta hijabi tana shafawa tana tabe baki kaman mai shirin kuka tana kallonshi, ganin hankalinshi nakan tuki yasa ta kece dawani irin shegen kuka da sauri ya juyo ya kalleta yace "menene?" wani sabon kukan takara kecewa dashi tace "yunwaaa" da sauri yace "okay okay dena kukan, zakici apple?" gyadamai kai tayi hakan yasa yay parking abakin hanya daidai wajen masu saida fruits yasai mata apples dayasa aka wanke mata ya biya ya mika mata karban ledan duka tayi da sauri ta ciro daya tafara ci tana murmushi, kallonta yayi da sauri ta dago dara daran idanunta ta kallai washe mai baki tayi tasa hannu taciro katoton data balla yake cikin bakinta taciro ta mikamai da sauri ya girgiza kai yace "no bazan ciba" wani irin ihu tayi, ta kece dawani irin kuka da sauri ya mika mata hannu yace "okay okay, sorry karki yi kuka bani to" sakamai tayi ahannu tana washe baki kaman ba ita take ihu da kuka yanzun nan ba, ya karba yana dan murmushi kafeshi tai da ido tana jiran yaci tareda shagwabe fuska ahankali tace "ci" kallon Apple din yayi yanda yay dama dama da miyau sanan ya kalleta yanda ta tsareshi da ido, dan murmushi dole yasake yimata yay yunkurin kulle hannun, wani irin ihu datayi wlh saida ya firgitashi dan mutum ne shi marason hayaniya tawani irin fashe da kuka tace "ci" baisan lokacin daya hadiye apple dinma, tafashe da dariya tana kallonshi tacigaba dacin apple dinta shikuma ya kunna motar ya cigaba da tafiya har gidan gona, bishiyoyi kala kala da shuka ne daban daban, ta gefe kuma wani flat ne kwara daya babba sosai, parking yayi yafito ya zagayo ya bude mata da sauri tafito tana waige waige rike da apple dinta ahannu, gaba yayi hakan yasa tabishi da sauri ya bude kofa ya shiga, babban palour ne dayasha kujeru sai tv bango akan dogon kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa dashi da sauri tana kallon fuskarshi, shima ita yake kallo saikuma yaciro wayarshi yay dailing number wani mai kula da kajinsu ahankali yace "Umar dan Allah turomin Zainab" katse wayar yayi ya ijiye ya tashi, da sauri itama ta tashi dan juyowa yay ya kalleta saikuma yay Jim yacigaba da tafiya abinshi, kitchen ya shiga tana biye dashi tea yahada mata mai kauri a cup yadau slice bread ya shafa mata butter ya daura mata akan plate ya dauko ya juyo ya kalleta ganin yanda take kallonshi tana kallon abincin yasa yace "zaki ci?" da sauri ta gyadamai kai yace "okay to muje kici" yajuya yafita daga kitchen din da gudu tabiyoshi falo suka shiga ya ijiye mata cup din tea da plate din akasa da sauri ta zauna tana kokarin cire hijabin takasa saita dago kai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kwaye fuska tace "yaki fita" daidai lokacin wata yarinyar yar budurwa haka doguwa sanye da hijabin ta ta shigo bakinta dauke da sallama tace "gani Uncle" murmushi yamata yace "yauwa Zainab dan tayani cire mata hijabin nan" murmushi tayi ta shigo dakin tace "Uncle bakuwa kayi" kwanciya yay akan kujera yace "yeah bamata da lpy ne" daidai lokacin zainab takaraso gabanta da sauri takoma baya ta make ajikin kujeran dayake kai tanason tai kuka, ahankali yace "hijabin xata cire miki karki damu she's my sister" kallonshi tayi idanunta sun ciko da kwalla ya gyada mata kai tareda nuna idonta ahankali yace "don't cry, bari tacire miki" ya kalli Zainab yamata alamun datazo, zuwa tayi da kyar ya samu tabari zainab tacire mata hijabin sanan ya dauko mata tea ta tacigaba da sha, saida tagama sha, nan ma bakaramin daru yasha da itaba kafin ta bari zainab ta kaita ciki dantai wanka da kyar yasamu ta yarda suka shiga bedroom, suna shiga yadau key yafita dan zuwa yasiyo mata kaya sanan yayo take away danshi bai iya girki ba.