← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 89

Sashe 12

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shigowa katafaren falon mai kama da aljannar duniya yayi, yan aikin dake sanye da uniform suna kokarin gyara dining suka bishi da kallon waye wanan ammadai basuyi magana ba. "Popsy, Popsy" yakara kwalama baban nashi kira, baki zai bude yakara kiranshi sai yay turus yana kallon fuskar shi ta jikin uban show glass din dake falon da aka jera wasu hadaddun verses aciki, madubi ne gabaki daya, yanda gashin kanshi suka wani mummurde kaman dada ga gemushi busu busu da yanda fatar shi tai wani irin mugun baki ya tsaya kallo shi kanshi yana mamakin shine haka, dan yama kasa gane shine. "Boy!" yaji Abba yakira shi da irin muryan manya dinan wayanda suka kwana biyu aduniya da sauri ya juya yaga Abba akan stairs ya tsaya tareda kama karfen stairs din dan baida karfin tsayawa complete ga Mami itama tsaye a gefenshi duk sun kafeshi da ido.
"Pops" yafada kaman zaiyi kuka yay hanyar benen da sauri, Abba ma yafara tattakala stairs da sauri kaman bashine mara lpy ba. "Boy, Mah Boy is back, Ayaan is back" da gudu da Ayaan yafada jikin Abba ya kankame shi sosai, hakama Abba ya kankame shi ya sumbaci gefen fuskarshi batare daya damu da warin da fatarshi yakeba, sunfi minti kusan biyar ahaka yan aiki sai kallonsu suke suna murna da yau sunsan zasu sami special kyauta dan gatan alhaji da aketa nema yadawo, sakin juna sukayi Abba yay cupping fuskar shi yakara sumbatar goshin shi kafin ya kara rungume shi akaro nabiyu ya sauke ajiyar zuciya, murmushi yay wanda daga rashin yake anya akwai abinda yakeso a duniyar nan kaman Pops dinshi kuwa, sakinshi Abba yay yakara cupping fuskarshi kaman zaiyi kuka yace "maiya faru dakai Boy? Babu wani gidan talabijin da gidan radio dabamu sanar da bacewar kaba, da saka hotunan ka aduka gidan talabijin din Nigeria nan, waye yama wanan abun Boy, yaushe ka girma mema kasani dahar mutum saiso cutarmin dakai, kuma agidana ma, koma waccece maid dinan data baka abinci ranan da sunan ka mahaifiyar ka sai annemota zata gane ta tabamin kaine wlh azim" zame fuskar shi yay daga hannun Abba yawuce ya rungume Mami daketa kallon su tareda daura kanshi akafadar ta ahankali yace "i miss you Mami na" wani kwalla ne yazo mata kafin itama ta ciroshi ta sumbaci goshin shi daidai lokacin Baba Sule ya shigo da Hajiya Saratu (uwar gida) data shigo da kuka sosai ta tsaya agaban shi takai hannu tana shafa fuskar shi tafashe da kuka sosai cikin kuka tace "maiya sameka d'ana, Ayaan haukacewa kayi ashe da gaske dai? Innalillahi wa innaillahi raji'un, duniya ina zaki damu?" cikin kuka takara kallon Alhaji daketa shafa kan Ayaan din kaman zai hadiye shi dan so, tace "Alhaji wlh ko bangon duniya ta shiga anemo maid dinan data bashi abincin karshe" tasake fashewa dawani irin kuka tafada jikin Ayaan din, dago da kanta yay ya girgiza mata kai tareda sa hannu ya goge hawayen dake zuba daga idonta yace "stop crying Big Mummy, am okay now" gyadamai kai tayi kafin tai murmushi tace "to ya akayi kaji sauki, CCTV footage damuka kalla ya nuna a haukace kafita daga garden din, ya akayi ka warke?" yatsine fuska yay tareda dafa kanshi da sauri Abba ya rikeshi ya kalli Big Mummy yace "ki barshi haka da tambayoyin nan daga dawowan shi muje side dinka ka huta" yarike mai hannu tareda kallon Baba Sule yace "muje Sulaiman" Baba Sulaiman yabisu abaya suna sauka kasa Abba yafara kwalama chief of staff din gidan kira "Mike, Mike" da sauri mutumin yafito shima sanye da uniform yace "call for home service masu massage, manicure, pedicure, da kuma barber dakemai aski be fast" dukar dakai Mike yay yace "to Alaji" ya juyo ya kalli big Mummy yace "kekuma kira Dr Hassan yaduba min shi" ashagwabe ya kalli Abba ya turo baki yace "Pops no basai yazo ba, zanyi prescribing drugs din danake bukata Mike yaje yasiyo min a pharmacy" ahankali Abba ya shafa kanshi yace "are u sure, likita fa baya duba kanshi saidai wani likita ya dubashi" dariya yay a sangarce ya kalli Baba Suleman yace "Baffa tell Pops to leave me alone" duk dariya sukayi kafin Abba yace "shikenan Boy tunda hakan kakeso baza'a kirashin ba" yasake juyowa ya kalli Mami dahar lokacin take tsaye sai kallon dan nata take yace "jekimi shi fevorite dinshi Firdausi, kinsan bayacin abincin yan aiki" da sauri Big Mummy tace "Alhaji tabarshi ni zanmai" girgiza kai yay yace "a'a Saratu, kinsan Boy bayason spicy food kuma girkin ki is way too spicy for his liking, kibarshi Firdausi ta dafamai" yana fadin haka yajuyo ya kalli Mama jummai wacce itace mai gyara bangaren Mami, yanzu ma tagama aikin tane zata tafi taga Ayaan yadawo ai da sauri ta tsaya dan tasan yau akwai buduri zasu sha kyauta harda na innanaha abunka da alhaji mai kyauta bare yau da dalili, Abba yace "Mama Jummai konawa kikeso ga Sulaimanu nan zai baki, kinajina direba ya daukeki kije kasuwa, inaso ahadamin gagarimin girki sanan dukan ku" ya kalli duka yan aikin yace "harda su securities dukku fada musu su gayyaci koma wasukeso azo anjima bayan sallan magriba akwai walima anan" Yasake kallon Baba sule yace "Sulaimanu inaso kaje office kai order motoci dari, and kai contacting dangote company inaso akawo min trailer daya na buhun shikafa araba ma marasa karfin gari Boy yadawo" duka yan aikin sai murna suke, sake kallon Ayaan din yayi dake kallon mahaifin nashi yana murmushi, ya saki hanunshi kafin ya tsugunna yay sujjadan godema Allah na amsa mai addu'a dakuma bayyanar mai da danshi, aiko dakin yadau kabbara kowa saida yay sujjada ganin Abba yayi banda shi gogan daya tabe baki ashagwabe yace "Pops am tired of standing fa" kama hanunshi Abba yay kaman wani yaro ya sanya dayan hanunshi yakamo kafadarshi ya kwanto da fuskar shi kan shoulder dinshi yana murmushi ya shafa uban gemun daya tarun mai yace "sannu dan albarka, muje kahuta kaji" fita sukai daga dakin Mami da Big Mummy dama kowa na dakin suka bisu da kallo, girgiza kai Mami tayi kafin ta sakko ta karaso inda Big Mummy take tace "barka da rana Hajiya" "barkan mudai" Big Mummy ta amsa mata awulakan ce, murmushi tayi tawuce kitchen kasancewar ta mace mai hakuri ko sau daya bata taba biyema Hajiya Saratu sunyi fadaba koma ko mezatayi.
[7/15, 12:18 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

15 - 16

Alhaji Abdulrasheed Gwanaye shararan mai kudine dakeda shakaru sabain da bakwai 75 aduniya, su biyu iyayen su suka haifa shi da kaninshi Sulaiman, ya girma Sulaiman dakusan shakara ashirin danhar mahaifiyar su ta cire ran haihuwa sai Allah yabasu Sulaiman, shahararan mai kudi ne Alhaji Abdulrasheed dake business din man fetur, danhar jirgin ruwa dake tsotsomai yanada shi, sanan yanada gidan mai gidan mai daban daban akowana gari na Nigeria, sunan gidan man shi Gwanaye filling Station, cikakken bahaushe ne shi, mutum ne shi mai saukin kai ga yawan kyauta, tun yana da shekara 20 yay auren shi na farko da Saratu sabida yanada son yin aure, suna zaman lafiya sosai bayan shekaru biyar maman shi ta matsa mai ya auri yarinyar makwabciyar ta da mahaifiyar ta ta mutu wato Firdausi, nan fa akai aure dudda Saratu bataso ba amma ganin yanda Mami kemata biyayya yasa tadan sauko haka suka zauna dukba haihuwa.
Alhaji harya cire rai dan har yakai shekaru 45, rana daya kawai Allah ya albarka ceshi da da namiji. Lokacin da aka gane Mami nada ciki bakaramin murna yayi ba yakasa boye farin cikin shi hakafa aka haifi yaro namiji kyakyawan gaske kaman bature, yaro sak mahaifin shi, aka radama yaron suna Ayaan, duk wani son duniya Alhaji ya daurama yaron nan, wani zubin ko abu kakeso kabiyo ta hanunshi shikenan kasamu, nursery da primary kawai yay a Nigeria Alhaji ya fitar dashi waje anan yay secondary yay karatun gaba da secondary ko hausan dayakejima dan yana dawowa gida hutu ne. Alhaji da Hajiya Saratu sun bata yaron, kullum cewa suke yarone idan ya girma zai gyaru da kanshi, Mami ce ke tsayin daka wajen tarbiyan tar dashi amma bata sami goyon bayaba dazaran tafara mai fada zai fara kuka yafada jikin Abba, Abba yadinga bala'i kenan har washe gari shida hajiya Saratu. Baba Sulaiman kadai ne ke supporting dinta. Bari nabar labarin haka zakuji sauran nan gaba.
Chapter 12 · 0% Book details