← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 89

Sashe 58

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dayake wuraren sha daya sukabar Bauchi sai gurin biyu da rabi suka shigo garin kano kafin sukai police headquarter kuma sai wuraren karfe uku da minti biyar, parking sukayi suka fito ya zagayo tabaya rike da pringles din daya saimata a hanya da bottle water sabida bacci takeyi tuntuni ya bubbuga kujeran hakan yasa ta bude ido da sauri ya dauke kai, waige waige tayi tana kallon wurin tace "sweetheart mun iso garinmu?" dan ita tazaci wani wurine mai suna haka, gyada mata kai yayi hakan yasa tafito tana Kalle Kalle shikuma ya maida kofar ya rufe ya kalleta yanda take kallon polisawan daketa harkan su sun ririke bindigogi yace "muje" girgiza mai kai tayi tana neman yin kuka ta nunamai yan sandan ahankali yace " don't worry babu abunda zasu miki muje" gaba yayi tana binshi abaya har inda Dr Ameenu yake suka shiga ciki saida suka rubuta sunayen su sanan sukace inspector Husaini Ahamad suke nema dan sunanshi aka rubuta a page, kujera aka nuna musu shima dan polisawan sungan su sunyi shigan alfarma ne yasa sanan wani daga cikin su yatafi office din inspector yay kusan 10 min sanan yafito yace "muje" tashi sukayi suka bishi har office din inspector dake zaune yana jiran su sanan yafita, inspector na ganinta ya mike tsaye cike da mamaki kafin ma suyi magana yace "am coming ku zazxauna" fita yayi yay upstairs office din CP, yana shiga ya kame yay saluting CP sanan yafada mishi abinda yagani Cp yabiyo shi suna zuwa office din tsayawa yayi baice komiba yana kallon Bilkisu take fama da bude goran ruwa saikuma yasa hannu a aljihu yaciro wayarshi ya duba yaga ai yarinyar hoton nanne wacce akai kidnapping wani irin shan mur yayi ya kalli su Aaman dake kallonsu yace "su waye ku? And waccece yarinyar nan? A ina kuka samota? Menene hadinku da ita?" kafin ma Aaman yace wani abu Dr ya mike yaciro ID card dinshi yace "am Dr Ameenu and my Friend here is Barrister Aaman, nan ya shiga basu labarin komi tundaga kan yanda Ayaan ya tsinceta da lokacin daya kawota hospital yagama sanan ya bashi file din medical record dinta. Saida Cp yagama dubawa yay wani irin hamdala ya mika musu hannu yana godiya sanan yace sutashi suje office dinshi dan gaskiya wanan good news gwara Alhaji ya gani a office dinshi ba'a office din inspecta ba yau ya tabbata sabuwar mota da kujeran maka zai samu, office suka tafi suka zazzauna sanan yadau waya yakira Abba.

Alhaji dasu Baba da Baba Sulaiman wanda yadawo jiya jiyan nan sabida kiran da Mami tamai dan Alhaji ma ciwo ne yarufe shi, yaudai duk dauriyan da Abba yakeyi kasawa yayi yafashe da kuka sosai, babba dashi amma kuka yake ganin abinda yafi soyuwa agareshi, aduniyar nan gabaki daya ma Ayaan baimasan wake kanshi ba, gashi yaki yarda a kaishi asibiti agida Dr Ibrahim yazo yamai allura yamishi fixing drip, Mami dai fita daga dakin tayi ta shiga nata tana kuka sosai, Baba ne ke kanshi yanamai addu'a aka, shikuma Baba Sulaiman yana calming Abba down, ringing da wayar Abba yayi yasa Baba Sulaiman ya mike ya dauko wayar daga kan gadon da Ayaan yake a kwance ganin Cp ne yasa ya mikama Abba yace "ka dauka Cp ne Allah sa Muji alkairi" goge idanunshi yayi da bakin malummalum din dake jikinshi ya kalli Ayaan da aka sakama oxygen dan baya iya numfashi da kyau ya sake girgiza kai yana kokarin tsayar da hawayen dakeson zubomai, yay picking call din tareda yin sallama ahankali, zumbur yamike tsaye yana neman fadi Baba Sulaiman ya taroshi bakinshi har rawa yake yace "Cp kace anganta, Bilkisu Bilkisun mudai?" kowa na dakin kallonshi yake tsabagen murna ma jefar da wayan yahi ya tsugunna yay sujjada sanan yayo gadon baima bi takan Baba Sulaiman dake tambayan shiba yay cupping fuskar Ayaan da idanunshi ke lumshe yana girgiza shi hawaye na gangarowa daga idanunshi na farin ciki yace "Boy, Boy tashi muje police headquarter anga Bilkisu Boy, anga matar ka" da kyar ya bude idanunshi dasuka kankance ya rike hannun Abba da karfi yana kallon fuskar shi batare daya iya magana ba, gyadamai kai Abba yayi yace "yes, yes my baby Boy, anga matar ka, i love u Boy so so much, oya get up let's go get ur wife" da taimakon Abba da Baba yatashi har lokacin kallon Abba yake dan gani yake kaman zafin zazzabi yasa yakejin Abba nakiran anga Bilkisu, ciremai robar oxygen din Abba yayi sanan yacire mai drip din ya kalli Baba Sulaiman yace "ban rigan shi" clean white t-shirt ya mikomai Abba ya dauramai akan singlet din jikinshi suka mikar dashi yay mugun haske lips dinshi jajir ga rama saidai bai hana kyanshi fitowa ba, takalmin yasaka da kyar Abba da Baba suka fitar dashi shikuma Baba Sulaiman ya shiga dakin da Mami take yace "anga Bilkisu kije gida kuyi girki dan zamu dawo da bakin da suka kawota, kibar kuka Boy ya warke haha" yay dariya kafin ma Mami ta jefamai wata tambaya haryabi bayan su Abba da gudu duk suka shiga mota sai headquarter.

Tun kafin suyi parking suka hango Cp yana washe musu baki dan kasa hakura yayi ya zauna aciki so kawai yake dashi Alhaji ma zasu fara haduwa, fito da Ayaan sukayi dake bude ido da kyar Cp yakara so wajen yana kallon Ayaan dake kallonshi da idanunshi dasuka kankance yace "ciwo ya kare, muje Alhaji suna office dina" yana gaba suna biye dashi abaya har upstairs Cp ne yabude office din ya shiga suna biye dashi, daidai lokacin Bilkisu ta daura hanunta akan kafadar Aaman tanason ta leka meyake nunama Dr Ameenu awayan shi dayan hanunta kuma rike da pringles takai baki tana gutsura. Dukansu binta sukai da kallo harda Ayaan daya kara bude ido da kyau yana kallonta tundaga yatsar kafarta har zuwa kanta, dago dakai sukayi jin anbude kofa da sauri Aaman ya ture hanunta daga kafadar shi suka mimmike tsaye shida Dr dan daga ganin su sun gane family tane sabida manyan kayan dasuka sa, hannu suka mika ma su Abba daduk Bilkisu suke kallo barinma Ayaan dako kyafta ido bayayi, itakuma tana zaune tanacin pringles dinta batare datama kallesu ba, ga teddy ta agefe, ajiye pringles dinta tayi tadau bottle wata dinta ta mike tsaye ta kusa da Aaman kaman zata shiga jikinshi ta mikamai ruwan kaman zatai kuka tace "sweetheart budemini" wani irin mugun tari da Ayaan yafara yasa ta juyo dakai tana kallonsu barinma mai tarin da manyan mutanen ke kokarin rikeshi ganin yana neman shidewa, da sauri ta boye abayan Aaman tasa hannu ta dafashi ta leko dakai tana kallon mutanen dai dai, hada ido suk sakeyi da me tarin da idanunshi sukai jajir yana tari yana kallonta jijiyoyin kanshi duk sun fito shikuma Aaman sai kokarin tureta yake daga bayan shi amma taki saima kara rirrike mai riga datayi tabaya tana make kafada tana "oh'oh" shikuma yacigaba da tureta, wani irin kallo Ayaan yama Aaman kirjinshi na wani irin zafi kaman an juye garwashin wuta daidai lokacin wani dan Sanda ya shigo dakin hanunshi rike da kulki, fizge jikinshi Ayaan yayi daga hannun Abba da duka karfin dayazo mai, yatako ya fizge kulkin hanun dan sandan daya shigo azuciye yay kan Aaman.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

67 - 68
Chapter 58 · 0% Book details