Sashe 15
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Koda suka fito za'a tafi bai fitoba, Abba yakara komawa part dinshi Mami tabishi da kallo tana girgiza kai dan wlh bata data cewa amma abu na Alhaji ya isheta, tare suka fito da Abba yawani sha mur bakaramin kyau manyan kayan sukamai ba bakin soft yard ne da akamai dinkin half jumper daya kama jikinshi yafito da murdaden jikinshi sosai, ga yadin ya haska shi tareda kara bayyana farin fatar shi da pink lips dinshi, harara Mami ta watsamai dasuka hada ido hakan yasa ya dauke kai da sauri, Abba daya kamata lokacin data harare shi ya nunata da yatsa. "kifita daga idona fa Firdausi wlh inkikace xaki takurawa yaron nan zamu zuba dake nefa" gidan gaba ya budemai yashiga dudda akwai body guard dake wajen wanda aikinshi bude kofa ne, Baba suleman ya shiga baya, driver Abba ya shiga mazaunin shikuma Abba yakoma baya ya zauna Mami da Big Mummy suka musu Allah kiyaye hanya suka tafi.
Wuraren azahar suka shigo zaria agaban wani massallaci suka tsaya sukai salla sanan suka kara shiga mota hakadai yadinga nuna musu hanya har gaban bolar nan.
Kin fitowa yay daga mota saidai ya nuna musu ginin suka shiga Abba harsaida yay kwalla babu komi a wajen sai carpet din data sakamai, fitowa sukayi suka shiga motar Abba nata kallon fuskar shi ta madubin kofar mota yana mamakin wakeson halaka mai da, shi baimasan Abba na kallonshi ba dan danna waya yake. Duk wani samari dazasu gani a anguwar saisun tambaye shi koyasan Muji suce basu saniba, hakadai har suka fara zuwa duk inda sukaga yan keke napep sunyi parking suce basusan wani Muji ba, har akai sallan la'asar suka tsaya sukayi suna fitowa yace "Popsy ni am tired fa" "shikenan to muje hotel kahuta gobe macigaba da neman sun" wani hadadden hotel sukai lodging a The Fabs anan suka kwana, washe gari tun wurin 8 Abba ya shigo yatashe shi yace ya shirya su cigaba da nemanta kaman zaiyi ihu haka yatashi ya shirya cikin farar shadda ya dauko black shade yasaka ta sanan yafito sai uban kamshi yake mai shegen dadi fuskar nan daure kaman zai fashe.
Tasha tasha haka suke zuwa har wurin karfe biyu suna abu daya, ata bakin kasuwan tudun wada sukai parking inda masu keke napep ke parking Abba da Baba Sulaiman ne suka fito suka gaggaisa dasu suka tambaye su ko sunsan wani mai keke sunanshi Muji, wani daga cikin su ne yace "Mujin filin mallawa?" shiru Abba yay chan yace "wlh bamu san dan ina bane mundai san sunanshi Muji" mutumin yace "to bari nakira shi kuga ko shine" godiya Abba yamai cike da fara'a aiko yana gama wayan mutumin yace" yace gashi nan zuwa" Kudi Abba yaciro masu yawa yamasu kyauta aiko sai murna suke nan fa suka fara koda yazo inba shi bane koma waye yake nema saisun nemomai shi. Abba yadinga godiya dan shi mutum ne mai fara'a mara girman kai, dason mutane idan yafita baruwan shi baya yanuna shine mai kudin nan da Nigeria keji dashi. Shidai gogan yana mota abinshi iskan Ac na hura shi yana danne danne awaya dan Meram ta isheshi da message.
Cikin minti talatin saiga Muji yazo da keken shi yay parking yafito, ya kalli abokin daya kirashi yace "Maska yane tasamu ne wanan kira dakamin ina masu nemana din?" daidai nan Abba da Baba Sulaiman suka taso daga jikin mota dasuka jingina, dafashi dayaji anyi yajuyo ganin magidanci ne yadafa shi yaci uban babbar riga yasa yay murmushi tareda dan dukar dakai yace "ina yini alaji" murmushi Abba yay yace "Mun wuni lpy, yar tambaya nake dan Allah Kaine Muji" gyada kai yay yace "eh sunana Mujittapa amma Muji ake cemin, kaikasa akirani Alaji dafatan dai lpy?" murmushi Abba yasake mai yace "lpy kalau, dan Allah tambaya nakeson nama kaine kokuma nace kasan wani mahaukaci haka achan wata anguwa haka gaban wani Bola a sabon gari. "wanan mara mutuncin mahaukacin na hanyar dogon bauchi, ai yariga ya warke Alhaji, kanwata data lura dashi tun yana sato buredi ta dinga kawomai abinci yanaci daga bayama ta karbo mai magani wurin baban mu tabashi yasha shine yana warke wa ya zanemu dagani har ita, ya kwada mata mari nikuma ya shakeni yakusa kasheni ai namai Allah ya isa wlh" tunda yake maganan Abba yakasa dauke ido akanshi, saida ya ijiye maganan sanan yace "shine ya shakeku?" da sauri Muji yanuna mai wuyan shi yace "kagani alaji har yanzu wuyana bai dawo daidai ba, har yanzu da shati shatin jan dayayi" dan murmushi Baba Sulaiman yayi dan so kawai yake yaga me Abba zaiyi, ga mamakin shi sai yaga Abba yarike hanun Muji yace "zokaga wani abu" kofar gaban motar ya bude daidai inda Ayaan dake chatting yake, bakin glass din fuskarshi Abba ya cire hakan yasa Ayaan dago kai ya kalli Abba, Abba ya nuna Ayaan da hannu ya kalli Muji yace "wanan ne ya shake kan?" shiru Muji yay yako kafeshi da ido shima Ayaan Mujin ya kalla rass ya ganeshi amma yawani basar ya cigaba da danna wayar dayake yi, ta kwayar idonshi masu kama dana mage muji ya gane shi dan har gobe bazai manta da idanun mahaukacin daya shake shiba aiko ya ballamai harara ganin ya dauke kai ya kalli Abba yace "shine alaji" Abba ya daure fuska tamau yace "Boy dama abinda kama wayanda suka taimake ka kenan dan iskanci, oya bashi hakuri right dis minute" tsaki Baba Sulaiman yaja aranshi dan yazaci Abba zaidan zubama Ayaan mari ne ya ramama yaron amma ina bazai iyaba, tashi ma yay daga wurin yakoma bayan mota ya bude ya shiga abinshi ya xauna. Ayaan dako dago kai baiyiba Abba yace "badakai nake ba bashi hakuri" dago kai yay ya zubama Muji ido batare dayace komiba, bakaramin kwarjini yama Muji ba, dauke kai Muji yayi ya kalli Abba yay murmushi yace "haba alaji basai yabani hakuri ba, mu dan Allah muka yi kumama wlh inda nasan dan kane daban fadama ba saiyanzu naga kaman ku wlh kaman kai kaki" murmushi Abba yay kaman bashine ya daure fuska ba yanzun nan yace "nagode dan albarkan yanzu kaimu gida mu godema mahaifin naka da ita yarinyar ko" rasa yanda Muji zaiyi yasa yakoma keken shi dan kunyan tsohon yake ya kunna keken shikuma Abba yashiga mota sukabi keken nashi abaya har kofar gidan su Bilkisu dake cike da almajirai anata karatu.
[7/15, 12:20 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
21 - 22