Sashe 26
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Misalin karfe takwas na safe tafito daga wanka daure da zani a kirji Baaba dake zaune gaban murhu ta bita da kallo yanda take uban sheki, murmushi tayi tajuya tacigaba da dama kokon datake yi, daki ta shiga ta shafa mai ta shirya cikin doguwar rigan kampala shaddan purple da fari da Baaba ta iniye mata aiko yay mata shegen kyau tana cikin fama da daurin dankwalin dan takasa sabida dan kwalin yay kaba kaba Baaba ta shigo tace "ke imaza yapa gyalen tunda kin kasa daurin kije Baban ki ya aiko Muji ya kiraki iyayen mijin ki suna hanya zakuyi sallama su tafi, mike" Baaba ta dagata ganin bamata da niyyar tashi tadau gyalen ta yafa mata tace "imaza tafi nima ganinan zuwa" fita tayi daga gidan jikinta duk asake har gidan su da babu wasu mutane sosai dan yan uwan su kadanne suka rage dakinsu tayi tana shiga uwar daka tafada kan Maman su tafashe da kuka sosai dagota Mama tayi ta share mata hawayen dasuke zubowa tace "kiyakuri Baby, nasan yanda kikeji, haka Allah ya kaddara zai faru dama chan Isyaka ba mijin ki bane, bahakanan Allah ke hadaka da wani arayuwa ba rana daya ba, kin hadu da Ayaan ta dalili ne, asheko shine wanan mijinki, ki yakuri kinji anriga andaura babu yanda zakiyi" cikin kuka tabude baki zatai magana Mama ta girgiza mata kai tace "banison ji" sallaman da akayi yasa Mama ta amsa ta fita ganin Mami ce itakadai dan sauran duk sun shiga falon Baba yasa Mama tai murmushi tace "barka da zuwa kun iso, shigo" shigowa Mami tai tasami waje ta zauna tace "ina kwana ya gajiyan bik" Mama tace "lpy lau ya taku gajiyar" murmushi Mami tayi tace "Alhamdulillah ina yar tawa?" murmushi sosai Mama tayi tace "tana ciki bari nakira miki ita" da sauri Mami tace "a'a kibarshi dan Allah ni nashiga?" a kunyace Mama tace "kai dan Allah keda yarki kike wani tambayana, ni kinga ma tafiyata bari naje agaggaisa" Mama tadau hijabi ta fice zuwa dakin Baba, Mami ta daga labulen da sallama ta shiga dakin, a kunyace ta mike tsaye dan taji Mama na magana bama ta tsaya ta saurara ba sabida kukan ta take, tsugunnawa tayi tanadan murmushi ahankali tace "ina kwana Mumy" hannu Mami tasa ta dagota sama kafin ta sumbaci gaban goshin ta, lumshe ido tai a kunyace dan bata sababa, Mami ta zauna da ita akan gado kafin ta zauna agefenta tana murmushi tace "Allah miki albarka Bilkisu kiyakuri kinji, Ayaan zai kula dake karkija komi zamu rikeki amana" jakar hannunta ta bude ta ciro wata sabuwar Samsung ta mika mata kin karba tayi saima kara sunnar da kanta kasa datayi tana wasa da bakin gyalenta, ajiye mata wayar Mami tai agefe tace "ga wayar kinan nasamiki number na aciki, zan dinga kiranki, kiyi karatun jarabawa da kyau kinji Allah yabada sa'a" ahankali tace "nagode Mumy" shafa kuncinta Mami tayi kafin ta tashi tafita daga dakin itama ta shiga falon Baba anata magana.
Fadawa tayi kan gado tafashe da kuka sosai tarasa inda zatasaka ranta taji dadi, zumbur tamike kaman an tsikareta tafito daga dakin Maman ahankali tai hanyar zaure tana tafiya sadaf sadaf tana bude kofa tafita zaure saida tadan labe abayan kofa kafin tadan leka kofar gidan kosu Baba nanan awaje ganin babu kowa sai kusan motoci uku dake fake akofar gidan nasu akukkule yasa tai wuf tafito, tana waige waige ganin lallai ba kowa dan ko almajiri daya babu yasa ta gyara gyalen kanta tareda tattare doguwar rigar dan tadan mata tsawo ta arce a guje.
Ayaan da tunda take leke leken ta daga bayan kofa yake kallon ta dan yana cikin mota ya kunna AC yana sha, gajiya yay da surutan su yay fitowar shi waje, dayake glass din motar tinted ne saisa bata lura dashi ba, gyara zama yay ya kalli madubin window motar yanda take tafiya gudu gudu, sauri sauri ya kafeta da ido tareda hade hannayen shi biyu ya dunkule yakai karamar yatsan shi daya yadaura akan lips dinshi kaman mai tunani, ganin tasha layin tai kwana yasa ya kunna motar yaja yabita.
Babban wuri ne haka da akamai runfa sabida asamu inuwa, mutane ne zazzaune daketa aikin hannu, wasu na sakan hula wasu kuma na aikin wuyar shadda, da sauri da sauri take karasawa wajen fatanta Allah yasa ta ganshi anan dan tasan baida wajen zuwa sai nan, anan duka abokan shi suke, tsayawa awurin tayi tana kalle kalle ganin bashi awurin kaman ance ta daga kai ta hangoshi kan bencin dake gaban wani shagon dake gefen wajen, ga yar jaka agabanshi yanata diban kayanshi dake gefenshi akan bencin yana jerasu acikin jakar, da gudu tai wurin tana share hawayen dataji yafara kwararowa, kaman daga sama yaji ance "mena maka kafasa aure na?" dago kai yayi asanyaye ya kalleta gani tayi idanunshi sunyi jajir suma harma sun kumbura, kasa daurewa tayi tafashe da kuka sosai tasa gyalenta tana sharewa bata ma damu da mutanen dake shiga shagon siyan abu bama cikin kuka tace "maiya sameka idanunka sukai haka? Mena maka? Maiya sa kace kafasa aure ne kasan illar da hakan yamun kuwa? Inda kasan baka sona maiya sa tuntuni baka fadaba sai a wurin daurin aure? Maisa kamin haka eh?" baki yabude zaiyi magana saikuma yafasa yay shiru taga ya kurama bayanta ido, da sauri ta juya dan taga maiyake kallo Ayaan ne acikin mota yay wining glass down idanunshi sanye cikin bakin glasses, daure fuska yay tamau ya kalleta babu alamun wasa atattare dashi yace "get in" kaman bada ita yake ba ta juya ta kalli Isyaka daya cigaba da hada kaya abinshi kaman bashi a wurin tace "kasan yanda nake sonka kuwa shine ka cutar dani haka ko, maiya sa kamin abinda kami..." tsawan dataji yasa takasa karashe maganan datake yi. "are u deaf nace kishiga mota mutafi" yay maganan har lokacin yana zaune cikin mota afirgice ta juyo tafashe da kuka sosai batare data shiga motar ba mutane sai kallon su suke, bude kofar yayi yafito yana wani irin taku da duk taku daya saitaji har a kokon ranta, da sauri ta runtse ido sabida wani irin mugun tsoron dataji yana shigan ta, hanunta dataji ya fizga kaman zai katsa yasa ta bude ido janta yayi ya bude mota ya wurgarta ciki kafin ya koma ta dayan side din yanama Isyaka dasuka hada ido wani irin kallo, da sauri Isyaka yadau jakar ya juyama motar baya kirjinshi na bugawa, wani irin dan iskan murmushi yayi kafin ya bude motar ya shiga ya bata wuta, kuka take kaman ranta zai fita kanta nakan cinya.
Bai tsaya ko inaba sai gidan dam, wurin babu kowa gashi very peaceful sai iskan bishiyoyin daketa kadawa da kukan tsintsaye dake wucewa, zagayawa yay ya bude side din datake har lokacin kanta nakan cinyanta kuka take sosai cikin kakkausar murya yace "fito" ko dago kai batayi ba balle yasa ran zata fito, hakan yasa ya jawota da karfi luuu ta taho zata fada kanshi dan ko karfi daya bataji dan rabonta da abinci tun jiya ya matsa gefe da sauri hakan yasa ta zube akasa, wani wahalanlen kuka tasaki ahankali tana share guwiwar hannunta daya bugu da kasa, ya dawo ta gabanta yay wani irin tsugunnawa daya karamai kyau yana karkada key motar dake hanunshi yana mata wani irin kallo yace "baki da natsuwa ko, bakisan kinada aure ba zakije kina ma wanchan dan kauyen magana" turo baki tai cikin kunci tace "Isyaka na niba dan kauye bane karka sake cemai dan kauye" takarashe maganan tana wani lankawasa wuya gawasu sababbin hawaye dasuka zubo mata tsabagen takaici, dagota yay da karfi ya jingineta jikin mota ya kafeta da ido da sauri ta kawad dakai tareda sa bayan hannu tana goge kwallan yace "ke ki natsu fa banason raini ko kadan wlh, auren taimako nayi, na taimake ki da mahaifin ki danaga hawan jini na neman kamashi da almajirin chan yace yafasa auren ki" murguda mai baki tayi dan wlh yakaita bango tace "eh almajirin ne aidai Allah ya halicce shi, kuma ahaka nakeson abuna har yanz..." bakinta daya kaima duka da karfi yasa tai shiru ta fashe da kuka, hanunta ya kama yakai baya ya murde hakan yasa ta bankare tana ihu. "wayyo Allah na Mama zai ciremin hannu" hadata yay da mota ya matseta danhar jikinsu na gogan juna ya kalli kwayar idonta yace "wlh idan kika sakemin rashin kunya sai namiki abinda zaki dinga kuka tunda ga yau har ranan daza'a kawoki gidana".....
[7/17, 11:57 AM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
33 - 34
Ya ja hanunta ya bude side dinta ya wurgata ciki kafin ya koma mazaunin driver ya shiga ya yatada motar yabar wajen, duk tacika mai mota da kuka abakin layin su yay niyar sauketa hango su Abba da Malam awaje yasa yawani dakamata tsawa. "ke!" atsorace ta dago kai ta kallai hannu ya daura akan lips dinshi alamun tai shiru hakan yasa ko tai shiru har yakarasa kofar gidansu, aiko su Abba sukabi motar da kallo parking yay yafito da sauri ya zagayo ta inda take ya bude mata daidai nan su Walawa dasuka zo wurinta suka fito daga gidansu, murmushi both Abba da Baba harda Baba Sulaiman duk sukayi hankalin su yakara kwanciya ganin Ayaan da Bilkisu tare. Fitowa tayi daidai lokacin su Walawa sun iso sai kallonshi suke atare suka gaidashi "ango ina yini, ina kukaje kaida Amaryan tun dazu mukaxo fa" murmushin dole ya kakalo ganin su Abba a wajen itakuma wucewa tai cikin gida abinta, su Walawa sai uban surutu suke mai yana yake daga baya sukamai sallama rapper kudi yaciro yabasu suka karba sukamai godiya kafin su koma cikin gidan.
Sai bayan azahar suka tafi bayan sun cika gidan da kayan abinci da kudi duk yanda malam yaso yaki karba kin yarda Abba yayi yace ai yanzu anzama daya kafin su wuce kano kowanensu rai fess.