Sashe 51
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko parking bai gama yi da kyau ba awaje yafito yana kallon gate din gidansu dako rufewa ba'ayi da kyau ba, runtse idonshi yay da mugun karfi kirjinshi na wani irin bugawa kaman ba gobe, da kyar ya iya daga kafan shi daya mugun yimai nauyi ya shiga ciki, da mai gadi yafara cin karo azube kaman baya numfashi ga fuskarshi dukta kumbura sabida naushi, wani irin bugawa kirjinshi yayi ya karasa ya tsugunna ya sauri yana duba pulse dinshi ganin he's still alive suma ne kawai yasa yay reviving dinshi sanan da gudu yay cikin gida, jinin daya gani a stairs yasa heart dinshi ke wani irin mugun racing da mugun gudu, yay sama yana kallon plate dake kasa sanan ga dakunan su duk abude, dakinta ya shiga da gudu babu kowa, wani irin mugun bugawa kirjinshi yayi kaman zai fashe da sauri yabude bayi ya shiga nan ma ba kowa, da gudu yasake fita kaman mahaukaci ya shiga dakin shi da bayin shi bakowa yasake fitowa da gudu ya shiga dayan dakin bakowa, yafito yay kitchen ba kowa ya shiga store bakowa, yafita yay garden bakowa, dawowa falo yayi yana jujjuya wa yana kallon ko'ina amma bakowa, kanshi yawani irin rike da hannu biyu kafin da bude baki da karfin bala'i yace "Bilkisssssss" yawani irin zube akasa ya rirrike jikinshi dake wani irin mugun rawa kaman mai farfadiya, da gudu yafita yay inda mai gadi yake arude ya dauko ruwa ya yayyafa mai hakan yasa yabude ido gabaki daya da sauri ya dagoshi da idanunshi dasukai jarababen ja muryan shi har bata fita da kyau tsabagen bala'i yace "me..me..meya...meya faru?" Mai gadin da biyu biyu yake gani da kyar yace "wasu mutane su biyar sukazo amota sun rufe fuskokin su, suka dakeni sukai cikin gida daga nan bankara saning meya faruba daga nan ba" Gabaki daya jikinshi rawa yake kokarin ma saita yanda zuciyar shi ke bugawa yake sabida karya samu heart attack, da kyar ya mike tsaye yana dafe zuciyar shi yana runtse ido kanshi na juyawa da kyar ya iya ya lalubo waya bama yagani da kyau ya lalubo number Abba yakira ringing biyu Abba dake kan dadduma yagama shafa'i da wuturi ya dauka yace "Boy" da kyar ya iya bude baki yace "p...pops kazo" zumbur Abba yamike daga kan dadduma jin yanda muryar shi ke fita da kyar tana breaking, Mami dake kwance ta bishi da kallon mamaki, arude yace "Boy are u okay, menene, talk to me Boy, u don't sound like u, menene?" da kyar yace "Pops Bilkis, an, ban..ban ganta ba..an dauke..." tsabagen yanda jikinshi ke rawa ma wayar tazame tafadi akasa ta tarwatse, Abba yace "boy, boy" kallon wayar yay yaga ta yanke, Mami tace "menene ba yanzu nan yabar nan ba bayan yay treating kafar hajiya baima tsaya ya auna BP taba fa haka Munari takece min" girgiza kai Abba yayi yace "sako hijabi ki sameni akasa, Boy doesn't sound gud something is wrong" yana maganan yana fita Mami tadau babbar hijabin ta saka ta bishi abaya, Big Mum suka gani tana dingisawa tana zuwa sanye da hijabi hanunta rike da plate tana ganin Mami da Alhaji tace "ina zaku haka nida nazo na debi fruits a fridge nawa ya kare" Mami tace "ga Alhaji nan shinake bi wai Ayaan ba lpy" arude big mumy ta kalli Abba tace "meya sami Boy Alhaji? Mutafi mutafi mugano danmu" gaba Abba yayi suna biye dashi Big Mum ta kalli Mami tace "kedai wlh Allah wadaran halinki Ayaan baida lpy ne shine wai Ayaan" direba Abba yakira ya shiga duk suka shiga aka jasu sai gidan Ayaan.
Yanayin parking motar Ayaan dasuka gani awajen yasa Abba yacema driver yay parking duk suka sassauko Abba ne yafara shiga tsakar gidan ko lura damai gadi ma baiyi ba sai Ayaan daya hango a tsugunne jikinshi nawani irin rawa uncontrollably, da sauri Abba yay kanshi yana "Boy, Boy" dago shi Abba yay yay cupping fuskarshi, hanun Abba yakama gam gam yarike da kyar ya bude baki yace "Pops where is mah wife?" hanunshi Abba yakama ganin kaman ma baya hayyacin shi yay cikin gida dashi yana binshi luuu su Mami suka bisu abaya hankali tashi, shikuma direba ya taimaka ma mai gadi ya shigar dashi dakinshi ya kwantar dashi yanamai sannu.
Zaunar dashi Abba yayi yana kallon jinin daya ga a stairs bakinshi na furta "innalillahi wa innalillahi raji'un" Big Mum tafashe da kuka sosai ya kalli Mami datai shiru tana kallon Ayaan da jikinshi ke wani irin rawa hancinshi jini na zuba yace "ban ruwa Firdausi, mara sanyi" da sauri Mami tai kitchen ta dauko goran ever mara sanyi ta bude ta mikamai Abba ya karba da hannu daya dayan hanun nakan kafadar Ayaan yakai goran bakinshi yana tofamai addu'o'i, Kukan da big Mum keyi yasa Abba ya dakama ta tsawa akule yace "ke kokimana addu'a kokiyi shiru" yasama Ayaan goran abaki ya tsiyaya mai ruwan da kyar yasha sanan yadawo kusa dashi ya zauna ya kwanto dashi yadaura kanshi akan cinyarshi yana kara tofamai addu'an ko jikinshi zai dena rawan, kafin yaciro wayarshi daga aljihu number governor kano yakira gabaki daya, ringing biyu gwamna da kanshi da dauka, Abba yamai explaning abinda ke faruwa.
Within 15 good minutes karan motocin police kakeji suna shigowa anguwa, ansace matar da tilo ga Abdulrasheed Gwanaye ai dole gwamna dakanshi ya turo polisawan, tundaga waje CP yafara saka team dinshi bincike wasu na interrogating mai gadi daya farfado kafin yazo da kanshi har bakin kofa yay sallama Mami tabashi izinin shigowa shida wasu manya police guda uku suka shigo ya tura biyu dake tareda shi sama bincike sanan ya zauna kusa da Abba dake ma Ayaan dahar lokacin bai dawo daidaiba addu'a, saida Abba ya idar sanan ya nisa yace "Alhaji naga akwai CCTV camera a compound din" sai a lokacin ma Abba yatuna yace "harda ma falon nan akwai" IG yace "ina computer to zanzo mu kalla dan musan meya faru" da kyar ya mike tsaye Abba ya rike shi yace "Boy" gyada ma Abba kai yayi da kyar alamun zai iya, Abba yarike shi sukai sama IG nabiye dasu abaya, Mami da big Mummy ma suka bisu, wani daki sukaje nan suka tariyo computer har zuwa daidai inda goons din sukazo sukai horn mai gadi yafita waje dubawa sai gashi daya daga cikin su sanye da mask ya shigo da mai gadi yana dukanshi kafin ya sumar dashi ya bude musu gate bakin van din ya shigo, pursing video IG yayi ya rubuta plate number motar down sanan ya danna play suka cigaba da kallo gashi sun shigo sun fiffito daga motar sunyi cikin gidan sun bude kofa sun shiga falo sukai upstairs, dayake babu CCTV a sama basu ga maiya faru ba saidai ihunta dasuke ji da lokacin datake kiran Ya Ayaan, runtse idonshi yay da karfi wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomai da sauri ya share, saikuma inda daya daga cikin su yasa kafa yatokare mata ciki tafado ta fasa kai wani irin dunkule hannu yayi zai daki computer da sauri IG ya rike shi calmly yace "be strong Man, i know how u feeling, zamu kamasu idan ma kidnappers ne dan basuyi kama da yan fashi ba, inda yan fashi ne da sata xasuyi, indai har kidnappers ne zasuyi contacting dinku, so u people should stay alert zasu iya kiranku kowani lokaci, yanzu dai one good thing is zamu nemo motar nan tasu ta hanyar plate number nan koma ina motar take a fadin kanon nan, sanan Alhaji" ya kalli Abba yace "yakama ta yanzu akwai body guard dazasu dinga yawo da family ka most especially ur son, yanzu dai zan koma office zan zuba team dina akowani hanya da express way na barin garin kano zamu kamasu da izinin Allah, one last thing is i need hoton ta, dan nan CCTV footage fuskar ta is not clear sosai dan musa a media incase idan wani yagan ta" Da sauri Abba ya kalleshi yace "kanada hoton ta Boy kabamu?" saida yarike hanun Abba sanan ya iya magana da kyar yace "yafashe" Abba ya kalli Cp yace "wayarshi tafashe dazu amma zasu samo hoto bari yadawo daidai tukun" ajiyar zuciya cp ya sauke yace "shikenan we will use dis for now, please take care of him he doesn't look good" yanuna ma Abba Ayaan sanan yawuce yafita daga dakin, da taimakon Abba suka fito sabida jirin dayake ji sosai suka zauna afalon sama ya daura kanshi akan kafadar Abba shi kadai yasan yanda yakeji, Abba sai addu'a yakemai jin yanda zuciyar shi kewani irin rawa, tashi Big Mum tayi ta kalli Mami datai wani irin tagumi daurewa kawai take danji take kaman tai ihu tace "bare na shiga bayan gida" gyda mata kai kawai Mami ta iyayi tai shiru tana tunani abu kaman mafarki Bilkisu da dazu dazun nan tana tare da ita, da dingishi Big Mummy ta shiga dakin dake kusa dana Bilkisu ta maida kofar ta rufe, bayi ta shiga ta rufe sanan tafito da wayarta daga zani wacce tuntuni ta maidata silent, message din Bala tagani da sauri tabude;
“hajiya mun dauketan muna warehouse din saidai fa, Ahmad ya bugeta sabida gardaman dataso tamana kanta yafashe har yanzu bata farfado ba”
Da sauri big Mummy tamai reply
“Bala bakace min gobe zakaje Bauchi ba, inaso da daddaren nan kudau hanyar Bauchi kunemi wani daji achan ku karasata kuyar, sabida yanzunan za'a baza police ako ina agarin nan, banason ko gawanta su tsinta agarin nan, ka tabbatar bata numfashin daga yanda nake ganin yaron ma dazaran ta mutun shima rayuwar tashi karewa zatayi, ka tabbatar kunbar garin nan yanzu, yanzunan zakaji alert din kudi, kudin aikin ka kuma saina tabbatar kai komi da kyau sanan zan biyaka miliyan goma, kubar garin nan yanzu, i repeat yanzu! ". Tura mishi dubu dari tayi sanan ta kashe wayar gaba daya ta wanke fuskarta tafito daga bayin tadawo ta dayan gefen Ayaan ta zauna tana tofamai addu'a tana matse kwalla, ahankali Mami ta tashi ta dauro alwala ta shiga daya daga cikin dakunan tafara salla.
Bala na ganin text dinta ya kinkimeta yasata amota sauran ma suka shiga suka bar gidan.