← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 89

Sashe 69

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ledan yayi ya karbi Ice cream din yarufe ya kakkabe jikinta data bata sanan yaciro ta daga motar yarufe sukai cikin asibitin office dinshi sukayi yay cikin bedroom din da ita, magungunan ya bude ya karance leaflet din tas sanan ya dauko ruwa yabata tasha da kyar, ya zauna kusa da ita, da sauri tahau kan jikinshi ta kankame shi rungumeta back yayi yana shafa bayanta kafin good 20min bacci ya dauketa murmushi yayi ya kwantar da ita yaja bargo ya lullube ta ya rage mata ac sanan ya kwashi ice cream dinta yasaka a fridge kafin yasake dawowa kan gadon yamata addu'an bacci yawuce yafita daga dakin, statoscope dinshi yadauka daga kan table yafice daga office din dan zuwa ward. Sai bayan yay sallan azahar sanan yadawo office din ahankali ya bude kofar dakin har lokacin bacci take, bayi ya shiga yayo wanka dan black nicker kawai yasaka yahau gadon shima dan yagaji bacci kawai yakeso yayi, jawo ta jikinshi yayi yay cuddling dinta ya lumshe ido wayarshi datai ringing yasa yaja dan gajeren tsaki ya mika hannu ya dauko wayar yadawo da ita, sunan big mum daya gani yasa ya kafe screen din wayar da ido har wayar ta katse bai daukaba saida tasake kira akaro na biyu sanan yay picking ya daura akunne. Daga ta dayan bangaren Mami tafashe da kuka tace "My Boy" shiru yayi baice komiba, cikin kuka sosai tace "My Boy nasan nama laifi amma dan Allah ka yakuri kayafe min banda lafiya bansan ko mutuwa zanyiba, nasan nai kuskure like how on earth ma zanyi yunkurin kashe matar dana guda, wats wrong with me, Boy please forgive me dan Allah yakayafe min kanajina?" dan lumshe ido yayi saikuma ya budesu ya saita muryan shi yace "shikenan Big Mum komi yawuce" wani ajiyar zuciya yaji ta sauke tace "Alhamdulillah, Allah nagode ma, ya jikin ta?" Ahankali yace "fine ta warke" kecewa dawani sabon kukan tayi cikin kuka tace "kuna gidanku ne naga baku dawo gidaba jiya" dan shiru yayi saikuma yace "eh achan muka kwana" gyada kai tayi tace "to ka gaidamin da ita sai anjima" katse wayar tayi tasa hannu ta goge hawayen datake yi da sauri ta lalubo number Bala dayay kusan 2weeks kenan tai blocking dinshi unblocking tayi tai dailing number bayan ta shiga bayinta ta kulle, saida kiran yakusa katsewa sanan Bala yadauka kafin ma tai magana ya kece da dariya yace "kenen sakona ya girgiza ki wanan dakika kirani da rana tsaka" "wani sako kuma" Big Mum ta tambaye shi tana wani irin shashan kamshi, "yau tun asuba na bama wani dana gani yafito da mota envelop dake dauke da sako na abaki" dafe kirji Big Mum tayi tace "na shiga uku ubanwa yanzu ya karbi sakon babu wanda yakawo min wani abu kuma Ayaan bai kwana agidan nan ba Alhaji ma baya gari towa kaba sakon karfa Katona min asiri" shima shiru yayi saikuma ya tabe baki yace "koma mutum yabude yagani bazai gane komiba kawai tambayan cikon kudinmu nayi" nan ya sanar da ita abinda ya rubuta dan ajiyar zuciya ta sauke dudda haka bata natsu ba, anatse tace "kasan misa nakira ka" "saikin fada" "sonake kamin aiki wanan karan banda kuskure dan yarinyar nan bata mutu ba tana nan araye yanzu ma haka suna gidansu ita da mijinta yaron Alhaji" "kai hajiya" tsawa big Mum ta dakamai tace "dakata kaji, sonaka ka kwashi yaranka kuje gidan ka kashe min daga matar har mijin dan nariga na kwafsa jiya dayasa duk ana zargina, gwara su mutu insan saura Alhaji da Firdausi suka rage dazaran suma nagama dasu kaga ai dokiya ta dawo tawa I don't need any of there signature anymore, ka tabbatar ka kashemin su ta yanda ma za'a zaci kuyan fashine kunzo sata, dazaran ka gama nai comfirming death dinsu wlh wlh yau dinan ko kwana daya bazan karaba zan aiko ma da miliyan goma sha hudu" wani irin dariya Bala yayi yace "angama hajiya ki kwantar da hankalin ki kaman kinyi bako ya mutu, kaman mun kashesuun mun gama kisiyo likafani ki ijiye, sai anjima zanje na shirya anjima da daddare muje farauta" ya katse wayar wani irin murmushi tayi tafito daga bayin ta kwanta akan gado tareda jan bargo ta lullube dan rashin lafiyan karya takeyi.
Chapter 69 · 0% Book details