← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 89

Sashe 84

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saida tai game din ta gaji ta ijiye wayan akan gadon ta kwanta tana lumlumshe ido sabida wani irin zazzabi dake cinta ga cikin ta dake wani irin juyawa tanaso tai amai, shigowa dakin Mami tayi yanda taga tana jujjyawa akan gado yasa ta karaso da sauri ta dagota zafin dataji ajikin ta yasa tai salati tace "bakida lpy ne daughter sannu kinji bari nakira mijin naki yaduba ki" gyara mata kwanciya tayi daidai lokacin idanunta suka sauka akan wayar Ayaan dake kan gado, kokarin tashi da take yi daga gado yasa Mami tace "ina zaki" nishi take tana shafa wuya yanda takeyi yasa Mami tace "amai?" kaman jira aman yake takira sunan shi, amai ta shiga yi anan Mami bata hanata ba Sai sannu take mata saida tagama sanan tafashe da kuka Mami ta kaita bayi tasata ta kuskura baki sanan tafito da ita ta kwantar da ita akan gado ta gyara wurin ganin bacci yadan dauketa yasa tafita ta shiga dakin Abba dake tareda Baba Suleman cike da damuwa tace "alhaji Bilkisu batada lpy kuma Ayaan yafita yaje asibiti yabar wayar shi agida" da sauri Abba yace "subhannalah bari nakira Ibrahim to yabashi wayar idan kuma baya wajen shiyazo ya duba mana ita" wayar shi ya dauka yay dailing number Ibrahim ringing daya ya dauka, da sauri Abba yace "Ibrahim Ayaan na wajen ne wlh matar shi ba lpy" anatse Ibrahim yace "a'a baya hospital bai dawoba tun bayan barinsu dazu, amma ai karku damu ciwon datake yi normal ciwo ne kasancewar tana dauke da sabon ciki" zumbur Abba yamike yana kokarin faduwa da sauri Baba Suleman ya mikamai sandarshi ya karba ya rike gam gam yace "me, me, mekace Ibrahima?" dan dariya Dr Ibrahim yayi yace "Abba dama boy baifada ma ba, aiko dazu bayan kun tafi tanata zazzabi shine fa yaban jinin ta nakai lab akai test gwajin farko yanuna tana dauke da juna biyu" "juna biyu" Abba yafada yana goge yar kwallan farin cikin daya zubomai da sauri yace "kaga Ibrahima fadamin kome kake so inhar baifi karfina ba nakane wlh" dariya Dr yayi cikeda murna yace "Abba dama spain 🇪🇸 nake so nakai matana mudanje yawon bude ido" cikin wani irin farin ciki yace "katura min duka information dinka kaida matar ka zansa amuku visa ka shirya ba Spain kadaiba harda wasu kashashen ma saika zaga tukwuicin ka nabani wanan albshir dinne" ihun dadi Dr yayi yace "godiya nake Abba Allah kara tsawon kwana ya Kade fitina" katse wayar Abba yayi yay ma Allah sujjada yana godiya saikuma ya tashi zaune yana kallon Mami yace "ashe dai boy angirma kiga fa bai fada mana Bilkisu nada ciki ba" yay wani irin dariya irin ta manya yana girgixa kai saikuma ya kalli Mami da tsabagen farin ciki bakinta yaki rufuwa yace "Firdausi jeki tambaye ta koma metake so inhar zai zauna acikin bazatai amai ba, aje asiyo ahada mata, koma dai amata shashaka ne kinsan fa lokacin dakike da cikin Boy har tsakiyan dare tadani kike zakici shashaka" da sauri Mami ta rufe fuska tajuya tafita Baba Suleman namata dariya tasan idan tace zata Kara Koda minti dayane Alhaji saiya tona asirin duka abinda tayi datana da cikin Ayaan yanda yake cikin farin cikin nan. Kaceme wa anguwan yayi dan Abba kyauta yadinga yi harda na innanaha.

Wuraren goma ya shigo part din sanye da 3quater white, sai white long sleeve t-shirt dabai kulle boturan ba kirjinshi abude sai wani irin kamshi yake mai tafiya da zuciya, ganin bakowa afalon yasa yay sama dakin Mami ya bude ya shiga dayar gajeren sallama daidai lokacin tafito daga bayi daure da towel daya tsaya mata acinya, hada ido sukayi da gudu tazo ta fada jikinshi ta fashe da kuka tana dukan shi, kunenshi ya kama yana kallon fuskar ta murya chan kasa yace "am sorry" make mai kafada tayi ta sakeshi tana turomai baki ta juya tai kan gado tadau rigar baccin da Mami ta ijiye mata akan gadon, da sauri ya biyota kwantowa yay tabayan ta ya daura duka hannayen shi akan cikinta yana shafawa, ahankali ya lumshe ido yayi yana shakan kamshi turaren da Mami tahada mata a ruwan datai wanka dashi dake fizgar shi sosai, murya chan kasan makoshi yace "please baby" bude kofa da akayi yasa ya bude ido ahankali batare daya saketa ba hada ido sukayi da Mami dake rike da mug, akunyace ya saketa yay wajen Mami ya karbi mug din yace "sannu da aiki Mami na" kallon shi tayi saikuma ta kama kunenshi ihu yayi asangarce yace "wash Mami zafi" ajiye rigar tayi da gudu tazo wajen tana kallon yanda Mami ta rike mai kunne, ta kalli Mami tafashe da wani irin kuka tana tsalle kokarin takai kunenshi ta ture hanun Mami, wani irin murmushin dadi yayi mai sauti yana kallon Mami shima kaman zaiyi kuka, hakan yasa Mami ta sakeshi tareda dungure mai kai, da sauri Bilkisu ta rikeshi ta rungume hannunshi tana share hawayen daya gama wanke mata fuska, baki Mami takama tace "ah lallai yaran zamani, wato na ja kunen mijinta tana kuka, kunga tafiya ta ai, kabata mug din natane" tajuya zata fita, dariyan iskanci yabi Mami dashi hakan yasa ta juyo itama dariyan ke cinta daurewa take ta harare shi tace "mara kunya kawai dauketa kubarmin dakina kafin nadawo" tasakai tafice, juyowa yayi ya kalleta da wani irin smile akan fuskar shi abinda tayi yanzunan har kasan kasan ranshi yamai wani irin dadi, ahankali ya ijiye mug din akan stool yawani hau yimata kiss tako ina, washe mai baki tayi haka ya cigaba da kissing dinta harya jata zuwa gado, rigar baccin ta white da Mami ta fito mata dashi ya dauka ya saka mata iya guiwa ya tsaya mata wani irin kallo yabita dashi sanan ya dauko hijabi yasa mata yadau mug din yabata, karba tayi ta kafa abaki water melon da dabino Mami ta Nika mata a blender tasaka madara da Zuma bata taceba, sosai yamata dadi ta shanye tass tabashi mug din iyewa yayi anan sanan ya juya mata baya ya duka ya kalleta yace "hau" washe mai baki tayi sosai da gudu ta dane bayan shi ya mike tsaye da ita ya gyara mata hanunta akafadar shi sanan suka fito daga dakin sukai kasa, Abba da Mami da tunda sukaji Karan bude kofar su sukadan leko, tafawa sukayi Mami ta kalli Abba tace "like father like son" hararan ta Abba yayi yace "kyau Kenan bakiga yanda kika mutun munba da tsufa na amma duk randa bana dakinki baki Iya bacci na Iya luv emmata" filon kujera Mami ta bugamai ya chabe yana dariya.
Chapter 84 · 0% Book details