← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 89

Sashe 55

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda aka idar da salla yafi minti talatin azaune shi kadai amsallacin dan duk an watse sai shi baima da karfin tashi, dafashi dayaji anyi yasa ya dago kai limamin masallacin ne daya shigo daukar wayan shi daya manta dashi yace "baka da lafiya ne na taimaka maka na kaika gida" dago kai yayi ya kalli Imam kafin ahankali yace "tambaya nakeda shi" yanda yay maganan kaman zararre yasa lmam ya zauna ya lankwshe kafa, jingina kanshi dayamai nauyi yayi ya kalli Imam da idanunshi dasuka kankance ahankali yace "a Austria na girma, achan nai secondary school har nazama likita, am a very bad boy, idan nace bad i mean bad baddest, d only thing danasan banayi shine shaye shaye but zuwa clubbing, daukan mata, saka sarka, dan kunne, rashin salla duk nine, bayan nakare karatu na tattas na dawo harna fara aiki a asibitin abokin Pops dina inanan da halina even though Mami na da Abba suna kokarin su barinma Mami suga na dena amma naki, bansan meya sameni ba sai akace na haukace, ranan dai dana farka na ganni cikin kaya masu datti, awaje mai datti da bola ga wari, sanan gani kusa dawata yarinya wacce ita ta taimakeni da ina hauka hawaye duk sun bushe a idonta, ba karamin wulakanci namata ba har ina marinta a fuska amma kasan wani abu Imam?" yatambayi limamin yana bude ido kadan dan idanunshi a lumshe suke Imam yace "ina jinka" cije leben shi yayi cikin jin azaban da kanshi kemai yace "bayan na koma gida dudda fuskar yarinyar data taimaken nata bijiromin koda kulle ido kuwa nayi amma nai shiru naki fadinma babana harsai randa babana ya tamabye ni ya akayi na warke, na fadanmai, shine muka shirya mukaje zaria neman gidansu, bazan taba manta ranan" ya dafe kanshi yana wani irin murmushi yace "kafarta nafara gani da dogayen yatsun kafar dan batasa takalmi ba, kafarta na cikin jan lalle dayay wani irin kyau ta shigo dakin baban nasu da muke ciki tana sanye cikin pink hijabi mai hula, yanayin yanda take magana da komi nata sainaji ta shiga raina sosai, bantaba son wata mace aduniyar nan ba, banma san ya ake so ba amma saina ji ita ta tsayamin arai sosai, kome nakeyi saita fado zuciya ta, bantaba nunama kowaba saidai duk lokacin dazan hadu da ita saina mata wulakanci, naci xalin ta, nasata kuka, ranan da mahaifiya ya bijiromin da zancen aureta ranan banyi barci ba sabida farin ciki amma ban nunama kowaba saima kekashe ido danayi nace banison ta, ni mamakin kaina nake nine keson karaman yarinya haka yar talakawa, aranan da mukaje gidansu mahaifin ta yace mana ansa mata rana bikinta saura sati daya zuciyata takusa bugawa, da gangan nai karyan waya nake nafito ko zan ga wani almajiri ya nunamin waye isyakan da akace zata aura, ina fitowa naganta tana hira da shi jinai kaman na kashe isyakan wlh Imam, luckily sainaji yana fada mata inda zashi koda muka tashi tafiya saiban bisu munkoma kanon ba, adayake nai wayau nadau hoton isyakan saina turama wayan su kanin abokina dake zaria yana karatu a ABU da abokanshi hoton Isyakan nafada musu inda naji yace zaije, haka suka je basu ganshi ba suka fadamin saina cemusu to suzo layin su yarinyar su jirashi, suna zuwa suka kamomin shi aka kaishi hotel din dana sauka, kaga dukan danami kuwa wlh nakusa harbeshi sabida tsananin kishin yanda na gansu tare suna hira harda wani wai yasiyo mata ice cream, to saikuma na kwabi kaina akan kissan kai ba halin da musulmi yakama ta yanayi bane, saina bijiro mishi da ranan biki awajen daurin aure yace yafasa aurenta sanan namai kyauta sosai namai warning daya tsorata yaron ainun, shekaran jiya saida nakira shi na rokeshi ya yafemin bansan ko harda alhakin shi yake binaba yanzu ba, yace ya yafemin yanzu ma yay aure sanan ya bude shago dakuma makaranta da kudin dana bashi" sai yay shiru Imam yace "ina jinka" ahankali yace "Imam inason Bilkisu sama da yanda kake tunani amma inhar zan hadu da ita sau dari saina sakata kuka sau dari da hamsin, inci zalinta in gaya mata bakar magana, har muka tare agidan mu, yanzu haka yan kidnappers sunzo har gida sun dauke min ita, i think Allah na hukunta nine akan laifuffukan dana mishi" hawayen daya zubomai ne ya share da sauri yana sauke ajiyan zuciya ahankali yace "na tuba Imam, bazan kara koma ma aikin alfahasha ba, dan Allah katayani rokon Allah yadawo min da farin cikina Bilkis, ya tsaremin ita duk inda take, yadawo min da ita cikin koshin lpy, wlh na tuba, na tuba, na tuba, nai nadaman duk abubuwan danai ada, I love my wife more than life itself, Imam mezanyi Allah ya yafemin yadawo min da Bilkis?".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

65 - 66

Sassanyar murmushi Imam yamai yace "Allah gafurur Raheem ne, kadage da addu'a kadinga tashi cikin dare kana rokon Allah, kana gayama Allah bukatun ka, matar ka zata dawo, da izinin Allah zan tayaka da addu'a banda hakama duk inda take Allah ya tsare maka ita ya kare maka ita" ahankali yace "Ameen" Imam ya mike ya mikamai hannu yace "tashi na taimaka ma katafi gida" ahankali yamika ma Imam hannu da taimakon shi ya mike tsaye suka fita daga masallacin daidai wajen masallacin suka hadu da securities din da Mami ta turo azo adubo mata shi dan tajishi shiru, mika musu shi Imam yayi suka tafi dashi gida.
Suna shiga cikin gidan idanunshi suka sauka akan motar shi dake parking lot, wajen motar yayi da taimakon su ya bude, idanunshi ne suka sauka akan jakar Bilkisu daya karba ranan dazata bata hakan yasa ya mika hannu ya dauko, ahankali ya rungume jakar sosai ajiki yay cikin gida rike da ita, a parlor ya zauna yana zazzage jakar babu komi ciki sai wayarta da lace dinta da sauri yadau wayarta yana duddubawa amma akashe take ba chaji, da kyar ya mike yay sama ya shiga dakin ya makala wayar achaji, tana dan yi 10% ya kunna da sauri, gallery ya shiga da saurin bala'i kaman mahaukaci nanko yaci karo da hoton ta guda biyu kacal wanda tai selfie daya tayi shine kwance kan gadonta daga ita sai yar rigan bacci kusan rabin kirjinta waje rungume hoton yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mai sai kuma nabiyun tana sanye da doguwar rigar atampa afalo kan kujera tai hoton azaune, murmushin daya dade baiyiba yayi ahankali yakai bakinshi ya sumbaci hoton yace "i love yhu wifey" hanunshi ya tura cikin aljihu ya zaro sabon wayan da Abba yabashi sabida fashewar da tashi tayi, dailing number Cp yayi yana dagawa da kyar yace "an samu hoton ta kazo" yana fadin haka ya katse wayar yasake kwanciya anan kasan dakin ya rungume wayar sosai, kanshi dayaji ana shafawa yasa yadan bude ido kadan Mami daya gani ne akanshi yasa zai bude baki ta girgiza mai kai ahankali ta zauna ta daura kanshi akafafunta tana mai head massage.

Abba yadade yana magana da Malam a zaure kasancewar dalibai sunje bara saida yagama Malam ya nisa fuskarshi dauke da murmushi yace "da izinin Allah ankusa ganin ta" Abba kaman zaiyi kuka yace "zamu shiga cikine na fadima mahaifiyar ta?" girgiza kai Malam yayi yace "a'a banaso suji komi kasan mata da sa zance arai, yanzun nan saisu iya shiga damuwar dazai haifar musu da ciwo, bari in shiga gida namusu sallama zan bika na dubo Ayaan sanan akwai addu'a danake so namai sanan nayi agidan da aka dauketan, in sha Allah kwann nan zata dawo".

Ba'a jimaba malam yafito dauke da wata yar jakan malamai Abba ya mike suka shiga motar driver yajasu.
Cp na zuwa kasancewa yay bacci Mami ce tabashi hoton ya karba yace "za'a watsa hoton duniyar yanar gizo da gidan talabijin da sauran kafafun yada labarai hakan zai taimaka sosai.

Wuraren 9 nadare suka shigo gidan sabida go slow daya rikesu akano, bakaramin tausaya wa Ayaan dake bacci Baba yayiba.

*Bauchi*

Yau kusan satin ta biyu kenan agidan tun washe garin ranan datazo kanwar shi Ummy wacce yan makarantar su suke cema Ummy fingers tazo Buchin, yarinyar badai kyau da iya gayu ba, da kyar da kyar yasamu tana dan yarda da Ummy harma su kwana daki daya amma dudda haka saita ga dama take kula Ummy gashi Ummy na sonta bana wasaba.
Chapter 55 · 0% Book details